CIWON 'YA MACE
By
Fadila LamidoADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 11- 12
Can ta hangeta bakin Ofishin su na tsaye da Malam Zubairu, hadawa ta yi da gudu domin ta isa wurin tun kafin Mamy na fadawa Malam Zubairu abin da ya kawota. Ta na daf da ta isa gurin tai saurin cewa, "Mamy!" Cikin Sauri Mamy ta kalleta adaidai lokacin da Mamy take cewa, "A'a ta dawo fita ce ta kama mu, ina tunanin kar a tashi makarantar ta dawo ta iske bama nan, shi yasa na ce barin biyo"
Cike da gamsuwa Malam Zubairu ya jinjina kansa, kallon Nur yayi kadan sannan ya wuce Ofishinsa.
Kallon Nur Mamy ta yi cikin daure fuska sannan ta ce, "Ina kika tsaya Nur baki dawo gida ba? Sawuna uku makarantar nan babu kowa aciki?"
Kwalkwal Nur ta yi da ido sannan ta ce, "Mamy Yaya Abdallah be miki bayani ba? Mu na tare da shi a gidan Kaka, Kuma na ce mishi ya gaya miki." Jimm, Mamy ta yi zuwa can ta ce, "Wanne Yayan?" Hawayen da ya zubo mata tasa hannu ta share sannan ta ce "Yaya Abdallah" Shiru Mamy ta yi a lamar nazari ta ke, zuwa can ta ce, "Shi na fara kira da na ga yaci ace kin dawo gida ya ce min shi tun da ya sauke ki ya wuce abin shi" Da Sauri Nur ta dago ta kalli Mamy "Mamy wallahi ba haka ba ne, Kuma a tambayi Malam Zubairu sannan mu je gidan Kaka kiji, a gaban ta na ce mishi dan Allah ya gaya miki..." Hannu Mamy ta daga wa Nur alamar dakatarwa sannan ta ce, "Bazan tambayi Malam Zubairu ba, kuma bazanje gidan kaka ba, ke da bakin ki zaki gaya min in da kika tsaya, daure fuska sosai Mamy ta yi, sannan ta ce, "Wuce muje gida" Nur batai musu ba ta shiga gaba, Itako Mamy juyawa ta yi gurin Malam Zubairu, lokacin da Mamy ta fito makarantar Nur na tsaye tana kuka, hannunta Mamy ta rike tare da fadin, share hawayen ki karki sake min kuka atiti, shasha kawai, so ki ke sai kowa ya fahimta me kike ciki?" Daker Nur ta iya dakatar da Kukanta har suka isa gida, a harabar gidan su ka samu Aunty Saratu, tasowa ta yi itama cike da damuwa ta na cewa, "Ina kika tsaya Nur?, Kallo Mamy tabi Nur da shi tare da cewa "Ta ce, gidan Kaka ta tsaya, ta kuma cema Yayan su ya fada min" Mamy ta karake maganar tana kallon fuskar Yaya Abdallah da ya fito da ga cikin gidan yanxun.
Kallo daya Abdallah yayi ma Nur, sannan ya ce "Ke! Me kike cewa?"
Dagowa Nur ta yi da jajayen idonta ta ce, "Ai kai kace Malam Zubairu ya taho dani gidan Kaka, kuma da na ga lokacin makaranta ya yi nace maka zan wuce makaranta ka gayawa Mamy..." Afusa ce Abdallah ya tako gaban Nur cikin yanayin da ke nuna cewa yana cikin mamaki ya ce, "Maimaita in ji! Ke dan baki da kunya har ki iya kallon idona kimin Karya?" Ganin yana Shirin daga hannun sa tai saurin matsawa tare da fadin, "Karka da ke ni hannun ka akwai zafi" Kara yowa kanta yayi Mamy ce ta ce "Karka taba ta wuce abin ka" Wayar sa ya dauko a aljihunsa yana cewa, "Ba dai gidan Kaka ta ce ba barin kirata"
"A'a karka kirata." Mamy ta fada cikin bada Umarni. Juyawa ta yi ta kalli Nur, sannan ta ce muje ciki" Cikin gidan suka nufa, yayin da Abdallah yai ficewan shi waje. Bayan sun shiga ciki ma Mamy da Aunty Saratu matsawa Nur suka yi, akan ta fada musu in da ta tsaya, amsan nan dai da ta bada tun farko ita take sake badawa, dan haka suka barta kawai badan sun gamsu da zancen ta ba.
