Chapter 19-20

26 3 0
                                    

19-20.

"""""""""""Harararshi tayi tare da cewa "duk ma yarda aka mata dai-dai ne, tunda tona min Asiri kake da niyyar yi", "uhmmmmm ba zaki gane bane Adda girman bukatata ta wuce na Yar 20years ma balle 15, kaya kawai zaku haɗani da shi", ya fada yana mikewa.

        "ngd kuma ba sai ka gwadamin ban isa da kai ba", ta fada tana haɗe fuskarta alamar tayi fushi, matsawa ya yi kusa da ita, tare da riƙe hannunta yace "Adda na Amince..!", yana fadar haka ya fice daga bedroom din, cike da murna ta fito itama, haɗa baki suka yi gurin cewa "Adda ya amince?", wani kallo ta musu irin na wasa tare da cewa "ko yake jira sai kun amince", ta fada tana zama, dariya duk sukayi dan susan dole ma ne ya amince.

         Washe gari gaba dayansu suka tafi Saloon , sai da suka je kafin Adda Zainab ta sa driver ya je ya taho da Nazlah  , cikin minti kaɗan ya je gidan, kafin ya je ma Nazlah ta shirya dan sun kira Ummu ta Yar kwararraɓar wayarta sun sanar mata,cikin shiga mai kyau Nazlah ta fito sai kamshi take ,mota Driver ya bude mata, shiga tayi ta hakimce a baya, sai da ya rufe kafin ya koma mazaunin driver, ya kunna motae suka kama hanyar shagon saloon din.

       15minutes ne ya sadasu da ƙawattacen shagon Saloon din da yake kan Hanyar Kano road , shago ne mai kyau da tsari , na masu kuɗi, bayan sun karasa ya bude mata motar ta fito, jagora ya mata har ciki, da Sallama ta shiga cikin shagon, duk juyowa sukayi da murmushi kan fuskarsu suka amsa mata, ƙarasawa tayi ta ɗuka har ƙasa ta gaishesu, Jaan ta Adda Zainab tayi jikinta ta rungumeta, tare da cewa "kina lafiya Ƙanwar Adda?", ta fada da murmushi kan fuskarta.

        jinjina kanta tayi alamar lafiya lau, rungumeta suka shiga yi daya bayan daya suna tambayarta lafiyar ta, Haleesa da take mata murmushi tace "Sannu Amaryar Auta..!", dan murmushin yaƙe ta mata dan sam bata fahimci kan maganar ta ta ba, karɓar Ƴar Adda Zainab tayi ta zauna kusa da Haleesa tare da fara ma wasa.

         Wata Yar siririyar Mata ce ta fito daga wata yar kofa tana cewa  "Ayya kuyi hakuri na barku kuna jira na, yanzu me za'a fara muku kuma da wa za'a fara, "ta fada tana dan murmushi.

          Nuna Nazlah Adda Zainab tayi tare da ce wa "ita zaki fara mawa gyaran jiki zaki mata da gyaran kai, sai ki wanke mata ƙafa , " kallon Nazlah tayi tace "kina son kitso?", da sauri ta girgiza kai alamar bata so, "mai yasa ba za'a miki ba? , zai fi fito da ke", dan kwaɓe fuska tayi tare da cewa  "kaina namin ciwo in aka min", ta fada tana matsawa kusa da Mai gyaran jikin.

         wankin ƙafa aka fara mata, duk da cewa ƙafarta tsaf take ga laushe da tsantsi, hakan yasa da aka wanken sai ta kara kyau da tsari, kumba ta gyara mata ƙafar tayi tarrr² har wani jaa² take kamar jini zai fito, wani ɗaki suka shiga  anan aka mata dilka da halawa, komai binshi da ido Nazlah take, dan ita wannan abubuwan bata sansu ba, sai kallon jikinta take, tana mamakin wai ita ce ta koma haka, jikinta ya koma kalar na jarirai, sai shinning yake gwanin burgewa, bayan an gama turara mata jiki da turaren jiki mai kamshi da zama cikin jiki suka fito.

           duk tsura mata idanu sukayi suna kallon zallar kyau irin na Nazlah dan haskenta ya kara fitowa sosai , dan in kai mata kallo daya ba lallai je ka iya gano daga wace ƙasar ta fito ba, dan kwata² batayi kala da Yan nigeria ba, zaunar da ita tayi gurin da zata wanke mata kai, dan kwallin kanta da tunda tazo bata cire ba Matar ta kama ta fara warwarewa, kyakyawan gashin kanta ne ya fara warwarewa daga gammon da ta mishi.

           tana zare gammon gashin ya warware gaba dayanshi ya zubo akan bayanta, faɗowa Haleesa ta kusan yi sa boda tsananin mamakin irin yawan gashin kan Nazlah, duk da Ahalinsu na da gashi sosai Amma bata taɓa ganin mai yawan gashi da kyan gashi ba irin na Nazlah, matsawa tayi gurinta jikinta na rawa ta kama kasan gashin tace "Duk wannan naki ne..!?", gyaɗa kanta Nazlah tayi.

NAZLAHحيث تعيش القصص. اكتشف الآن