CIWON YA MACE
By
Fadila LamidoADABI WRITER'S ASSOCIATION
PAGE 27-28
Cikin sauri ta dago wayar ta kalla sannan ta sake mayarwa kunnenta batare da tace komai ba.
Muryansa ta sakeji ya ce, "Me yasa bakya zuwa makaranta? ko kina tsorona ne? Kin fada a gida?"
Duk tambayan babu wadda ta amsa aciki, jin shirun yayi yawa ya sake ya cewa, "Ki fito kije makaranta abin ki, babu abin da zan miki, na gane cewa babu sa hannun ki, na gano bakin zaren, kuma komai zai dawo kamar baya, yanzun dai abin da nake so dake ki yafeni, kuma ki fito dan Allah, ina kofar gidanku, akwai abin da zan gaya miki..."
Mikewa Nur ta yi a fusace ta jefawa Zainab wayar tare da cewa, "Idan kin je kice mishi bazanzoba, bayan wancen karon ya daukeni a titi yanzu zaizo har gida ya daukeni sabo da yaga ba'a dauki matakiba?" Cikin sanyin murya Zainab tace, "Ba daukarki zai yi ba Nur, ya ce mini hakuri zai baki, ni abin ya fara daure min kai, kulum na dawo makaranta sai ya tambayeni mun hadu dake, idan nace bamu haduba ya fice, anjima ya sake tambayata, yanzu Kuma kawai ya ce mini inzo muje gidanku a baki hakuri."
"Ya gaya miki abin da ya mni?
"A'a Ni yace min ma ko kince zaki gaya min kar in saurareki, amman dai in baki hakuri."
Wanni irin kallo Nur taiwa Zainab sannan tace, "To yanzun in gaya miki ko baza ki saurareni ba?"
Jimmm Zainab ta yi sannan ta ce, "Karki gaya min tun da ya baki hakuri, yanzun kizo muje yana jiramu na ga kamar ma bashi da lafiya ne."
"Ai yanzu ya fara ciwo, aduk sanda na saka goshina akasa saina roki Allah ya saka min, idan kinje ki gaya mishi bazai warke ba ya dinga ciwo kenan daga nan har ranar mutuwanshi, kuma tunda kin goyi bayanshi karki sake zuwa gidanmu, ki gaya mishi ya shirya zuwa kotu bayan bikin Yaya Abdallah, sai anbi mini hakkina akan abin da ya yii mini...
Zainab bata cire idonta akan Nur ba saida ta ji wayar na ta sake daukan kara, ganin Poul ne ke kiran ta juya da nufin fitowa a gidan dan tasan ya gaji da jirane. Zainab na fita Aunty ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi, dakuwa taiwa Nur tare a fadin "Wai ni Nur waye ke koya miki magana haka? Wani maganar idan kika yi saina tsaya na kirga shekarun ki, me yasa zaki yi fada da kawarki tun ta kuruciya akan wani.?"
"Aunty ba wani bane yayan tane ai."
"Eh, be dace kiyi fada da ita ba..."
"Aunty cewa fa yayi wai yana kofar gida inzo kinga har a gidan ma zuwa zai ya daukeni sabo da yaga ba a kamashi ba ranar..."
"A'a Nur bana tunanin haka, ai da kinje ba abin da zai miki."
"Aunty Poul din? Ni ko ganin shi banson na kara yi, itama Zainab din ba ruwana da ita har mamma"
Dariya Aunty ta sake yi tana kallon yadda Nur ke share hawaye. Bayan ta gama karewa Nur kallo ta tashi ta isa bakin window, labulen ta daga sannan ta leka har yanzun Motar poul na tsaye a kofar gidan, yayin da helen ke tsaye abakin motae tana magana. Dariya Aunty ta yi tare da sakin labulen sannan ta dawo daf da Nur ta zauna tana kokarin boye murmushinta.
****
"Kisan duk yadda za ki yi ki fito min da ita, ina son in gantane kawai."
"Bazata fito ba fa, maganganu take marasa dadi ta ke ta fada, kuma tace na fada maka"
"Karki gaya mini, amman ki koma ki bata hakuri tazo."
"Ta ce fa bayan bikin yayansu Abbanta zaikai ka kotu akan abin da kai mata." Shiru Poul ya yi tsayon lokaci, zuwa can ya shafa kanshi tare da fadin, "Ban mata komai ba, idan sun kaini kotu zan iya kwatan kaina, ni yanzun damuwata kawai kizo min da ita."
Juyawa Zainab ta yi domin ta rasa yadda zata yi ya hakura, dan ita bawani saba magana dashi ta yi ba, ko da ta koma nacin duniya taiwa Nur ta ki zuwa dan haka ko da ta koma kasa magana ta yi tai tsaye kawai tana wasa da yatsunta. Shima Poul kallo ya kare mata sannan ya figi motar sa ya wuce, ganin ba gida ya nufa ba Zainab tai a jiya zuwa sannan ta koma gida mamaki cike da zuciyarta.
