34

49 1 0
                                    

MATAR FARKO
   PAGE 34

      Shamsia Abdallah labbo (Mrs Dallatu)

Wattpad @nanashamsia

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

NAYLA

Ina cikin  cin delicious din da Ummu takawo min, kiran Abdallah yashigo, ajiye abincin nayi na dauka da hanzari saboda missing dinsa danayi, bamu dauki dogon lokaci muna magana ba yacemin zai kirani back, ajiye wayar nayi inata jiran kiransa sai naga video call din Mubin ta whatsapp yashigo, bancika son VC ba amma ganin Mubin ne yasani dauka saboda jininmu  yahadu, inayin picking wannan gorgeous smile dinsa yafara min Sallama, sai da gabana yafadi at first nadauka Muyassar ne, fuskarsa na kalla sosai naga kamanninsu  saidai shi yafi Mubin hasken fata kuma shi  Mubin baida dimple, sai wushirya irin tawa, tashi daga kwancen  da yake yayi yacemin

"Aunty mai kyau munbarku lafiya, hope i didn't intervene in your privacy"

  "No don't worry, you are always special to me, saboda kafi brother dinka kirki " nafada tareda murguda baki

Kasa riqe dariyarsa yayi ya qura min ido, cikin daria yace" Zan fada masa kina murguda masa baki fa, kuma kinsan he is very strong kamar shari'a" sai da ya tsagaita da dariyar yakuma cewa "Aunty Mai kyau Big Brother yafi kowa kirki a gidanmu, you just got to know him, idan jininku yahadu bazaki taba son ya matsa kusa dake koda na 1 minute ba, i don't know why you guys are  pretending "

"Am not pretending, he just doesn't like me"

"He likes you, misunderstanding ne tsakaninku and a little uhm"

  "A little what?

Shiru yayi yanata kallona da murmushi yace "Nothing,  bari in kai ma Big brother wayar ku qara gaisawa" dasauri nace "No no no , his eyes are scaring me ". Wane irin dariya ya tuntsire dashi har sai da nima nafara dariyar , sai kuma nasamu kaina da kallonsa inajin tausayinsa tuno da maganar Ameera "is he really psychotic? Na tambayi kaina,

  "Hello Aunty Maikyau what are you thinking"
Sai lokacin nadaw daga tunanin danakeyi nace

"Bakomai ina Ummu tayi bacci ne?
"No bari in kai mata wayar tashiga daki" da haka yatashi yanufa dakin ummu nikuma Aunty Ruma tashigo tanamin magana, komawa kan video call din nayi sai naga ya katse, sake kira nayi sau biu baiyi picking ba, komar da wayar nayi charge ina tsammanin kira daga wajensa amma shiru..

Palo nakoma sai na tarar da yan uwan Jidda sunzo suna gaisawa da Mamanmu da Aunty Ruma, Jidda sai duqar da kai takeyi kamar ta Allah, gaishesu nayi nakoma ciki ina dubawa ko Mubin yaqara kirana amma shiru sai naji hankalina bai kwanta ba saboda lafiya lau muke magana a video call din, qara kiransa nayi amma baiyi picking ba, dole na ajiye wayar na kwanta amma bacci yaqi zuwa, tashi nayi nawuce dakinsu Safna , ina shiga na tarar babu kowa a dakin, na kama handle din qofa zanfita sai naji vibration din waya, dubawa nayi naga banga komaiba ba ga vibration inaji, dai-dai inda nakejin qarar wayar naje , ina dubawa  sai naga haske ta qarqashin gado, ina duqawa nahango waya qirar Iphone 11 sabuwa gal, gabana ne yafadi saboda nasan cikin qannena babu mai wayar iphone a cikinsu, Safna ce mai waya infinix wacce mamanta ta kawo mata watannin baya. Daukar wayar nayi nataho dashi dakinmu batareda na nemi mammalakin wayar ba, koma waye zaizo yayi cigiya..

Bincika wayar nayi naga an saka password ga miss calls dayawa daga different numbers..

^^^^^^^^^
Jidda suna komawa sashenta yan uwanta sunata yaba Maman Nayla amma banda Aunty Fannah da tace " Wallahi kubar yabonta wannan daga ganinta makirci zatayi, irinsu ne suyita maka kisan mummuqe amma anfi tausayinsu saboda silent face dinsu, bafulatanin mutum da mugunta..Jidda karaf ta amshe zancen tace "Ai haka Matar Yayarsa inna Habi tace, ai dafarko naso yin shirme danake nuna kishina a fili, shi ne tabani shawara irinsu ta qarqashin qasa ake binsu anfi samun yanda akeso...babbar yayarsu  cikin fad'a tace "dalla yima mutane shiru ,ke yanxu har kinada bakin magana bayan duk da mugun halinki kinsamu ansake aurenki shi ne bazaki natsu ba kina biyema Fannah da wata Inna Habi, kekuma Fanna dama duk da goyon bayanki takeyin abunda takeyi, ku guji ranan qin dillanci dai, yanzu tsakani da Allah meye ita kishiyar Jiddan tayi muku da kuke nema cutar da ita? Kawai kuna Sha'awar daukanma kanku zunubi? Yanxu inda daya daga cikinmu kishiya zata cutar ya zakuji?? Auranta nafarko kun hada kai kun ruguza, wannan na biyun kuma tasamu kishiyar kirki kinason cutar da ita babu gaira babu dalili..daga Jidda har Aunty Fannah duk shiru sukayi suna sauraronta, amma zuciyar Jidda ko gezau baiyiba saboda irin son da taji yashigeta da zafin kishin da takeyima Baban Nayla bazata iya hadashi da kowa ba, tunda ita Maman Naylan tayi sake anyi mata kishiya ita bazata yarda tahada kishi da kowaba, ga uban dukiyan da tagani a gidan, da sannu sai ta korata ita kadai ta cancanta da Alhaji Yusufa...hakurin qarya suka fara ba  babbar yayar tasu ganin ranta yabaci sosai...

MATAR FARKO (by Shamsia Abdallah Labbo)Where stories live. Discover now