006

1 0 0
                                    

*Z* *A* *A* *N* *E*

*006*

A tare suka fito suna wuce masu tsaronsu ta kowane kusurwa na gidan ,Lokacin da idonta suka sauka akan Narka narkan Ƙattin da dake tsare da babban gate din gidan sai da taji gabanta ya fadi rass shekarunta Shida a Tareda su, kullum In zata fita sai ta hadu dasu, Amma sam ta kasa Sabawa da ganinsu, a duk lokacin da ta gansu sai taji gabanta ya fadi, bakake ne wulik dasu sanye cikin baƙaƙen kaya babu alamar imani a tattare da su, ga manya manyan bindigu rike a hannunsu , ga wasu ƙananun bindigu a ƙugun kowannensu.

Muƙut ta tattaro wani irin miyau ta hadiye ganin sun kafeta da idanu , nan take taji zufa na gangaro mata ta cikin sumar kanta, ta sake ƙanƙame hannayensa dake cikin nata , a yayinda shi kuma ya sake tsuke fuska, da zarar sunzo gotasu sai su damƙe Bindigoginsu suna rissinar da kai , kankameshi tayi Jikinta na rawa , ya mannata a Jikinshi sosai, Gabaki dayansu Suka sunnar dakai, Gudun ganin abinda zaisa Thaubaan ya koresu.

a haka Suka nufi wurin parka Motoci nan ma jami'an Tsaro ne birjik ta ko ina cike , cikin Sauri akazo aka buɗe masa ƙofa, tun kan yayi magana Driver ya shige yana shirin tada motar ya daga mai Hannu alamar ya bashi makullin Jiki na ɓari ya miƙa masa, yaja motar ya fice daga gidan, ya harba motar saman Titi, Tunda suka fito ba Wanda yayi ma ɗan uwansa magana, shi yanata driving Ɗinsa Nusaibah na kalle-kalle ta Window har yanzu tanajin zafin maganarsa na dazu, ko wannensu da irin karfin izzar da yake jidashi.

Sun Isa katafaren asibitin ido na ƙasar, inda take aiki mai kyawun gaske, inma badan sunan ASIBITIN Dake manne a saman katafarar Dogon ginin ba saika ɗauka wani ƙayataccen wurin shaƙatawa ne, asibitine babba wanda shiganshi sai manya manyan Mutane kuma aikin ido kadai Sukeyi aasibitin, parking Yayi ya dubeta yace.

"Zan jira ki"

Ta dago ta dubeshi Kaman zatayi magana sai kuma ta basar ta dau Labcoat ɗinta da jakarta ta Shige ciki tana daga masa hannu, murmushi yayi , yana son matarsa ko dan kyautatawan  da take mashi.

A zahiri Duk wanda yaga Yarima da matarsa zaiyi Ma kansa fatan Zama irinsa ta ko wane siffa, Kuma babu macen da bazata so ya zama uban ƴaƴan ta ba Saboda yanada kyau, Ga kuɗi ga mulki ga iya soyayya da ƙyakkyawan Alaƙa .

Saidai duk Nasabar sa Yana da Tawaya ta fannoni da dama ,Yarima duk kudinsa bai yarda yan waje suci albarkacinsa , hatta Dangin matarsa basu cin kuɗin sa baya basu ko sisi, saidai In an biyata  albashi takan raba albashin nata biyu Ta tura masu kashi daya sauran kashin kuma tayiwa dangi da abokan Arziki masu ganinta kaman Bangonta hidima ,kafin yareema ya aureta yayimasu hidima har gida Ya siya ma iyayenta saidai tun bayan auren ya samar mata aiki yace ita ya kamata ta basu daga guminta, zatafi samun albarkar iyaye a rayuwarta, tun daga wannan lokacin Ya manta da shafinsu kuɗin shi ya zama daga shi sai matarsa da yar ɗansa.

Ga izza da mulki  wanda ya wuce misali a ko ina jin kansa yake kaman wani sarki, dokokin gidansa da Mulkin da yakeyi a cikin gidansa ma sun wuce na misali,  idan matarsa zayi masa magana sai ya bata Umurni da ido, idan kuma bai bada umurni b duk mahimmancin Maganar dake bakinta fasa furtashi zatayi, idan kuma ta karya doka sai ya hukunta ta, dalili kenan da kukaga tana Ɗan shareshi, ba Izza bace, Kuma ba mulki bane saidai bin umurnin mai jida izza da mulki ne.

Rayuwarsa nada tsari sosai , yanada dokoki dadama, ranakun nuna  Soyayya ga matarsa ma daban yake  haka ranakun Mulkin Mallaka a cikin gidansa duk ya ware, tanada haƙuri sosai bata Son hayaniya shiyasa Suka zauna lafiya tun bayan Shekaru takwas da yin Aurensu.

Yana da saurin Fushi da halin Rikau ga kafiya , wadannan sune abubuwan da Suka yiwa  Thaubaan jiɓi a rayuwa, A zahiri ka kalli rayuwarsa bazakaga komai ba face Haske, amma idan ka nusa cikinta zakaga tsantsar duhun da yake ciki.
Talaka shike jure rashin mutuncin Miji Expecially ma idan yana da kuɗi.

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now