77

37 5 1
                                    

MATAR FARKO

MYSR

Komawa yayi cikin asibitiny tarar da angama ma Mubin checkup din komai da komai, Dr ya tabbatar masa da cewa a duk gwajin da sukayi masa lafiyarsa qalau babu abunda suka gani na wata matsala tattare da shi ba..shidai jin Dr din kawai yayi shi yasan Mubin yanada matsala ko ba ta qwaqwalwa ba yaron dai ba normal yakeba

   haka suka baro asibitin Mubin ya ishe shi da surutu shikam hankalinsa gabadaya yatafi gurin Nayla da tunanin anya zata karbi soyayyar sa cikin sauqi kuwa, musamman yanda Abdallah yayi rugurugu da zuciyarta , idan kuma tasan abokai ne su qila ta qara nisanta kanta daga gareshi, idan kuma ta haqura da abunda Abdallah yayi mata sukayi aure shikenan yarasa ta kenan ! Anya zai iya jurewa kuwa, da yasan haka lamarin soyayya yake da bai afka ciki ba! Saidai zuciya bata shawara lokacin da zata fara son wani, don shikam ji yake idan Nayls batayi accepting dinsa bai san ya zai kasance ba, ballantana ta auri Abdallah, yayi nasara akanshi a karo na biu kenan "Ya Rabbin Alamin" ya fada yana dafe kansa da yayi masa nauyi saboda tunani...
  
     "She will accept you karka damu, itama tana sonka "  kaman daga sama yaji Mubin ya fada yana dafa kafadarsa, saurin kallon sa yayi lamarinsa na qara daure masa kai, taya akayi yasan me yake tunani? Anya Ummu Full mutum ta haifo kuwa!

    Cikeda sanyin jiki yayi ajiyar zuciya baice masa komaiba, kiran Ummu ne yashigo wayarsa yana dauka yasan ba lafiya ba yanda yajita,

    Daga chan bangaren Ummu muryarta na rawa take fada masa rasuwar babansu Nayla, wani irin kidimewa yaji yayi, tausayinta yagama mamaye masa zuciya , lallai tana ganin jarabawa! Dazu suna waya tanata dariya yanzu Allah kadai yasan irin kukan da takeyi, ga shi dama Abdallah yayi mata damejin zuciya, ina ma yanada dama ya dauke mata duk wnan damuwar da ya tunkaro ta!!
   Itama Ummu yasan tana chan tana kuka , shi kam ya tsani kukan mace, baiso yaga mace a damuwa ko kadan ballantana fitar hawayensu wani irin tausayi na musamman yakeji akan mata! 
    "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, what happened to him ? Dazu mukayi waya da ita fa!"

    "Hatsari akace yayi a chan Lagos, yanzu zamu wuce gidan"

      Bayan sungama waya da Ummu har yayi dialing numbar Nayla sai kuma yayi saurin kashewa yasan sautin kukanta kadai zaiji a yanzu...
   Dukansu jiki a salube suka koma hotel din inda suka baro Mansoor...

     Washegari jirgin safe suka baro qasar Turkey  zuwa Nigeria basu zarce ko'ina ba sai gidan rasuwa

Kamar wasa rasuwar Abbanmu ya karade yan uwa abokan arziki da yan gari,   Kafin kace mey Yan uwanmu na katsina da Bauchi duk sun iso,gidanmu yafara cika da mutane sai a lokacin muka qara tabbatarwa dagaske fa Abbanmu yatafi yabarmu, tafiyar da babu dawowa har abada, inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!

   Hankalinmu baigama tashi ba saida aka kawo gawar Abbanmu , tashin hankali da ba a saka masa rana, sai a lokacin Mamanmu ta fashe da wani irin kukan da bantaba ganin tayi ba, fadi take "nayafe maka Yusuf, Wallahi nayafe maka , bantaba riqeka a zuciya ba Yusufa kai mutumin kirki ne, katafi kabarni da marayu yazanyi dasu?

    Kowa dake gurin babu wanda baiyi qwalla ba! Hajiya kakarMu kam suman ta yakai uku! Baba Umaru da qyar aka bambaresa daga jikinsa rana nafarko danaga hawayens kenan!!

tafaru taqare anshafe babin Abbanmu har abada!
 
