007

1 0 0
                                    

*Z* *A* *A* *N* *E*

*007*
Da wannan tunanin ya miƙe, ya dau dayan wayansa da Recorder ya fice izuwa Gidauniyar da suka karɓi barkwancin Sule, saida aka tantance shi kafin a barshi ya shiga.

Kaman dai yanda suka ɗauko shi, yana nan zaune kaman Gunki , Gabanshi abinci ne nau'uka kala kala amma Ko kallon abincin baiyi ba , ya zubama wuri ɗaya ido,fuskarsa busassun hawaye ne shaɓe shaɓe,  yana sanye cikin farar riga mai gajeren hannu da blue jeans, Babu laifi yayi fasali ya fito a mutum ɗinshi saidai babu alamar kwanciyar hankali a tattaredashi.

James ya jawo Kujera ya zauna yana Fuskantar shi, sai a lokacin Sule ya ɗago ya Dube shi, kallon second ɗaya yayi masa ya kauda kai, James ji yayi gabansa ya faɗi Fuskar Bintoun Abdool ya gani Manne a fuskar yaron, da sauri yasa hannu ya ɗago fuskar ,ba fuskar bintou bane saidai tsananin kamanninta da yaron har ya ɓaci har baisan sanda ya tambaye shi.
"Sulaiman kasan wata bintou"
Banza sule yayi mai, shuru ya ratsa wajen, James ya cigaba da kallonShi cikin tsantsar mamaki.
"Me yasa ka dawo?"
Ya tsinkayi Muryar sule kaman daga sama, saidai har yanzu bai kauda idanunsa daga kallon inda idanunsa ke kallo ba.
Sai James Ya samu kansa da amsa masa yana kallon fuskarsa, 

"Nazo ne dan Na dau Bayanai akan guduwar mahaifiyar ka"

Sai ya Lumshe ido a hankali ya juyo ya kalleshi, ya sake maida idon ya kafe waje ɗaya da kallo.
Shuru ya ratsa wajen na yan sakanni, take hawaye suka fara sauko mai Jikinshi ya hau rawa, abubuwan da suka faru a wannan daren suka sake ziyartar ƙwaƙwalwar sa.
"Idan kana bukatar wani abu ka faɗa min kafin na fara maka tambayoyin"
Ya kalleshi jikinshi na cigaba da rawa hawaye na sauko mashi.
“Me zaka tambaye ni? Yanda suka kashe MERO a Gaban Ido na? Ko yanda suka sumarda mamana? Ko kuma kana so na sake gaya maka komai su sake aikata abinda suka aikata?”
Shiru yai yana kallon yanda idonsa dake zubarda hawaye fararen idanunsa sun koma jazir kaman gauta  tsabar kukan da yake yi, muƙut James ya haɗiye yawun bakinsa tare da maida numfashi a hankali.
“Ka kwantar da hankalinka babu abun da zai sake faruwa , kawai ina son na tambayeka abinda ya faru a daren ranar da Mahaukaciya ta bar Asibin da MERO ne"
Sai ya kai Dubansa kan tulin abincin da aka kawo masa
"Kaci abinci?"
"Bana jin yunwa"
Ya bashi amsa, laɓɓansa  a bushe dan har sun fara daddatsewa, ga wani irin fari da yayi kana ganinshi kasan yunwa har ta fara masa illa, James ya taɓe baki hadi da dage kafadarsa.
"Tho ka bani amsata, me ya faru a ranar?"
James ya faɗa yana ƙara Saita mai abin magana.
"Malam dan Allah ka tafi..., Ka tafi dan Allah bana son ganinka,Dan Allah ka bar ni da damuwata, ka bar ni na ji da abun da yake damuna , azabar da kasa aka gana Min ya isheni Haka ya Ishe Ni ka tafi , dan Allah ka fit...."
Ya kasa karasawa saboda kukan da yafi ƙarfin shi numfashinshi yayi sama, jikin James yayi sanyi a karo na farko da ya ba zuciyarsa dama tausayin yaron ya samu mafaka a cikin Zuciyarsa, duk maitarsa da san sanin musbbabin guduwar Mahaukaciyar dole ya haƙura ya fice yana sake sake a ransa, haka bai daina mamakin kamannin Bintou da ya gani a fuskar Sule ba.
Sule na ganin Fitarsa yaji duniyarsa ta koma sabo, kadaici Da kewan Mahaifiyarsa da ƙanwarsa suka dawo masa sabuwa, tunowa yayi da Yanda aka ketawa MERO haddi a gabansa babu wanda ya damu dasu, kowa burinsa yasan abinda ya faru a sami na yaɗawa,babu wanda ya damu yaji Labarin sa dan ya taimaka masa, rayuwarsa da mutuwarsa duka daya ne, saboda shi ba kowa bane.

Idanunsa yakai kan Abincin da aka kawo masa tun da safe baici ba kuma babu wanda ya damu, ji yayi rayuwarsa tada tare da Mahaukaciyar mahaifiyarsa da kanwarsa ya fiye mashi nan sau dubu,ko bbu komai idan baici abinci ba MERO na nuna damuwarta, basuda Damuwar da ta wuce farantawa junansu da nemowA kansu abinda zasu ci ,sunyi rayuwa a inda babu katanga Babu tsaro, jikkunansu sune Abincin sauraye , sun kwanta a inda idan akayi ruwa a jikinsu ake farawa a kuma tsayar a jikinsu, Guguwa iska da hayaƙi duk sun ƙare a kansu, amma yau gashi a daki mai rufi yana fatan komawa wanchan Rayuwar, zaiso Ya kwanta a Bola Tareda ƙanwarsa da mahaifiyarsa akan ya zauna anan da ake masa barazana da rayuwarsa, duk irin rayuwar da sukayi bai tabajin ya Tsani duniyar ba kuma ya fidda rai akan komai ba sai yau, sai yau yasan bashida amfani mutuwa ce ta dace dashi.
Yana kaiwa nan a tunanin shi ya miƙe zumbur ya nufi wajen window kaman wanda ake controlling da remote ya nufi wajen window, ya diro, hankulan ma'aikatan Wurin baya kansa saida ya isa bakin Gate ya Bude zai fita aka ganshi security ya dakatar dashi da sauri, saidai ina Sule bayaji baya gani So yake ya mutu ya bar duniyan ya huta.
Da gudu ya karasa ficewa Duk suka rufa masa baya a guje hankula a tashe suna Ambaton sunanshi , bai tsaya ko ina ba sai a tsakiyar Titi daidai lokacin da Wata ƙatuwar Mota tazo wucewa duk yanda mai motar yaso dan kaucewa Sule ya kasa , saida motar yabi kansa.
Innalillahi Wainnailayhirraji'un

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now