CIWON 'YA MACE PAGE 39-40

88 10 0
                                    

CIWON 'YA MACE
     By
Fadila Lamido

    ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Page 39- 40

Dagowa Nur ta yi ta kalleshi har yanzun ita ya ke kallo, cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta ganin haka Poul ya ce, " Ba cikin gidan zamu shigaba daga bakin get zamu tsaya in yi maganar da zanyi sauki wuce" Cikin Sauri Nur ta girgiza kai alamar a'a, kallonta yayi  ya sake cewa tsoron me kike ji? Bayan gidan ba bakonki bane, kuma da mutane a cikin gidan nan bakin get ma akwai mai gadi, idan cutar da ke zanyi ai ba anan zance mu shigaba ko? Wannan maganar da yayi yasa ta tuna waye shidin, hakika duk wadda yaganta tsaye da Poul abin zai bashi mamaki matuka, dagowa ta yi ta kalli layin nasu babu kowa, tsoro ne ya shigeta kar wani dan gidan su yazo ya ganta tare da Poul, yin wannan tunanin yasa ta nufi shiga gidan, biyo bayanta Poul yayi yana Mai sauke ajiyan zuciya, mai gadin dake can kofar dakinsa ne ya juyo ya kallesu sannan ya dauke kansa, in da Nur ke tsaye Poul ya tsaya tare da kureta da Ido, sosai kallon da yake mata ya ke sata shiga cikin damuwa domin a duk sanda yai mata irin kallon tana shiga cikin wani yanayi wadda take rasa gane kanshi, ganin bashi da niyyar magana ta ce, "Ka yi maganar sauri nake yi  a gida za'aga na dade" kanshi ya shafa tare da matsowa daf da ita, can kasan makoshi ya ce" Duba yadda na zama Nur, gaba daya banda nutsuwa, wata daya da ya wuce idan ance min zan zama haka bazan yaddaba, yau da kika tsaya muka yi magana bakiji yadda naji dadiba, yanzun abu daya nake son kimin dan Allah karkice a'a, ki taimaka min in samu nutsuwa yau in yi bacci mai dadi" Dagowa Nur ta yi ta kalleshi, har yanzun a burkice ya ke, idon shi kawai ya isa ya tabbatar maka da hakan, cigaba yayi da cewa, "Zaki taimaka min?" Ahankali Nur ta daga kanta alamar eh, matsowa ya sake yi ganin haka Nur ta kara mannewa jikin get din kasa-kasa yace, "Dan Allah ki dan tsaya na rungumeki kona minti biyu ne" Cikin sauri Nur ta dago ta kalli jajayen idonsa tare da girgiza kanta, ganin haka ya kafeta da Ido tare da cewa mai yasa?" Kawar da kai Nur ta yi sannan tace Haramunne" Lumshe Ido yayi zuwa can ya bude su akanta tare da cewa, "Haram? Wannan karon ma kai ta daga mishi tare da cewa "Eh, babu kyau hakan ba daidai bane"
"Na gane, to hannun fa? Zaki bani hannunki mu gaisa?" Wannan karon ma kai ta girgiza alamar a'a, yawu Poul ya hadiye sannan yace "To shikenan amman zan iya baki waya anjima mu gaisa? Kai Nur ta sake girgizawa alamar a'a, cikin rashin jin Dadi yace "To shikenan, je ki na gode" kamar jira Nur take ta wuce tana daf da fita gidan ya sake kiranta, tsayawa ta yi, wani kati ya mika mata tare da cewa akwai number ta a jiki, anjima ki kirani" amsa kawai ta yi ta juya domin sosai ta kosa tabar wajen. A sanyaye ta isa gida, sannu taiwa Mamy sannan tai saurin wucewa dakinta domin gani take kamar mamy zata gane bata da gaskiya, a yadda ta shiga dakin yasa Saida Bilkisu ta bita da kallo, domin yanayinta ya nuna kamar batasan mai take ba, Daker ta iya cin abinci ta yi duk abin da zatayi sannan ta wuce islamiyya. Bayan sati daya Nur ce tsaye bakin makarantar tana jiran mashin, tun daga ranar da Poul ya tareta ta daina jerawa da Zainab, ana tashi take hawa mashin ta wuce gida abinta, yauma tsaye take tana jiran mashi taga motarsa ta tsaya gabanta, wani irin faduwa gabanta yayi, bude motar yayi ya fito, gabanta ya tsaya tare da cewa, "Sannu Hajiya" kawar dakai Nur ta yi kasa-kasa tace "Ina wuni"
" Lafiya" Ya fada idonshi a kanta, "Ya gida da karatu?" Wannan karon ma kasa-kasa Nur tace Lafiya lau" Zo muje mana in sauke ki? A'a mashin zan hau" Jimmm yayi zuwa can ya ce, "Shikenan, mai yasa baki kirani ba ranar dana baki kati na?" Na mance ne" Nur ta fada tana wasa da hannunta, shiko Poul cike da damuwa ya maimaita zancenta sannan ya ce to yanzun na tuna miki, dan Allah ki kirani.  Da kai anur ta amsa Motar ya koma ya shiga tare da cewa "Zaki kirani ko?" Wannan karon eh tace tare da tare mashin tahau, mashin din na shirin tashi ya taho da motar wurin ya daga murya ya ce, "Katin na nan ko?"