     Tunda Ummu tazo nake jikinta ina kukan da nakasa controlling din kaina, lallashina takeyi itama tana hawaye, bantaba jin zafin danakeji a zuciyata ba irin na yau!

***********
HAJIYA NAFISA

Ihu takey ba qaqqautawa tana kiran sunan uwani da yan biu, suna shigowa tayi shiru da ihun tana waige waige cikin rud'ewa, Mamaki yakama dukansu amma banda Amira don tasan meyake faruwa..

   Kuka Ummita ta fashe dashi tace
   "Abhi Wai meke faruwa da Hajiya ne? Kodai asiri akayi mata ne??  This is 3rd time tana irin abunnan fa, mukaita asibiti kawai"

  Nazarin Hajiyar yake tayi qwaqwalwarsa tana hasaso masa abunda baiso ya yarda,
  
     "Ku kamata muwuce asibiti kawai, something is definitely wrong"

  "Waye za aka asibiti? Ni lafiya ta qalau wani mugun mafarki nayi da Uwani, dama andade ana cemin Mayya ce banyarda ba!"

   Shiru sukayi dukansu sun kasa cewa komai , sai Abba da yace "shikenan Allah ya kyauta, ni zamuce gidan rasuwa Baban yar gidan Ummu yarasu sai nadawo"

  Sai a lokacin Amira taji rasuwar baban  Nayla, dukda tana jin haushinta amma ta tausaya mata ko bakomai tasan zafin rashin iyaye...
  
     Suna fita Hajiyar tasu tarufo qofa tana dialing numbar Aunty sa'a , saidai duk kiran da tayi bata dauka ba, cikin hanzari tadauki mayafi tace ma Ummita ta kaita gidan Aunty sa'a cikin rashin sa'a suna zuwa basu sameta a gida still, haka suka sake juyowa  a hanyarsu ta komawa Ummita cikin fargaban amsan da zataji daga gurin Hajiyar tasu tace

    "Uhm Hajiya nace ko zamu biya asibiti kigaida Junaid da jiki?

    "Shi Junaid din qanin ubanki ne ko qanin ubana ne?

    "Ba kodaya Hajiya wai dama naga.."
 
  "Kika ga uban mene? Wallahi kiyi hankali dani kar in juye abunda ke min yawo akai akanki, don ma  nabari kunje dubasa shiyasa har zaki samu daman min zancen banza ko"

     "Allah yabaki haquri " Ummita tafada tana ji kamar tayi kuka...

  Haka suka koma gida har washegari babu kiran Aunty sa'a ba labarinta....

  *******
A chan gidan rasuwa kuwa anata amsan gaisuwa sai ga Abdallah shima yazo, kallon kallo sukayi da Muyassar kowa ya watsar da kai gefe, tashi Abdallah yayi ya nufi cikin gidan don yi musu gaisuwa yana shiga sai gashi sunfito da Nayla tare , sai da ya tabbatar sun tsaya  setin inda Muyassar zai hangosu yayi yana aika masa wani irin miskilin murmushi,  ahankali yakira sunanta, kauda fuskatan tayi gefe tana goge hawayen dake Zubo mata batareda ta amsa ba tace masa

     "Daraja d'aya kaci shiyasa nafito kafad'a abunda zaka fad'a min zan shiga"

     "Nasan ban chanchanci daraja ko qwaya daya agurin ki ba Fatima, yanzu banda daman magana tunda hankali bai kwanta ba, but zuwa nan gaba zan miki bayanin komai kinji? Don Allah idan nakira ki ki dauka promise me that"

     Gyada kai tayi zata wuce yay saurin ce mata
"I love you so much, Allah ya gafarta ma Abba"

   "Amin" tace a taqaice sanan tajiya tawuce
shikuwa Muyassar  neman sukuninsa yayi yarasa, zuciyarsa na tashim boma bomai gashi yakasa dauke idonsa akansu dukda yayi qoqarin hakan, wani zafi zafi sanyi sanyi jiri jiri yaji yana kamashi ganinsu da yayi a tsaye ga wani irin matsanancin kishi da baisan yanada shi ba, ji yayi kamar yazama tsuntsu yatashi yaje yafizgo ta agabansa..
 
     Byan wasu yan mintuna da tsayuwarsu sai yaga ta shige shikuma Abdallah yana tunkaro inda suke zaune...

MATAR FARKO (by Shamsia Abdallah Labbo)Where stories live. Discover now