Washegari ta kama lahadi Mamy bata barta taje makaranta ba, hakama ranar litinin daker Mamy ta barta, saida ta hada mata da magiya, daka kalli fuskar Nur kake gane tana cikin damuwa, idon ta duk sun kunbura ga yawan tunani da take yi.
Misalin karfe 8 na safe ta isa makaranta, ita da Helen kamar yadda suka saba, acan suka samu Rahma dake dama can tana riga su zuwa, wayar Rahma Nur ta amsa ta fita waje ta zauna, number data riga ta haddace cikin kanta tasa wayar sannan ta kara a kunnen ta tsayon lokaci tana jiran taji an dauka amman harta katse ba'a dauka ba, batare da wani bata lokaci ba ta sake danna kira, sai dai wannan karon ma harta katse ba'a dauka ba, dan haka ta hakura ta mike ta nufi komawa cikin ajin su, sosai ta ji jikinta ya kara sanyi tare da jin komai baya mata Dadi, ta na daf da shiga ajin wayar ta dauki kara, kallo daya tawa wayar sannan ta juya ta koma gefe tare da ansa kiran.
Kuka ta saka cikin wayar, bayan tsayon wani lokaci ta sassauta kukan nata, zuwa can kuma ta share hawayen tass, sannan tabar shashshekar kukan tare da fadin, "Eh ina ji" Shiru ta sake yi tsayon lokaci, da ga can ta sake cewa, "Mamy kawai na fadamawa" Turo baki ta yi da alama fada ake mata cikin wayar, zuwa can ta ce, "Ai be dace ba abin da ya ke, kuma kowa kallon mtumin kirki ya mishi, ni ba sharri nake mishiba..." Shiru ta sake yi, bayan tsayon lokaci ta na saurare tace, "Sabo da Mamy" Sosai ta kara bata ranta zuwa can tai jifa da wayar can nesa, kallo tabi wayar dashi, kome ta tuna kuma saita mike da sauri ta dauki wayar, dake karamar waya ce babu abin da ta yi, ganin wayar bata katse ba ta sake maida ita kunnen ta tare da fadin, "Na bari" Shiru ta yi na wanni lokaci sanna n ta ce, ba yarwa na yi ba faduwa ta yi" Wannan lokacin ma shiru ta sake yi, zuwa can ta sauke wayar sannan ta nufi ajinsu jikinta a sanyaye.
Bayan an tashi makaranta ta koma gida, har yanzun Mamy fushi take da ita, dan haka ta cigaba da yin duk wani abu da tasan zai faranta wa Mamy rai, shiko Yaya Abdallah ba ta sake barin sun hado ba domin ya zun ta lura dashi ya riga da ya tsene ta.
Haka ta cikaba da lallabawa har saukanta ya rage saura kwana biyu, duk wani shiri ta gama yin sa, Abba da Mamy sun mata komai da akewa yar gata daidai gwargwado, a na i gobe sauka ta je lalle da kitsu, bayan ta dawo farin ciki ne ya kama Mamy kallon kurulla tai mata tare da fadin "Ba karamin me sa'a bane mijin da zai aure ki, tubarkallah ma sha Allah, duk wadda ya same ki a matsayin matar aurensa lallai ya tsinci dami akala
Murmushi ne ya subuce ma Nur cikin matsanancin jin kunya ta ce "Mamy ai fushi kike da ni har yanzun"
"Eh, ai kece kika mata min rai, bedace ace kina boye min komai ba, ni uwarki ce, idan har bazan san me kike ciki ba meye amfanina?"
"Toh ki yi hakuri kinji? Kuma ban boye miki komaiba wallahi Mamy, Yaya Abdallah yasan ba in da naje wallahi"
"Na ji Nur, ni dai fatana ki nutsu, ke mace ce, dan haka ki daina karanbanin saka kafar a ko ina"
Amsawa ta yi da to, sannan ta mike ta nufi dakinta, Mamy ko binta da kallo ta yi duk wani alamar girma ya riga da ya bayyana ajikin Nurr, yariya ce kyakyawa fara sol me mayan idanu, siriri ce sosai, saidai duk da cewa shekarunta bazai wuce sha shidda ba kirjinta cike yake taf ma sha Allah, sauke kai Mamy ta yi, bayan Nur ta kule tare da cewa "Allah ya nuna min auren yariyar nan lafiya sai naji tamkar inzoba ruwa a kasa in sha"
Washegari tun da sassafe ta shirya cikin fararen kaya safar hannu da ta kafa baki haka ma fuskanta bakin nikafi ne, dakin Mamy ta shiga bayan ta gaisheta ta dauki turaren Mamy kan madubi da fesa cike da murmushi Mamy tace "Allah ya kawo mu" Itama Nur murmushi ta yi tare da fadin "Mamy zan wuce dan Allah kuzo da wuri"
"In sha Allah Nur, dan ina ga ma ko Abban ku saidai ya saman acan" Da murmushi Nur ta nufi dakin Abba, acen ta samu Aunty Saratu zaune bayan ta gaishesu Abba ya shiga mata addu'a, in da ya kare da cewa, Allah ya sa in ga ranar auren ki kamar haka, duk yawan family nan bamu taba aurar da diya mace ba" Cike da shagaba Nur ta fice tare da da cewa "Saura dai ka ga na zama likita Abba" Abba daya juyota bayan ta fice yayi murmushi sannan ya kalli Aunty Saratu ya ce, "In sha Allah tun da tana son karatu zan tsaya mata ta yi sosai" Gyara zama Aunty Saratu ta yi sannan tace "Ai daman yaran gidan nan suna Karatu Alhaji."
