CIWON 'YA MACE PAGE 35-36

87 11 3
                                    

CIWON 'YA MACE
      By
Fadila Lamido

    ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Page 35-36

Awannan karon zabura Nur ta yi mai karfi dan haka ta kufce batare da ya fargaba, aguje tabar wajen tana waiwayen shi, shikuwa Poul kansa ya dafa domin har yanzun beji hankalinshi ya kwanta ba.

    "Ina kika je?" Ya Bashir ya jafawa Nur wannan tambayan yayin da ya tsareta da ido. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da hannunta tare da motsa bakinta, sai dai ta gaza furta komai, Idon Bashir a kanta ya sake cewa "Nur bakyaji ne Ina managa?" Dagowa ta yi ta kalleshi can kasan makoshi ta ce, "Fitsarine ya matseni" Kallon sama da kasa yai mata sannan ya ce "Fitsarin kikaje kenan?" Wannan karon daga kai ta yi, kallonta Bashir ya sake yi sannan ya bi hanyar da ta fito dan haka gaban Nur ya fadi, kallo ta bishi dashi tana dafe ta kirji, zuwa can ya dawo ya wuceta batare da ya kalli Inda take ba, bayan shi tabi da alama be gamsu da abin da Nur din ta fadaba, yana shiga motar Nur ma ta shiga ta zauna, saidai ta kasa sakewa da ka kalleta zaka gane bata da nutsuwa sam domin gaba daya jin ta take a yamutse, dan haka ta fara hawaye duk da cewa tabawa Bashir baya Amman tanaji ajikinta kallonta yake saidai bece mata komai, karatun Alqur'ani ya kunna yanabi acikin motar dan haka tuni Nur taci gaba sa kuka.
    Zuwa can taji ya tsaya tare da kashe karutun, waigawa tayi tare da zabura dalilin ganinsu a kofar gidansu, hawaye ta fara sharewa tare da kokarin sauka acikin motar batare da ta bari sun hada Ido ba, harta saka kafarta daya a waje taji yace, "Nur juyo mu gani" Ahankali ta juya ta kalleshi bayan ya kare mata kallo ya ce, "Kuka me kike yi?"
"Babu komai, ba kuka nake ba" Jinjina kai Bashir yayi sannan yace "Shikenan jeki" Sauka ta yi Cikin Sauri ta shige gida, dare ya riga yayi domin tun suna hanya aka Kira mangariba, Kai tsaye gefen Mamy ta shiga, wannan karon akwai saukin mutane, dafda Mamy ta zauna jikinta a sanyaye, cike da mamaki Mamy ta kalleta tare da cewa "Nur Yaya dai, na ga kin dawo jiki a sanyaye?" Kamar jira Nur take ta fashe da kuka dan haka Mamy ta saki baki, mamaki karara akan fuskarta tace, "Me yayi zafi haka?" Mikewa Nur ta yi nata kokarin fita batare da tace komai ba, dan haka Mamy ta mike ta biyo bayanta.
