chapter 13-14

8 3 0
                                    

☘️☘️ *NAZLAH*☘️☘️



*DAGA AL[]ALAMIN*


SALMAJI/[]AR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️




*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR KARSHENSHI, SADAUKARWAR NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF) WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YADDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA K'ARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHEERAH...*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
       {R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
  *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*


13-14


""""""""""""""Babu wanda ya kula da Nazlah kowa ta kanshi ya yi, babu kuma wanda ya yi tunanin zuws gidansu ya faɗi  halin da take ciki.

        Ummu tana ta jiranta, dan an kawo mata kashedinta har gida, hakan yasa take jiranta taji ba'asin Abun da ya faru, kafin ta dauki mataki a kanta, shiru² Nazlah bata dawo ba har gabanin Magrib, hakan yasa hankalinta ya tashi, ta kasa zaune ta ƙasa tsaye, tana cikin Safa da marwa, Yah Haleem ya shigo, kallonta ya yi tare da cewa "Ummu Lafiya kuwa?", ya fada yana kallonta, da sauri ta juyo gareshi tare da cewa "Nazlah ce bata  dawo ba, tun ɗazun da ta fita Islamiyya, gashi Abbanku baya nan, kuma ya hanani fita in baya nan, ko zaka je ka duba min ita ?", ta fada tana kallonshi, "to Ummu bari naje na duba", ya fada yana juyawa.

        cikin sauri yake tafiya zuwa Makarantar tasu Nazlah dan duhu har ya fara rufawa, cikin sa'a ko da yaje makarantar a bude take, sai dai ba kowa a ciki, hankalinshi ya fara tashi, cikin daƙiya ya fara dudduba Ajujuwan Makarantar, sai dai ba kowa a ciki, kuma duk a bubude, cike da tsananin mamaki yake kallon Ofishin Malaman da yake a bude , kuma makarantar ba kowa, hankalinshi ne ya kaiga wani waren takalmi da ya gani yashe a ƙasa kusa da Ofishin, tafiya ya fara yi zuwa ofishin, da sauri ya shiga yana furta "Innalillahi Nazlah! Nazlah!! Nazlah!!!", ya fada yana jijjigata.

      A hankali ta fara bude idanunta, da suka mata nauyi, "Yah Haleem..!  ta fada tana shigewa jikinshi", mikewa ya yi, da ita jikinshi ya nufi hanyar waje, da ita rungume a jikinshi, hanyar gida ya nufo da ita, yana cikin tafiya yaji an kwala mishi kira, da sauri ya juya yana kallon Iya da take nufoshi, da sauri ta ƙaraso gareshi tare da cewa "kaga Nazlan?", Nuna mata ita ya yi, tare da cewa "gata bacci na tarar da ita tana yi, babu kowa a makarantar sai ita daya", ya fada yana direta ƙasa, ganin yarda take ta mutsu² da son ya sauketa.

        Yana sauketa, ta Afka kan Iya tare da cewa, "Iya goyani bacci nake ji", ta fada tana riketa, da mamakina babu ko kunya Iya ta duƙa Nazlah ta haye bayanta, zaro ido Yah Haleem ya yi, tare da cewa "Iya dama har yanzu baki daina goyata ba,kar ta je ta karyaki fa", ya fada yana yunƙurin dauke Nazlah daga bayan Iya.

       kaɓe hannunshi Iya, tayi tare da cewa "mai yasha ruwanka da harkarmu, baka ji tace bacci take ji ba, " ta fada tana zare dan kwallinta, kyakyawan dogon gashinta mai kyau ne ya bayyana, wanda duk da tsufar da tayi amma yananan sumul sai dai furfurar da ba'a rasa ba akan tsoffafi.

         dakyar take takawa da Nazlah akan bayanta amma haka take tafiya, Yah Haleem ya yi, ya yi ta sauko da ita amma taƙi, sai ma kara kankameta da Nazlah tayi ta rumtse idanunta.


         *************

      Da sauri ta bi bayanshi, tana shiga ta tarar dashi zaune gefen bed dinshi, ya buga uban tagumi, zama tayi kusa dashi, tare da cewa "lafiya kuwa My Solder?", ta fada tana dafa kafaɗarshi.

NAZLAHWhere stories live. Discover now