The Twins

40 3 3
                                    

MATAR FARKO
PAGE 84

Wattpad @Nanashamsia

        EID MUBARAK NOVELLAS  🎉🎊🎈

(Kunji ni shiru ko, yaranku ne ya jefa wayar a ruwa sai da aka gyarota🤦‍♀️, bayan nan kuma na dan yi rashin lafiya amma Alhamdulillah komai yayi daidai yanzu, nima ba qaunar ji na shiru da kukeyi nakeyi ba, saura few pages dai a gama MATAR FARKO ku huta nima in huta 🤭🤭 gaisuwa ta musamman ga WATTPAD Family da kuma yan WHATSAPP GROUP dina , Nagode da qaunar da kuke mini da rubutuna❤️sannunku kuma da haqurij jira🥹)

*************
NAYLA

Tunda Baba Umaru ya sanar dasu Iyayen Muyassar amsar dana bayar nake cikin tashin hankalin kiran da Abdallah yake min babu qaqqautawa, tsoro ma abun yafara bani saboda nasan ba kiran alkhairi bane kuma ta wani bangaren zuciyata inajin babu dadi na fasa aurensa danayi, "ko dan Fasiqancinsa ya isa ki haqura dashi Fatima, Allah zai dubek yabakinagari In sha Allah" daya daga cikin maganganun da Mahaifiyara tayimin bayan na yanke shawaran fasa aurensa, na tabbata shi ne best decision din da nayi making ga kuma adduan danakeyi akan Allah ya zaban mini mafi alkhairi a rayuwata..

  Nayi mamakin irin qarfin halin da na tsinci kaina dashi saboda banji tashin hankali ko fargaban rasa Abdallah ba kamar yanda nake tunanin zan kasance a baya idan har narabu dashi saboda tarin qaunar danake masa, lallai addua takobin mumini ne don nasan shi ne garkuwa ta..

   Na yanke shawaran daukar wayarsa komeye ma zai fada min am ready nasan dai raina ne zai baci, ina dauka wani irin zagi ya mulmulo min sai danakusa yarda wayar saboda firgici, sake duba numban nayi dakyau na tabbatar Abdallah ne ya kira ko kuwa wani bamaguje ne yakirani  bansani ba, maida wayar kunne na nayi nace
   "Abdallah ni fa kake zagi"
   "Ke din banza ke din wofi, mayaudariya azzaluma, ni zaki ruguzuma rayuwa? Saboda wancan sakaran shashashan Ya hure miki kunne akaina ko, toh Wallahi both of you sai kunyi regretting, zakisan bakowa ake yaudara ba, sai na tarwatsa ku Fatima, and i hate you  natsane ki, ina duk promises din da mukayi ma junanmu cewa no mattaer what bazamu rabu ba? Ashe qarya kikeyi, har wani outsider zai shiga tsakaninmu"

     "Ban yaudareka ba Abdallah and.."

   "Don't tell me rubbish, idanma yaudara kikayi ba uban meye kikayi? Ya sunan abunda kikayi eh tell me."
  
    " ok idan yaudararka nayi Kai kuma abunda ka boyemin ya sunan shi??"

    "Woww Lallai Fatima, so har zamanku da Ahmad kinsamu guts irin haka, nawa mistake ne kuma kowa zai iya yin mistake"

     "Mistake ne yasa har taqara samun ciki na biyu duk babu aure?..

    Sai a lokacin ya dan yi shiru na wani sakanni da alama yaji mamakin maganar, cikin muryar dake nuna jikinsa ya danyi sanyi yace

    "Ita Layaan din tafada miki tanada ciki na biyu?"

    "Hmm" kawai nace  nayi shiru don nima bansan taya Baba Umaru yayi bincike yagano komai akansa ba, katseni yayi da cewa

     "Yanzu Fatima ko yara goma gareni babu aure nadauka soyayyar da kikemin zai saka kiyimin uzuri, kodayake ba laifinki bane Zugar Ahmad ne ke yawo akanki da munafikin da yaje ya binciko qarya da gaskya"

Nan fa naji wani zuciya yataso min na miqe tsaye nace      "Ya isheka haka Abdallah, Zagin ya tsaya akaina haka karka tabomin iyayena, Wallahi zakayi mamakina"

   Yanda shima yake sauke nannauyan numfashi sai kadauka  fada yayi da wani garwurtaccen  zaki yace
 
  "Do your worst, nafada koma waye yaje ya binciko abunda babu ruwansa munafiki ne kuma Allah ya isa ban yafe ba"

   Ganin kamar ma bai cikin hayyacinsa don gabadaya maganarsa kamar wanda ya haukace sai kawai na kashe wayar bayan yagama zazzago min kwandon rashin mutunci, Tabbas na tsorata da kalamansa nasan irin zuciyar Abdallah idan ya baci komi ma zai iya aikatawa...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: 5 days ago ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR FARKO (by Shamsia Abdallah Labbo)Where stories live. Discover now