   Bakin gadonta ta sameta zaune tana cigaba da kuka dan haka Mamy ta zauna a gefenta tare da cewa "Ke da wa? Abdallah ko?" Kai Nur ta girgiza dan haka Mamy tace "To waye? Girgiza kai Nur ta sake yi dan haka Mamy tace a'a bazai yiyuba Nur haka kawai mutum na kukane? Bana son irin wannan gaskiya, yau kowa gidan nan farinciki yake mene ne naki na kuka? Ganin Nur Bata da niyar magana Mamy ta mike ta fice, fitan Mamy ba jimawa Aunty Saratu ta shigo, kallon Nur ta yi cike da mamaki ta zauna gefenta tare da cewa, Wai maye haka Nur? Hannu Nur ta mika ta kara share hawaye, mene ne? Me aka miki? Aunty a fada bayan ta jawo Nur jikinta" Nur ta dauki tsayon lokaci ba tare da datace komaiba, zuwa can ta shiga bawa Aunty labarin abin da ya faru tsakaninta da Poul, bayan ta gama tace Aunty na gaji ya takura min. Fuskar Aunty Saratu cike da murmushi tace, "Nur dan wannan ki ke kuka? Wannan ai ba wani abin damuwa bane" Dagowa Nur ta yi ta kalli fuskar Aunty yayin da Aunty take cigaba da cewa, "Ni dama tun da naga irin zaryar da yar uwanshi take a gidan nan na zargi haka, Allah ne ya nuna mishi ikonshi, wannan shi zaisa ki sake agari batare da ya takura miki ba, ni dama bana wani son aje a yi kararsa, sabo da yana da kudi Nur, abin mu zaifi tabawa ya lalata mana suna, yaron yana takama da kudi Nur, yanzun abin da nake so dake ki kwantar da hankalinki ki daina sa damuwa, yanzu bazai iya cutar dake ba, kuma ta sanadinki dabi'unshi suna iya canzawa ya zama mutumin kirki." Wuri daya Nur ta tsurawa Ido tare da cewa, "Aunty tsoro nake ji, Kuma ni na rikici, Inajin tsoro sosai kuma ni bansan yadda zanyi ba"
   Kallon Nur Aunty ta yi sosai sannan tace, "Bari na fito miki a mutum, tun da naga kuruciya na dibanki, duk da ada Ina miki kallon wadda wayaunta ya wuce na shekarunta, amman yau duk kin daburce, idan baki fahimtaba ina son ki gane Poul son ki ya ke yi" Cike da mamaki Nur tace to Aunty ana yin haka ne dama? baya sallah fa" Nur ta fada tare da kallon cikin idon Aunty, "Cemin zakiyi ba fa musulmi bane, Ina sane Nur bakisan ta sanadinki konai na iya canzawa ba?" Wannan karon shiru Nur ta yi tana sake-sake cikin ranta, zuwa can ta dago ta kalli Aunty tace "Su Abba baza su yadda da wannan ba ai"
  "In ji wa ya gaya miki? wuyarta ace be musuluntaba, iyayenku sunsan abin da suke yi, abu daya zan gargadeki akai karki yadda ko hannunki ya sake rikewa, ki gaya mishi wannan haramunne a addininku, sannan in dai ba a gidan nan ba karki tsaya hira dashi a titi, duk da nasan zai bukaci hakan, amman karki yadda, idan da gaske sonki yake yazo ya tunkare Abbanku ya nema izini tukuna...
  Cikin sauri Nur ta katse Aunty da cewa "Ba musulmi bane fa" Wannan karon cikin tsayawa Aunty tacewa Nur "Ina ruwanki?" Sunkuyar da kai Nur ta yi yayin da Aunty taci gaba da cewa, "Kamar yadda kika saba haka zakici gaba dayi, duk ranar da ya bude baki yace son ki yake sai kice yaje ya gayawa Abbanku, ki sake jikinki ki daina tsoronshi ranar Monday idan zaki makaranta ki biyawa Zainab kamar yadda kuka saba."