"A'a ya bace" Wani katin ya sake cirowa ya mika mata, sannan ya figi motar kamar zai tashi sama ya bar wajen, ko da Nur ta isa gida ciro katin ta yi ta kalla kamar yadda ta yi ranar da ya bata wancen, bayan ta gama karewa katin kallo ta dauko Littafin da ta saka wancen tasa wannan, sannan ta maida Littafin ta ajiye, tsayon wata daya suke shafe a haka, idan yaga kwana biyu bata Kira ba sai ya sake aiko mata da wani katin, harsaidata tara koma sha tara batare da ta kiraba, yasha aiko Zainab ta kawo katin tare da rokon ta kira din, amman ko sau daya Bata taba kwatanta kiraba, sosai suka saba da Bilikisu a yanzun hira suke sosai ta saki jikinta dasu Mamy ma, yau kawar Bilkisun ce tazo, wannan shine zuwanta na biyu gidan, tun a zuwan farko suka saba da Nur, dan haka yauma har da ita ake hiran, labarin saurayinta take bayarwa, sunata dariya, zuwa can kawar Bilkisu Madina ta kalli Nur tace "Ke baki bamu labarin saurayin ki ba?" Tabe baki Nur ta yi tare da cewa "Ni bani da saurayi karatu nake son na yi sosai."
"Wallahi karyane kice baki da saurayi, mu ma ai duk karatun zamu yi Amman ai da samarin mu" Madina ta fada tana kallon Nur, "Niko bani dashi, ku gani kuke na girma ko?"
"Eh mana to dame muka fiki" Bilkisu ta fada tana dukan kanwason Nur, dariya Nur ta yi sannan tace to awurin Abba da Mamy har yanzu karamar yariya ce ni, kofa waya basu yadda na rike ba" Dariya Su Bilkisu suka kwashe dashi yayin da Madina tace "An barki a baya wallahi"
"Ba wani baya, ni haka yafi min, wayar ma mai zan da ita, duk wadda nake son nai waya dashi zan iya amsan wayar kowa a gidan nan nayi wayata banda matsala da waya"  Domin karatu nake son na yi sosai." Bilikisu ce ta ce "Wai da gaske baki da saurayi? Maganarwa naji kuna yi ke da Zainab ranar ce?" Juya baya Nur ta yi tare da cewa "Wannan yayanta ne fa, waishi a dole sona yake, Kuma ba musulmi bane fa" Zaro Ido Bilkisu ta yi tare da cewa, "Kamar ya bamusulmi ba? Ba kince yayan Zainab bane?" Dan Waigowa Nur ta yi kadan sannan tace, "Eh yayantane amman ita da Mamman su ne masulmi shi arne ne, wai Kuma a hakan ya ke sona" Madina ce tace "Kuma idan Yana sonki fa saikiga ya musulunta."
