002

0 0 0
                                    

*Z* *A* *A* *N* *E*

*_002_*

"Ada Banida suna, wata rana na haɗu da wani mutumi a Abakin Titi lokacin naje kallon yan Ƙwallo sai Naji ya kirani da Sule wai nayi masa Kamada wani Sule ɗan abokinsa"

james ya Gyada kai alamun gamsuwa sannan ya ɗora da tambayanshi shekarunshi nawa , Sule ya kauda kai

"Ka daina Min irin wannnan tambayan, Kasan banida Amsarsu”

Shuru james yayi yana Dubansa da mamaki ,Batareda sule ya sake dubansa bayace

"Eh Ban san shekaru na ba, Bamuda kowa Bamuda gida, bamuda me kirga mana shekaru, A ginin makarantar Boko muke kwana ko kasan gada ko kango , so ttt....tari mmmm..munfiye kwana a Cikin Bola, Mu kadai muke rayuwa Mutane basu son mu basu son su Bamu Abinci Sun gummace su Bama kare akan su bamu, Yara masu shekaruna suna tsoron mu, suna jifan mu, Malam dan Allah akwai mutane irin mu a duniyar nan?, Dan Allah idan akwai irin mu ka kaini wajensu ina so muyi wasa tare, muyi dariya tare mu shiga Bola tare mu hana masu kuɗi irinku aikata mana irin abinda akayi ma Mero, Mahaukaciya ma anshayi mata hakan a gabanmu"

Sai ya dakata yana kai Dubansa kan Mero da ke kwance tana sauke numfashi a hankali, Mahaukaciyar ta ɗora kanta a kafaɗarta tana bacci ,shuru ya Ratsa wajen na wasu yan sakanni Bukhar na ƙoƙarin hana Tausayin Bayin Allahn Tasiri a zuciyarsa yayinda ,zuciyar James ta daɗa ƙosawa da zaman shi a Asibitin Burinshi ya Naɗi rahoto ya ƙara gaba ,kukan da yaron ya Kara kecewa dashi ne ya dawo dashi hayyacinsa,ya dubeshi

"Kukan me kakeyi?"

Sule ya girgiza kai Hawaye na daɗa Zubo masa, James ya sauke ajiyan Zuciya

"Ya Sunan Yar Uwarka?"

"Mero "

"ITA kuma taya akayi ta samo wannan sunan?"

"Ni na sa mata sunan saboda Ina ssson Sunan, Sunan wata ce me siyarda hura a jikin Kangon da muke kwana, ta kan kai talla in ta dawo sai ta rago mana Shine kawai Nasa mata Ss...Sunanta"

_yaron ya cika in ina_

Bukhar Ya furta a ransa sannan ya mika masa hannunsa yana kara Saita Cameran sa a Jikin hannun da yayi gaja Gaja da Kuraje, sai ya nade hannayensa ya matsa baya yana Zare manyan Idanuwan sa , wasu hawayen har sun fara sauko masa, wani zafi ma yake jin zuciyarshi na masa saboda yawan tambayan akan Rayuwar su da yake.

"Ina mahaifin ku?"

Ya tsinci Muryar Bukhar, bayan Ya Gyara zamansa, da mamaki Sule yace

"Dama Muma Munada Mahaifi?"
Bukhar ya daga masa kai sannan yace

"Ina yake?"

"Ban sani ba, Ni ai na Aza mu Uku ne a duniyar mu ,malam dan Allah Ina zamuje Mu ganshi? ,A Ina Zamu Samoshi?, Inason Zama dashi "

Yayi Maganar cikeda yarinta da rashin Sani, yanda yake maganar cikin Natsuwa bazakace kananun shekaru gareshi ba, james ya kauda kai daga dubanshi Dan duk Rashin Imanin shi wannan karon Saida yaji tausayin yaran da mahaifiyar su ya darsu a Zuciyarsa ,Bukhar ma gwiwan sa Dada sanyi Yayi, James ya kamo hannun Sule cikin hannunsa ɗaya, ya ƙara matso da abin Maganar daidai Saitin bakinshi cikeda Salon jan Hankali da neman Suna  ya ce

"Share Hawayen ka ƙanina kaji, kaima mutum ne kaman Kowa, kuma zaka iya zama babban mutum irina, da yardar Allah zaka samu ɗaukaka Samada Nawa Mahaifiyar ka sai ta samu Lafiya itama Mero Allah ya Bata lafiya"

Sule ya gyada kai Murmushin da ya Mance Rabonda yayi irinshi ya Ƙwace masa, Dauɗaɗɗun haƙoransa suka bayyana, James yayi Saurin Kauda kai a ransa yana faɗin

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now