   Wannan karron Nur batace komaiba saidai ta samu nutsuwa sosai duk da cewa har yanzun tana tunani akan zancen Aunty, mikewa Aunty ta yi ta fita bayan ta Kara kwantar mata da hankali, Aunty tana fita Nur ta shiga bayin dake makale jikin dakinta, auwala tayo sannan ta yi sallah, bayan ta idar addu'oi ta yi wadda suka Kara samar mata da nutsuwa, bata tashi a wurin ba har saidai aka yi isha'i sannan ta koma gado, wannan lokacin wani irin nishadi ta tsunta kanta aciki musamman lokacin da ta jiyo gud'a tare da hayaniyar mutane afalo, durowa ta yi a gadon cikin sauri ta nufi falon tana cike da fara'a, abokan Yaya Abdallah ta gani zazzaune a kasa yayin data hangi Abdallah zaune saitin kamar Mamy, da alama neman Albarka yazo yi zai shiga dakin Amarya, yin wannan tunanin ya kara fadada murmushi Nur, zagayawa tayi can bayan kujeran da Mamy take ta zura hannunta ta dafa kadan Mamy tare da leken fuskar Abdallah fuskarta cike da murmushi, tun zuwanta Abdallah ya kula da ita, saidai be nuna ma yasan da zuwan nataba bare ya daga kai ya dubeta, 'yan uwan Mamy ne suka mishi nasiha daka karshe Mamy tasa albarka sannan suka mike zasu tafi, wannan karon ma farin cikene ya sake lullube Nur dan haka ta daga murya tace, "Yaya Abdallah!" Juyowa yayi ya kalleta tana wasa da hannunta akan kafadan Mamy, hannunta daya ta daga mishi tare da yar dariya tace "Allah ya sanya alheri" Azuciye Abdallah yayi kanta cikin tsawa yace "Ina wasa dake ne?" Baki Mamy ta bude tare da cewa daga addu'a? Abokansa ne su ka jashi Dan haka ya fice a  falon yayin da mutanen dakin suke dariya haka itama Nur dariya tayi domin ko kadan batajin haushin hargaginshi ba, afalon ta zauna akacigaba da hira da ita, washegari da wuri aka yi budankai kowa ya watse, duk bakin da suka kwana a gidan sunje gidan Amarya sun ganu gidan yayin da kowa idan ya dawo yake mamakin haduwan dakin Bilkisu, yayin da ake ta yabon amarya kowa cewa yake yariya karama Mai hankali ga sanin darajar mutane, washegari ma Aunty da Umma sukaje suma haka suka dawo suna yabawa, Washegari ya kama Monday dan haka Nur da wuri ta shirya, bayan tawa su Mamy sallama ta nufi gidan su Poul gabanta na faduwa sosai.
    Tura get din kawai ta yi ta shiga, Mai gadin gidan ne ya juyo ya kalleta sannan ya dauke kanshi, tundaga nesa ta hanga Poul zaune a farfajiyar gidan, Saida gabanta ya fadi ganin shi sannan Kuma batama taba ganinshi zaune a gurin ba. Wannan karon kasa kwalawa Zainab kira ta yi kamar yadda suka saba, tsaye ta yi ita bata shigaba ita bata koma ba, tun da ta shigo Poul din yake binta da kallo, zuwa can ya rufe jaridar hannun shi tare da mikewa tsaye ya fara takowa, ganin haka Nur ta fara ja da baya batare data daina kallonshi ba ta ke nufar kofar gidan. Ganin haka ya tsaya cak fuskarshi na dauke da murmushi yace "Yun da bazaki tsaya inzo ba to ki kira Helen din ku wuce." Wannan karon ma bata tanka ba komawa yayi ya zauna Yana cigaba da kallonta fara'ar fuskarshi Bata yanke ba har wannan lokacin, ganita jima tsaye Kuma da alama Bata da niyar kiran Helen din yasashi  yace "Helen!" Amsawa ta yi da karfi yayin da ya sake daga murya yace "Ga kawarki, fitowa ta yi da Jakarta a hannunta tana kokarin goyawa ganin haka Nur tai saurin ficwa agidan, cike da mamaki Zainab ke kallonta domin Bata sa rai zata biyo mata ba. Misalin Uku ta dawo makaranta afalo ta samu Ummy zaune ita da Mamy, rungumarta tayi itama Ummy cike da Murmushi tace ke na yi ta jira ki dawo ki rakani gidan Abdallah" Batare da ta  Nur ta Bari Ummy ta rufe bakiba tace "Ai bansan gidan ba Ummy." Mamy ce tace "Ita ta sani tashi ki shirya tun dazon take jiranki."
   Karyar da kai Nur ta yi tare da yin kwalwal da Ido tace "Mamy ni baxani ba gaskiya."
    "Au bazakiba?" Ummy ta fada tare da cigaba da cewa "Toni barin wuce ai bansaniba dan ban zauna na bata lokaciba ba."
   Mikewa Nur tayi tare da amsar Jakar Ummy tace  "Muje in rakaki mota ni sai in tare da Mamy ne zani."