    "Hmm umm lallai, wannan mutumin ne zai musulunta? Bashi da kirki sam, shi a tunanin shi a hakane zan aureshi, kuma nasan Koda ace musulunta yayi Abba da Baffah bazasu yadda ba, ni shiyasa ma ban kulashi, baranma ya Bashir, tab" Nur ta kareke maganar tare da juyawa baya, Jimmm, Bilkisu ta yi yayin data shiga nazari jin Nur takira sunan mazan gidan bata kira na babban yayanta ba, share tunanin ta yi ta hanyar cewa, "Gaskiya ki yi saurayi soyayya da dad" Madina ce ta ce "Ke dallah rufe mana baki, keda kwana shidda da tarewa mijin ya bulaki ya tafi ya barki" Aunty dake kokarin shigowa dakin ce taja ta tsaya alokacin da taji Bilkisu na cewa "Wallahi yadda kike haka nima nake ba bulanin da aka yi" Madina ce tace "Wallahi karya ne, kwanaki shidda fa tare dashi a dakin kice ba abin da yayi miki har ya wuce?"
"Eh mana, alkawari muka yi bazai tabani ba sai ya dawo."
  Madina ce ta sake cewa "Eh, ji ya zama dole, amma yadda kuwa ba dole bace, daga ke sai Abdallah adaki kice anyi kwana shidda be kusanceki ba?" Cikin da nishadi Bilkisu tace "a rantse da qur'anin Ubangiji har mukai kwana shiddan abin da kike tunani be shiga tsakanina dashi ba, kuma wuri daya muke kwana."
     "Tabb lallai, amman na sarawa Abdallah da kokari, Juyawa Aunty ta yi rike da kular abincin, itako Nur bata saka musu bakiba saidai duk hiran tasu tana jinta cikin kunnenta.
                            *****
Gaban Mamy Aunty ta dire abincin tare da cewa, "Ikon Allah" Dagowa Mamy ta yi ta kalleta sannan ta kalli kular abincin tace "Lafiya kuwa?"
  "Dawowa nayi na kira Nur ta dauka"
"Lafiya ko?" Mamy ta tambaya, hiran da ta juyo ta kwashe ta gayawa Mamy cike da damuwa Mamy tace "Ikon Allah, to Abdallah lafiya yake kuwa Saratu?"
"Nima dai abin ya daure min kai Mamy, sai dai fa kinsan yaso abar bikin har ya dawo watakila shiyasa yayi hakan kinsan yaran nan idan Basu suka yi niyyar abu ba babu wadda ya Isa ya sa su"
  Jimmm Mamy ta yi tare dace "Niko da kinsani da baki Gaya min ba wallahi, yanzu zan shiga damuwa da zulkumi, meye ribarshi ta yin hakan to? Idan haka ne manene amfanin auren?"
"Yaran zamanin kenan ai Mamy, faface kawai wata rana zakiga ya dawo ya daukita dan ban tunanin zai iya hakuri har ya kammala batare da ya dawoba, suna waya da ita sosai, kuma kullum mukayi waya saiyace ya take, ta saki jikinta ko a'a, hankalinnshi Yana kanta."
   "Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan ta ce, "Shikenan, Allah ya kara karkato da hankalinshi gareta,, Aunty ta amsa da Amin tare da kwalawa Nur kira. Bayan ta amsa tazo ta dauki abincin. Sai yamma Madina ta tafi, har kofar gida suka raka ta ita da Nur sannan suka dawo cikin gidan, kitchen suka wuce domin yau Aunty tace su zasu yi kirkin ginan, cikin kankanin lokaci suka yi suka gama, suna yi suna kira, bayan sun gama ma jarashi sukayi kamar yadda aka saba, sannan suka koma daki suka yi wanka. Misalin karfe 8:30pm gaba dayansu suka zauna akan teburin cin abincin gidan Amman banda Bilkisu dan bata iya zama wurin har idan Abba na nan, dan haka adaki take cin nata, suna cikin cin abinci Bashir ya shigo, da ledoji niki Niki a hannunshi, afalon ya aje, sannan ya karasa wurin ya zauna, cike da Murna Nur ta gaidashi sannan shima ya gaidasu Abba, Aunty ce ta zuba mishi yaci kadan, sannan ya koma falon ya zauna tare