"Eh haka ne, sai dai ita mace ce, amman bazai garara ba, in dai ta maida hankali zan cika mata burinta" Nisawa Aunty Saratu ta yi sannan ta ce, "Amman Alhaji sai na ke ganin kamar rashin sa'aninta mata da babu cikin dangi yana taba ta sosai" Murmushi Abba ya yi tare da cewa, "A'a, babu wannan maganar anan gidan, sai dai da ya ke kinsan aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, Bashir da Abdallah su na janta ajiki, ga kuma Jamal da Jamil, nan gaba kadan duk aure za su yi, matayensu suma 'ya'yayenmu ne"
Bude baki Aunty ta yi da nufin yin magana kome ta tuna kuma sai tai shiru tare da mikewa.
****
Misalin Karfe 10:am filin saukar ya cika ya tunbatsa, sai dai har wannan lokacin baza ido Nur ta ke, domin bataga wani daga gidansu ba dan haka banda baza ido babu abun da ta ke,Tuni aka fara karatu, gashi an hanasu tashi bare ta nemi waya ta kira Mamy, ta na cikin wannan yanayin taji an kirayi sunan ta, Maryam Jibiril Mailafiya, mikewa ta yi tame jin kafarta na rawa, har ta isa kan munbarin ta amsa abin maganar, cikin nutsuwa ta ke rairo karatun ta, yayin da jama da dama suka maida hankali wajen sauraronta, bayan ta gama ta mika abin maganar ta sauka akan munburin tare da isa gurin zamanta, tana zama ta fara share hawayeta cikin nikabi, ganin har wannan lokacin babu kowa da ga gidan su, matar da ta dauki hoto ne a gurin tazo ta mika wa Nur hoton da ta dauketa wurin karatun, karba ta yi ta kalla, ganin bata da kudin da zata bayar yasa ta mika mata tare da fadin "Zan amsa anjima" Durkusuwa matar ta yi tace "Ina yan uwanki suke in kai musu?"
Hawaye ne ya zubo wa Nur alokacin da take cewa "Basu karaso ba" kafadanta ta dan dafa alamar rarrashi, daker Nur ta iya rokon matar aron waya, saidai har sau uku ta kira number Mamy ba'a daga ba dan haka me hoton ta kara bata hakuri sannan ta wuce.
Acikin ranta ta ke tunanin ko menene ya hana su zuwa? sam bata tsammaci haka ba, nan taji komai yabar yi mata dadi, kiran sunayin yan saukan da aka fara domin basu shahada ya dawo da ita cikin hayyacin ta, agefe guda ta hangi mata nan nata mata wa su hoton dan haka ta nuna mata alamar ta habari, matsowa matar ta yi kusa da ita tace "Wani ya amsa hotunan ki ya ce, a kara miki wasu" Duk da cewa batasan wane ne ba dadi taji har tai ajiyan zuciya batare da ta sani ba, zuwa can aka kira sunan ta, nan ta miki akaro na biyu ta isa gurin, acikin ranta take cewa, "Allah yasa koma wanene yazo min yamin kara kar a gane Abba da Mamy basuzo gurin nan ba, saidai ga mamakinta ta Abba tagani Yana tahowa filin cikin babban riga da hula, bayansa Yaya Abdallah da Yaya Bashir ne sai dai Abba ya rigasu isa gurin dan haka shine ya karban mata Shahada, bayan angama masu hototuna suka koma gurin zamansu, sosai Nur ta cika da farin ciki acikin zuciyarta take cewa, "Abba ma yana farin ciki sosai, hakama Yaya Bashir ya kasa boye farin cikinsa sai yake hakora ya ke, shi ko Yaya Abdallah fuskarshi babu yabo babu fallasa, bayan an gama bawa kowa sannan aka sake kiran sunan Nur a matsayin wadda tazo na daya, nan farin ciki ya sake rufe su Mamy, fitowa ta yi ta amsa kyautuntuka, sosai taron ya kayatar, kowa na nuna sha'awarsa, bayan an tashi gurin zaman su Abba ta nufa ta kwanta kafadan Mamy cikin shagwaba tace, "Mamy bakizo da wuri ba"
"Injiwa ya gaya miki, Yaya Bashir ne ya ce muna nan aka fara Karatu"
"Ni ban ganku ba har na fara kuka fa"
Dariya suka yi gaba daya da ga nan Yaya Bashir ya kira me hoton nan suka hadu suka yi gaba daya har da Baffah da iyalanshi.
