The cake

40 1 0
                                    

MATAR FARKO
Written by

   SHAMSIA A LABBO (Mrs Dallatu)

@wattpad NanaShamsia

Page 19📖
*************************
Banason Mamanmu tagane maganan da Abdallah keyimin sai nace masa zankirasa ana kirana,  natashi zanfita ina bude kofa Abbanmu na qoqarin shigowa , nasauke wayan daga kunnena nakoma gefe dan bashi hanya yawuce tsayawa yayi yana kallon Mamanmu datayi kamar batasan yashigo ba, shiga dakin yayi nikuma nafita, ina zuwa palo banga Jidda ba sai qannena da suke cin Abinci, nashiga dakinmu  nayi sa'a Aunty Ruma bata nan hakan yasa nayi dialing numbansa yana fara ringing yakashe sannan shi yakirani, sai na wayance nace masa

"Abdallan na,  naji kamar  kana  maganan Niqab dazu"

"Yes, nace inaso from now henceforth idan zaki fita ki taimakeni kiringa saka Niqab da dogon hijab and socks, am not giving you an order, roqonki nakeyi Fatima, saboda da hakane kadai mazan dake kai miki hari zasu daina, kuma ni zan aureki baki buqatan kowa yaga kyaun Fuskarki, dan Allah Fatima ki taimaka ma zuciyata, jiya nadauka zan iya fushin rashin magana dake amma nakasa, Allah kadai yasan irinson danake miki, gobe zanzo Kaduna gurinki zankawo miki hijabai da niqab din kinji? Please do this for me My Love..

Kamar kazar da aka tsoma a ruwa haka jikina yayi saboda gabadaya kalamarsa sun narkar min da zuciya, rabona da niqab tunda nayi sauka a islamiyya, kuma ba cika sonshi nakeba saboda idan nasa  inajin numfashina yana sama sama da kyar na iya sabawa, toh amma ya zanyi son da nakema Abdallah yawuce misali.. jina shiru da yayi ne yace

"Fatima are you there?? Na takura miki ko? Idan kuma kinga bazaki iya saka niqab ba yanxu shawara daya yarage?  Ajiyar zuciya nayi ina adduan Allah yasa tafi tafarko sauqi

"Wace shawara ce"

"Zan turo iyayena  a daura mana aure nan da sati daya, tarewa sai yabiyo baya, saboda zamu wuce Turkey da Mr president inaso in tafi hankalina a kwance nasan kinzama tawa nikadai"

Dim dim dim haka zuciyata ke bugawa miyau bakina ya bushe sai zufa kamar wacce aka kama da gagarumar gulma, da kyar na iya hada kalaman bakina nace

"A-a-aure fa ka-kace nanda sati daya, da dai kayi hakuri kadawo abi komai ahankali zaifi kamar ko"

"Bazanbi komai a hankali ba, lokacin da nabi komai ahankali ba ga irin sakamakon da nake ganiba  kin fara kula maza, wai kina ganin kina Kmin adalci ne Fatima, ko kinmanta tun yaushe nake binki maganan aure sai maidani dan iska kikeyi, yanxu nabaki simple option duk kin kasa bi, idan sona ne kika daina kifadamin in daina kashe kaina akanki, kuma magana taqarshe Wallahi Wallahi Fatima idan har bakiyi picking daya daga cikin options din dana bakiba kimanta kinsan wani AA Tafida nima zan mantaki ko da sonki zaizama ajalina"

"Wallahi bazan taba daina son...

banqarasaba yakashe wayar, kasa sauke wayar nayi a kunnena hawaye suncika min ido, wai ni yazanyi da raina ne dagaa wanan sai wanan, a haka nazauna ina hawaye Aunty Ruma tashigo, hankali tashe tazo kusa dani

"Subhanallah Nayla meyafaru haka, kukan abunda Jidda tayine haryanzu bikiyi shiru ba, kefa matsalarki kenan kinada saka abu a rai yayita damunki, duk abunda tayi ai tayima kanta ko, kiyi hakuri ki share hawayenki komai zaiwuce In sha Allahu kinji, taso ki dauraye fuska muje muci abinci.." kasa cemata komai nayi saboda bazan iya fada mata ga abunda yafaru tsakanina da Abdallah ba, share hawaye na nayi nace "Aunty Ruma banajin yunwa kije kawai kici, banida appetite a bakina, inaso in dan kwanta ne ko zuciyata zatai sanyi" cikin rashin jin dadi haka tafita takoma palo, tana fita wasu sabbin hawayen na gangaromin....

************
Bayan Abbansu yashiga ne yarufo qofar tareda saka makulli, yazo dab da ita yazauna, hanunsa yakai zai dafa kafadunta sai tayi saurin cewa

MATAR FARKO (by Shamsia Abdallah Labbo)Where stories live. Discover now