da cewa Nur, "Ki sauri ki gama kizo" Cukalin ta aje tare da mikewa ta dawo kusa dashi, kallonsu Abba yayi sannan yace "Kaga ka hanata cin abincin" "Ta koshine Abba" Ledojin dake nesa dashi kadan ya nuna mata tare da cewa, "Ki dauki ledojincan ki ki kaiwa Amarya inji ango" dariya Nur ta yi sannan ta tsuguna ta deba ladojin, kudi ya ciro ya mikawa Nur ya ce "Kice injishi fa" Amsawa ta yi da to sannan ta juya, Abba da tunda Nur ta mike yake kallon su ne ya kira Nur a lokacin da take daf da shiga kofar da zata sadata da dakin, bayan ta dawo ta tsaya ya kalli Bashir ya ce, "Ita ina nata? Me yasa bazai tuna da kanwarshiba? Bayan ita take debewa matar tashi kewa?" Yar dariya Bashir yayi sannan ya nuna ledan dake hannunshi tare da cewa "Abba ga nata nan ai" Dauke fuska Abba yayi tare da cewa "Yauwa ya kyauta" Ita ko Nur juyawa ta yi takaiwa Bilkisu sannan ta dawo rike da jakar makarantarta tana cewa, Yaya Bashir mun fara jarabawa fa ka dade bakazo gidan nan ba"
"Da banzo ba ai ko a waya baki kirani ba" Bashir ya fada yana mika mata ledar, karba ta yi ta daura a jikinta tare da cewa "Dan wannan?" Wani irin kallo ya yi mata sannan ya kalli Abba, ganin baya kallon su yace, "Kinsan da yaya na saya miki wannan din? Sabulone kawai bani da kudi" Hannu yasa a aljihu ya ciro kudi ya mika mata tare da cewa "Amasa idan zan tafi kiban dubu uku ki rike biyu" Abba Nur ta kallah har yanzun abincin shi yake ci dan haka tace "Kai ka saya min sabulo amman kana son kacewa Abba shine kudin ma so kake suka kamar shi ya bani?"
  "Eh mana, ko kinfi son suyita ganin laifinshi?" Ajikinta ya daura kudin sannan yace "Matso mu yi hoto tad'i zani, ta matsamin tana son ta ganki" Cike da zumudi Nur ta aje kayan hannunta a gefe ta matsa kusa dashi, wayar ya mika mata tare da cewa  "Amsa ki dauke mu" Kin amsa Nur ta yi ganin inda yake kallonta tace "Kai ka daukemu mana, katuwa zanyi idan na rike wayar"
"Nima bana rike waya idan za'ayi hoto"
Juyawa Nur ta yi ta kalli Aunty Saratu tace "Aunty zoko daukemu, budurwar shi zai nunawa hotunmu Kuma wai saidai ni na rike wayar dan karyayi muni" Daure fuska Aunty ta yi tare da cewa "Nice marainiyar wawonku ko? ku ta hoto ma kuke yi" Karake maganar ta yi da Jan tsaki, batare da Abba yace komaiba ya mike yaje ya amsa wayar tare da cewa "Ni bari na musu" Cike da fara'a Bashir da Nur suka gyara zamansu, hoto daya Abba ya dauka ya mika wa Nur wayar tare da zama cikin falon, kallon hoton Nur ta yi ta kwashe da dariya tare da cewa "Be yi kyauba Abba, baka iya daukan hotoba, shima Abba cike da dariya yace "Kawo ingani" Mika mishi wayar ta yi ya kalla sannan yace "Maye beyi kyanba anan? hannunshi yasa ya nuna Bashir yace "Ga Bashir ga Kuma Maryam, to meye abin da beyin ba?  Ko baku bane a jiki?"
"Mune Abba, Amma a karkace ka dauka, wurin mamy da Aunty Nur ta tafi da wayar suma dariya suke, yayin da Nur din ma keta dariya, idonta akan wayar ta nufa Yaya Bashir tare da cewa "Kallah hoton ya Bashir" Dagowa ta yi da nufin kallon sa, gabanta taji ya fadin dalilin ganisa yana tattara katin da Poul ke aiko mata dashi gaba daya suna watse a cinyanshi, tattarawa yake tare da yi mata wani irin kallo dan haka gaba daya ta rude alamu rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita...
  
   

CIWON 'YA MACEWhere stories live. Discover now