"Toh Allah ya taimaka" Ummy ta fada tare da yiwa su Mamy sallama, Bayan dawowan Nur fada Mamy ta mata akan kin bin  Ummy data yi kiri-kiri.           Ranar da suka cika kwana na hudu da tarewa Bashir yazo daukan Nur zuwa gidan Abdallah, wannan karon ma kememe taki zuwa, dan haka Bashir ya tsareta da tambayan dalilinta nakin zuwa, ganin babu wasa a idonshi ta ce, "Kawai nafi son in je ne tare da Mamy kasan yanzu haushina yake ji yana iya dukana"
"Kizo muje bazan bari ya dukekiba"  tashi Nur ta yi da ga kusa da Bashir ta koma can bayan Mamy tare da cewa "Ni gaskiya Yaya kaje abin ka ninafi son inje tare da Mamy, dan in da ita ko kallon banza bazai min ba" Mamy ce tai saurin cewa Ashe kuwa bazaki ba Nur, ni me zai kaini gidan su, ki tashi maza kina bata mishi lokaci dare na yi"  Mikewa Nur ta yi tana me buga kafarta tare da kunkunai take cewa "Ni Mamy nace bazaniba, ko an hana shi ya  dakeni idan ya yi ta hararata fa, saina dawo gida na ce ya harareni kuma kuce na yi hakuri ba gara banjeba" Karake maganar ta yi tana hawaye dan haka bayan Mamy ta gama kare mata kallo ta juya ta kalli Bashir da ke zubawa Nur harara tace "Jeka abinka" Kamar jira yake ya mike ya nufa kofa, cikin murya kuka Nur tace "Yaya ka gaida Aunty Bilkisun" Wani irin kallo Mamy ta sakewa Nur sannan ta kalli bayan Bashir da ya wuce ba tare da yace komai ba. Tun daga ranar babu wadda ya sake mata maganar zuwa gidan Bashir har suka cika kwana shida da tarewa wadda ya kama ranar ne Yaya Bashir zai wuce karatu, misalin karfe takwas na safe ta gama shirin makaranta, fitowa ta yi domin yiwa su Mamy sallama, tun kafin ta isa falon ta jiyo muryan Yaya Abdallah babu tsoron da taji domin dai tasan babu abin da zai mata, dan haka ta Isa falon tare da Sallama, duk mutanen dake falon amsawa suka yi Abdallah ne kawai be ma waigo bare ya amsa, karasawa ta yi kai tsaye ta nufa gurin amarya dake zaune daf da Yaya Abdallah cikin katon hijjabi dan haka bakama iya hangen kayan dake jikinta, hannunta ta rike tare da cewa "Auntymu Ina kwana" cikin sakin fuska tare da yanayin jin kunya ta amsa yayin da Nur ta kalli Inda Yaya Abdallah yake tace "Yaya Ina kwana?" Tamkar besan da ita a wurin ba haka yayi, dan haka ta sake cewa "Yaya Abdallah Ina kwana?" Batare da ya kalli In da Nur take ba yace "Mamy in tafi zakiyi Mai bayani ko?" Cikin mamaki Mamy ta ce "Ban gane ka tafi ba?, Ko ba komai ai dai ka bari ku yi sallama ko?" Nur sakin hannun Bilkisu ta yi sannan ta juya tai ma Mamy da Aunty Saratu sallama ta fice abinta, gidan Poul ta nufa tana me ardu'ar Allah ya sa ya riga ya fita acikin zuciyarta, bayan ta tura kofar ta saki ajiyan zuciya ganin babu kowa sai Mai gadi, Amma da Alama Poul din yana nan danga motar shinan an sakko da ita, kira ta kwalawa Zainab ta amsa sannan ta fito daga bayanta ta hangi Poul tafe, dan haka ta ji gabanta ya fadi, kallo daya yawa gefenta sannan ya juya ya shiga motar, ita ko Zainab matsowa ta yi tace "Nur zo ga Yaya yace zai kaimu" gabanta ne ya sake faduwa Dan haka tai saurin nufar get din gidan tare da cewa "Ni bazan hau motar kowaba."
Muryanshi taji kamar daga sama yana bawa mai gadin umarnin ya rofe kofar gidan dan haka ta kara sauri, saidai ki kafin takai wajen mai gadin ya rufe kofar, dan haka ta tsaya cak tana kallon motar Poul din  dake tahowa zuwa get din gidan. Daidai saitinta suka tsaya, Zainab na gefensa, ganin haka ta yi kwalkwal da Ido, Poul din ne ya sakko ya bude bayan motar ta gefen da take tsaye yace "Shiga muje"
  Kallon shi ta yi sannan ta kalli motar daya bude yake rike da murfinta, Nan take zancen Aunty ya shiga dawo mata...

CIWON 'YA MACEWhere stories live. Discover now