Itako Nur shigowan Abdallah ne ya dauke mata damuwar maganar Poul, bayansa kawai take kallo domin ta masifar kosawa ta ga matar tashi, sai dai har wannan lokacin bata hango kowa ba domin Abdallah dogo ne sosai, mikewa ta yi da sauri ta nufi tahowa tare da leken bayanshi wata zarkadediyar budurwa ta hanga kanta sunkuye dan haka tai saurin zuwa ta rungumeta tare da fadin "Oyoyo." Cike da fara'a suka rungumi juna sannan suka taho zuwa cikin, tuni Abdallah ya zauna binsu da kallo kawai yake, sosai Nur ta bashi mamakin ganin in da take ta farin ciki da ganin yariyar da zai aura. Itama Nur bakin gadon ta koma tana kallon yariyar, Aunty taita bata takalmi tana gwadawa har ta debi wadda take so, tare da Yaya Abdallah suka zaba, da kanshi yake saita mata takalmin har ta gama, ga dukkan alamu yana son yariyar sosai, dan baya miti daya batare da ya kalleta ba, yayin da yake yawan kai bakinsa saitin kunnenta yai mata magana kasa kasa, idan zata bashi amsa kuwa kunnensa ya ke kaiwa gurin bakinta, bayan ya gama saurara yayi murmushi sannan ya koma gurin zaman shi. Har suka bar gidan Nur murmushi take domin sun matukar bata sha'awa, kuma sun dace da juna sosai, har mota ta raka su bayan sun tafi ta dawo gida cike da fara'a. Afalo ta samu aunty na bawa Mamy labarin Bilkisu, yayin da mama keta fara'a "Wlh bakiga yariyar ba kyakyawa da ita, kuma wallahi d'aya sharaf da ita, dan bata wuce Nur ba"
Cike da fara Mamy tace "Eh lallai karama ce tun da kika kwatanta ta da Nur"
"Wlh Mamy har dan jikin nasu ma, mama kawai Nur zata fita, sai Kuma dan haske kadan, gaskiya na yaba da yariyar ga tarbiya."
"Wannan karon ma Murmushi Mamy ta yi tare da cewa "Toh ai shikenan, Allah dai ya zaunar dasu lafiya."
"Amin" Aunty ta amsa, ita ko Nur tunda taji aunty ta ce wai tafita nono maganar da Abdallah yayi kwanaki ya shiga dawo mata, in da ya ke cewa ita da ga han hangota hanci ake fara gani da wasu abubuwa, kawar da zanjen ta yi tare da fadin "I dan ma haka yake nufi Allah ya Isa."
Mamy da Aunty wuni ranar kayan akwatin sukaita hadawa dan gobe za'akai, kafin yamma sun gama zuba duk abin da ya dace. Misalin 10:37pm Abba da Abdallah ne tsaye a tsakar gidan, yayin da Abba kecewa, "Bana son in sakejin maganar daga biki, ai kaika nemo yariyar nan ba wani bane ya nemo maka, dan haka banga dalilin dagawaba, idan baka da wajen da zaka ajeta acan kana iya zuwa ka gano garin in yaso daga baya kazo ka sauki matarka."
Cike da gamsu Abdallah yace "Shikenan Abba, dama..." Kasa karawa yayi dalilin hango budurwar yariya tana shigowa gidan, ganin In da Abdallah ke kallo ya sa Abba kallon waje tare da fadin "Waye nan?"
Cak ta tsaya tare da cewa "Ni ce."
"Kece wa?!" Abba ya fada cikin tsawa tare da har gowa "Zainab ce Abba"
"Wacce Zainab din?!" Abba ya sake tambaya tambaya cikin kosawa, karasowa ta tayi tare da fadin, "Kawar Nur ce."
Kawar Nur? Cikin rashin fahimta Abba ke matsawa gabanta Yana mai jafa mata tambaya, ganin haka Abdallah ya ce, "Yariyar nan ce kawarta kanwar Poul" Dakatawa Abba yayi tare da cewa "To to na ji, lafiya dai ko?"
"Lafiya lau Abba."
"To me ya fito dake da dare haka" Abba ya fada yana duba agogo dake daure a hannunsa.
"Abba nazo wurin Nur ne zan amsa litrafina....
Batare da Abdallah ya bari ta rufe bakiba ya ce ta yi bacci ai yanzu, haba agogon hannun sa ya kalla sannan yaci gaba da cewa, "Shadaya ne take shirin yi fa.?"
Kawar da kai Abba yayi sannan ya ce "Ki daina fitowa da daddare haka, kai Abdallah rakata ciki, idan Nur din ta yi bacci ka bata jakar Nur din ta dauki abin da take so....

YOU ARE READING
CIWON 'YA MACE
RomanceCIWON 'YA MACE rikitaccen al'amarine mai kulle kai, nishadi,soyayya, cin amana, da yadaura, acikin labarin ne zaga yadda ciwon 'ya mace ya zama na yarwanta mace, duk kuwa da tarin alakar dake tsakani makusantan biyu, ta tsayawa yar uwarta mace duk k...