"Bon Appetite!"

953 83 19
                                    

Assalamu alaikum dearies ❤️

Fatan munyi azumi da sallah lfy. Allah ya karbi ibadun mu ya sa muna daga cikin yantattun bayin sa Ameen.

So, kamar yadda nayi alkawarin rubuta Safiyyah after sallah, gashi nan zanyi kokarin cikawa 😁. Ku dai ku taya ni addu'ar Allah ya bani ikon cikawar. Lol

Believe me, dama nayi niyyar yi ne on an impulse, sai daga baya kuma na fara cewa "anya kuwa?" But then na riga na fada muku and duk sanda nayi magana ina matukar kokarin ganin na cika ta, sai dai when it is beyond my control, as nobody is perfect. So, we will try insha Allah, but you will have to be patient with me idan an samu rashin update akan lokaci, ina so ku saka a ranku cewa ina iyakacin kokari na.

Kamar yadda na faɗa, littafin Safiyya hopefully zai zo a matsayin free tun daga farkon sa har karshen sa insha Allah, depending on in mun samu sponsors at least twenty, ku kuma readers ina rokon alfarmar ku bada haɗin kai wajen showing support to the sponsors dan suji dadin cigaba da siya muku littafin Safiyya kuna karantawa, idan babu sponsors, littafin Safiyya zai koma paid after the free pages.

I hope we will enjoy this journey tare da Safiyya and Gidado, it is going to be rough 😁, but I promise you a smooth landing.

*Episode One: Bon appetite!*

Breakfast is Served💔

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ina rokon Allah ya bani ikon rubuta alkhairi, ya hana ni rubuta sharri.

*Him*👳🏻

"Tell me you love me" yaji muryar ta ta daki dodon kunnen sa kamar a yanzu ne take yi masa maganar. Ya saka hannayen sa biyu ya toshe kunnuwansa sannan ya rintse idanun sa da karfi amma sai ya zama kamar kara clearing vision and hearing dinsa yayi. Abinda ya manta shine daga cikin kansa muryar take fitowa ba daga surrounding dinsa ba. A idonsa yana ganin fuskarta, as clear as the moon when it is full. A zaune a cikin motarsa, fuskarta dauke da murmushin da ya kasance tamkar maganin dukkan damuwa a gare shi, idanuwan ta cike da soyayyar sa.

"Tell me you love me" ta fada tana saita camera din wayar ta a fuskarsa, ya saka hannu daya ya kare fuskarsa yana murmushi. "Stop it!" Ya ce cikin muryar dariya, she giggled sannan ta chanja angle din camera din zuwa inda bai kare ba a fuskarsa. "Ka fada mana to, why are you shying away from a simple question. Do you love me?"

Ya bude fuskarsa yana kokarin frowning amma ya kasa, baya iya bata rai in dai yana tare da ita. Ya jingina kansa a headrest din kujerar motar yana kallon camera din tata yace "do you need to ask?" Tace "of cause. I want to hear you say it" ya lumshe ido ya bude yace "what is with the camera then?" Tace "as evidence. I want to record you say it sannan in ajiye as evidence yadda idan nan gaba ka ce baka so na ina da shaidar da zan shigar da karar ka zuwa kotun masoya".

Yayi dariya sosai yana kokarin ture camera din tata amma sai ta matsar away from his reaching hands, ta ce "confess! Say you love me" ya ajiye hannunsa ganin bata da niyyar bashi wayar yace "common! Why do I have to say it? Me yasa ke ba zaki fada ba sai ni?" Ta daga gira tace "because I say so... Kuma duk abinda nace ina so shi nake samu. Now I want you to say you love me". Ta karasa cikin turo bakin shagwaba.

Yayi ajjiyar zuciya "you are impossible Piya. Me zan fada miki ne wanda baki sani ba?" Tace "that you love me?" Yace "you already know that ai, you just enjoy.... enjoy.....en.." ta karasa masa cikin kwaikwayon muryarsa "you enjoy teasing me " sai kuma ta yi dariya. "You are right, na san dama ba fada zaka yi ba. I only wanted to see that" ta fada tana nuna fuskarsa, ya shafa fuskar kamar mai neman wani abu yace "see what?" Tace "your face is red my dear. You are blushing" ta karasa tana sake wata dariyar.

SafiyyahWhere stories live. Discover now