30

48 2 0
                                    

Wattpad @Nanashamsia
MATAR FARKO
  
        Page30

********************
Kallonta yakeyi yana mamakin yarintan ta yace

" Hmm amma kece yar auta agidanku ko" yafada yana cire ribbon din da tasaka masa ya miqa mata, amsa tayi tana  kallonsa tana mamakin ya akayi yake aikin napep da irin wanan haduwar tashi.

"dole inje inyi aski anjima" yafada batareda yasan taji ba, dasauri tace

  "Dan Allah karkayi just wash it ayi maka style irin na actors din korea zaka saje dasu please please" tafada tareda hada duka hannyenta biyu tana roqarsa, tsayawa yayi yana mamakin rigimarta, taya yana magidanci zaiyi aski irin wanan, girgirza kansa yayi yana daria sannan yaci gaba da tuqi, duk bayan wasu mintuna take sa hanu ta hargitsa masa gashin, sai yayi kamar zai mata masifa sai yaji daria tazo masa saboda bai taba haduwa da yarinya mai rigima da qarfin halinta ba..suna isa tasauka tace
" qarfe biyar zaka dawo kamaidani"

"Wai nazama driver dinki ne?"

"Yess  buzu boy , kuma dole kadawo don bazan baka kudin ba" har tajuya zata tafi sai kuma tadawo ta sake hargitsa masa gashin tawuce tana dariya cikin nishadi..sake baki yayi yana binta da kallon mamaki.."buzu boy" ya maimaita yana dariya domin shima tasaka shi nishadi, haka yakeson Bintun sa tazama so lively and jovial amma ita sam magana bai dameta ba.. gida ya nufa don yin wanka da hutawa kafin biyar tayi yadawo yamaidata gida...yana shiga suka ci karo da Adama itama zata shiga gidan, kallonta yayi yaga irin kwalliyar da tasha shikam yaushe rabon ma yaga kwalliyarta ransa ne yabaci saboda bata tambayesa zata fita ba, Sai da yabari suka shiga dakinta yace

"Ina kikaje batareda da sanina ba?

"Ina ruwanka da fitar danayi, kana kishi nane ballantana har kadamu" zama tayi tana ciro kayan ciye ciye cikeda leda , su ice cream dasu meatpie harda qasashiyar kaza, tashin hankaline ya bayyana a fuskarsa, wani zafin kishi na taso masa yace " Ina kika samo  abubuwan nan Adama? Gidan ubanwa kikaje sarkin kwadayi, tun last week fa kike wasu abubuwa da Bangane kanshi ba shiru kawai na miki inga gudun ruwanki"

"Bawani kaga gudun ruwana kishina ne dai bakayi, da wancan yar iskan matar taka ce ai da sai ka kusa haukacewa saboda kishi, donma kasamu zankadediya dani  ina qaunarka dukda talaucinka, kuma dama maza iri biyu ne, ko mummuna da kudi ko kyakkyawa talaka, abokanka gabadaya babu wanda baya cikin wadata sai kai, kuma tunda kayi karambanin qara aure da qanana shekarunka ai kasan wahala zakasha, kuma ka tashi ka auro wancan mai farar qafar abubuwa suka qara matsewa, anyi addua anyi addua amma shiru, haba ni nagaji tsakani da Allah, yanxu idan naga qawayena har boyewa nakeyi"  tsayawa yayi yana sauraronta maganganunta gabadaya sun juyar masa da kai, baisan lokacin da yashiga daki yadauko tsohuwar dorina ya nufota dashi ba, da gudu ta kwasa tashige dakin inna yabiyota

Tana shiga tayi sama da garin danwaken da Aka kawo ma inna daga niqa, salati tafari ganin kusan rabin garin yazube a qasa, " na shiga uku ni Latti, Yarinya tajamin asarar dukiya, ke Adama a rayuwarki meysa bakida natsuwa ne wai"

  "Toh ba yaya bane yabiyoni zai dukeni" sai lokacin ita innar ma ta kula da Junaidun a tsaye a qofa sai huci yakeyi kamar zaki, yana wurgoma Adama wani kallon takaici mai cikeda kishi

  " Kai Kuma me tayi maka zaka duke 'yar marainiyar Allah, hala akan Bintu ne ko? Toh wllhi baka isa ba"

  "Inna tafada miki da bakinta abunda tayi"

"Wai inna daga na tambayesa unguwa yahanani shi ne nace masa ai inda Bintu ce zai barta taje shi ne wai meysa zankira sunanta"  da sauri ya kalleta jin qaryar da tayi,?shigowa dakin yayi yana qoqarin jawota ya zuba mata dorina, inna ta shiga tsakaninsu tana masifa "Junai, yanxu a gabana zaka duke marainiyar Allah saboda bakada hankali soyayyar Bintu ya rufe maka ido? Nan inna tashiga tafa hanu tana salati sai kuma tafara kuka tana goge ido da gefen zani..kallon Adama kawai yakeyi maganarta nayi masa amo a kunnuwansa, jefar da dorinar yayi yafice batareda yace komai ba..

MATAR FARKO (by Shamsia Abdallah Labbo)Where stories live. Discover now