008

3 0 0
                                    

*Z* *A* *A* *N* *E*

*008*

Yana isa ya Hangota zaune tsakiyar Almajirai ta saka hannayenta bibbiyu tana cin abinci tare dasu a kwano ɗaya, tayi bake bake har wani ture su take tana kwasa tsabar haɗama ,Gidan Wani attajirin ɗan ƙabila ta rakasu sukayo bara Aka basu Tuwon semo da egusi, sannan Aka haɗa masu da ójo Abasha da Oro Okuyo, ji tayi Tunda tazo duniya bata taɓa cin abinci mai dadi kalar wannan ba..

Da ƙarfi kansa yayi wani irin sarawa, innalillahi Wainnailayhirraji'un, ya furta a fili sannan Yaja motarsa ya nufi wajen, a gabansu ya faka Motar saidai daɗin Abincin da santin da takeyi ya hanata kula da tsayuwar sa a wajen da ƙarfi ya kira sunanta.

"Hubbah"

A razane ta ɗago, ta Wani Zaro ido a lokacin da Idanunta suka sauka a kan nasa ,ta nufoshi a guje zata rungume shi ,Duban yanda take nufoshi yayi, yayi saurin dakatar da ita cikin tsawa irin wanda bai taba mata ba.

"Keh gidan uban wa zakije da kike nufoni?, Ke anya ma mutum ce kuwa?"

Baki ta saki tana Dubansa da tsananin mamaki, Tsoro da fargaba duk sun cikata , , ƙudaje sai kaikawo Sukeyi a Jikinta Warin Jikinta na dada busowa ,  tayi tsaye tana kyafkyafta Idanu kaman zatayi kuka tana fadi a ranta

"Ina ruwanka da Ƙazanta ta?, Kana min tsawa ina ruwanka da rayuwata?"

A fili kuwa turo baki tayi tana wani irin narkewa

"Shine zaka min tsawa"

Dubanta yayi daga sama har ƙasa Uniform din gado ne a Jikinta, sundaɗa yin Daga daga har sun fara sauya kala, fatar Jikinta har wani kauri na musamman suka daɗa yi tsabar ƙazanta da rashin wanka da Wari ,ƙarni, da hamami da yake buso mai ,yau kam bintou ta kaishi bango duk juriyar shi da hakurinshi yau ta ƙureshi, bazai iya ba, dole ya sama ma kansa mafita, Aslaaf ya girgiza kansa a ƙyamace cikin takaici ya ayyana a ransa ayau babu abinda zai hana yakai Bintou gidan mahaukata a duba lafiyar ƙwaƙwalwar ta, yanada tabbacin batada cikakken lafiyan ƙwaƙwalwa,Shuru tayi tana zare idanu, ya galla mata Harara ,Sai ta sake turo bakin nan gaba tana lasar hannunta cikin ranta kuwa Zaginsa take.

"Biyoni muje"

ya fada yana Nufar motarsa,Motarsa ya buɗe ya shiga ta buɗe ta shige ciki tana cigaba da salɗe hannu kaman zata cire yan yatsun hannunta,  take warin Jikinta ya haɗe da Sanyayyan ƙamshin motar ya bugo da wani irin wari mara daɗi.

Yarinyar tana sa masa damuwa dayawa, inba ƙaddara ba ina Bintou ta isa ta haɗa hanya dashi?, Batareda ya bata lokaci ba ya fara ƙoƙarin Tada motar cikeda ƙyamar kansa da na motar gaba ɗaya, bintou ta leƙa ta window ta dube Almajiran ta wage Murya tace

"Ku rage min abincina, Kun sannni ba mutunci ne dani ba,idan kuka cinye baku barmin ba zan iya bin mutum har gaban Malaminshi in Masa Dan banzan duka babu abinda ya damen,, ai bani na hana iyayen naku kula daku ba''

Tana fadar haka ta shigar da kanta tana cigaba da Tsotse yan Yatsunta, Aslaaf ya ja tsaki Cikin ɓacin rai ,lallai rashin jin Bintou ya shahara takaici ya hana Abdul cewa komai, Ya figi Motar ya kama hanyar Neuro Psychiatric Hospital na Zaria (babban Asibitin mahaukata na Zaria) wanda da Bintou Tasan inda ya kawota da tun farko bata yarda tabishi ba,kafin su isa asibitin kuwa ta kwaso damin gulman mutane kala kala ta Dire Masa dukda yau takaici ya hanashi tanka Mata Amma Bata Fasa ba.

Ji tayi motar ta tsaya ta ware idanu tana kallon Inda ya kawota, cikin sauri ta fito cikeda Farinciki tana tsalle, tsawa ya daka mata wanda ya sa ta natsu, sai yanzu ya bita da kallo sanye take cikin wannan Uniform din na Gado PCap din har ta koma ash Tsabar dauɗa , ƙudaje na Binta , ji yayi bazai iya shiga cikin Asibin da ita haka ba, amma da wani tunani yazo masa sai ya murmusa ya dauko wayarsa ya latsa wata Number.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 11, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now