Kowa cikin fara'a ya ke, adaidai wannan lokacin ne Nur ta hangi kyawawan samari guda biyu, tun da Nur ta gansu fara'ar fuskanta ya dauke, Mamy ce tace, "Nur ga su Jamal can ki maza kije ku gaisa"
"Mamy su karaso nan mana' kasa Mamy ta yi da murya ta ce "Ki je dai domin kema kinsan ba zuwa zasu yi ba"
Sakin hannun Mamy ta yi ta isa gaban su, tun tana cikin su Mamy su ke mata wani irin kallo har ta iso gaban su, cikin girmamawa ta gaidasu yayin da suka amsa a wulakance tare da fadin, "Da baza kizo bane?"
"A'a mu na yin hoto ne" Nur ta fada tana satan kallon fuskar Jamil wadda ko gaisuwar ma be amsa ba, Muryan jamal ta ji yana cewa "Ke ma kinsan idan ba dole ba babu abun da zai kawomu cikin wannan unguwar bare wannan yar tsukukuwar makarantar dako iska ba shigowa ya ke ba"
Bakin shi kawai Nur ta kalla ta kara yin kasa da kai.
Jamil ne ya ce "Jamal mu je, ai dai ta gammu ko? Cike Da haushi Jamal din ya ce, "Ni wallahi ko bata gammu ba babu abin da ya dame ni. Tsoronta akeji ne? Ko zumuncin dole ne?"
Lumshe Ido Nur ta yi ganin suna kokarin barin wajen ta ce "Baku gaisa da su Abban mu ba gasu can"
Jamal dake baya ne ya ce "Ayya, haka ne fa, oya to mu je mugaida su" Yana maganar ne yana cigaba da tafiya dan haka ta bisu da kallo har suka shiga motar su suka bar wajen.
Bayan ta ga wucewan su tsaki ta ja afili ta ce "Dadin abun dai mu ma ba matsiyata bane, kuma da zuwan ku da karkuzo duk daya" A daidai wannan lokacin ta ji an gota ta bayan an hankade kafadarta, dan haka ta bi mutumin da kallo, mamaki ne ya kamata dan haka ta kara baza idonta domin gani ta yi kamar yayan Helen ne Poul ya wuce ta.
Tsaye ta yi a gurin tana son tabbatarwa, motar da ya nufa tabi da kallo, har ya isa gabanta na faduwa tare da tambayan kanta me ya kawoshi cikin musulmi? Yadda ya ke da shigarsa bazaka taba gane cewa ba musulmi ba ne, haka Kuma ko magana yayi babu alamar da zata nuna maka hakan, "Kenan ya yi amfani da hakan ya shigo makarantarmu?" Nur ta fada cikin zuciyarta tare da saurin takawa domin tabbatarwa, motar ta ga ya bude ya shiga ya zauna, sannan ya waigo ya suka yi ido hudu tamkar yasan tana kallon shi dama can. Sosai gaban Nur ya fadi faduwa me tsanani, ganin irin kallon da ya ke mata, haka ta tsaya cak tamkar an dasa ta agurin, fararen ya tsunsa ta ga yana karkadawa alamar tazo kusa...

CITEȘTI
CIWON 'YA MACE
DragosteCIWON 'YA MACE rikitaccen al'amarine mai kulle kai, nishadi,soyayya, cin amana, da yadaura, acikin labarin ne zaga yadda ciwon 'ya mace ya zama na yarwanta mace, duk kuwa da tarin alakar dake tsakani makusantan biyu, ta tsayawa yar uwarta mace duk k...