The Path of Destiny

680 58 13
                                    

For sponsorship,

contact 0704 203 0419 on WhatsApp

or

send a dm to my Instagram page

https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ==

Save my business number

0704 203 0419

and say hi on WhatsApp dan inyi saving naku.

Please, dan Allah, abeg, ban da kira

Ina fita na hango Mustapha yana tsaye a corridor din yana kallon kofar office din da na fito daga ciki, na dauke kaina nayi kamar ban ganshi ba na zo na wuce shi. Ya biyo baya na yana gyaran murya. "excuse me... Akwai mutum fa a tsaye tun dazu yana jiran ki" ban kalle shi ba ban kuma tsaya ba. Ya cigaba da bi na. "Nima bani na kawo kaina ba ballantana ki wulakanta ni. Cewa akayi inzo in jira ki in kin gama in mayar da ke gida, shi yasa na taho ba dan wai ina son hakan ba, kin san ni ina jin maganar Mommy da Daddy in sun gaya min bana tsallake wa". Na tsaya da tafiyar da nake yi na juyo ina kallon sa cikin ido, yayi murmushi, sai kawai na girgiza kaina na juya na cigaba da tafiya a raina nace he is not worth it, so yake in kula shi, in na kula shi kuma na bashi abinda yake so kenan.

Ya cigaba da bi na. "excuse me??? Motar tana can side ɗin ba nan ba. You have two options here dear little sister, you can either come with me in kai ki gida kamar yadda iyayen mu suka ce or you can walk tun daga nan har gida, and in your condition, that will be very impossible". Still bance komai ba nayi hanyar inda side din da na bar Daddy dazu. Ya cigaba "okay. You have another option to get home. Maybe zaki samu wani ya baki lift. It won't be hard for you. I mean you are use to it tunda har tsaraba kika samu saboda shiga motar mutane".

Na juyo a fusace na buga masa handbag ɗina a kansa, a raina naso ace tana da nauyin da zata ji masa ciwo. Ya dafe kan "aww. Me nayi? Daga fadar gaskiya? I guess ita dama gaskiya daci ne da ita" na juya na cigaba da tafiya ganin yadda mutane suka juyo suna kallon mu. Ya cigaba da bi na yana sosa inda na dake shi. "Kar ki damu. Na yafe miki. Ni bana fushi ai kin sani. Ko da zanyi fushi ma ba zan yi fushi da 'wife' ɗina ba. We will put all these behind us. Now, you will follow me muje in kai ki gida kamar yadda Mommy tace and in turn ba zan faɗa wa Daddy inda kika je ranar nan ba, ba zan bashi labarin me Tesla ɗin nan ba. I guess it won't be hard to trace him with that kind of a car, musamman in akayi considering da rashin girman makarantar ku. I bet shi kadai yake da irin motar a cikin makarantar".

Na dakata da tafiyar da nake yi amma ban juyo ba sai da na rufe ido na na ja dogon numfashi da fatan zan hana kaina sauke mari kyakkyawa akan fuskarsa, na juyo da murmushi a tawa fuskar ina kallon sa nace "look Mustapha. Daga maganganun ka na fahimci cewa you are yet to receive the recent memo. Daddy ya fasa aura min kai, because I told him bana son ka. So stop following me around and find a life. And also stop threatening me because it is not going to work".

Daga yadda yayi da fuskarsa na fahimci cewa Mommy bata gaya masa ba. Maybe tana fatan zata yi convincing dina na amince da auren so she thought he doesn't have to know. Yace "you are lying. You have always been a little liar" na daga kafada "of cause I am a liar, na sha yiwa mutane da yawa karya, people that matters a lot to me. But I won't waste my time lying to you because you are not worth it. In baka yarda ba ka tambayi Mommy" na juya zan tafi sai dai kuma har nayi taku biyu sai na tsaya na kuma juyowa ina kallon sa nace "and about cikin jikina. Ni na yarda akwai kiyama, na san kuma ni da kai zamu je can. A can ne kuma zamu karasa maganar".

Sai da na yi nisa sannan na fahimci baya bina, kuma sai a lokacin na fahimci nayi batan kai na bi hanyar da ba ita ya kamata in bi ba. Sai da nayi tambaya sannan na gane inda na baro Daddy. Ina zuwana tarar da Mommy a zaune a waje. Na karasa gurinta ina haki saboda tafiyar da nayi kuma da sauri. Ta mike tana goge min gumin goshina da hanky din hannunta. "Ya naganki a kafa? Ina Mustaphan da na tura ya dauko ki ya mayar da ke gida ki huta?" Nace "ban san inda yake ba. Ba gida zan je ba. Ya Daddyn? Sun gama?" Ta koma ta zauna tace "eh sun gama. Na gaya miki fa ba wani abu bane za'a yi masa mai wahala ba. Bacci dai yake yi yanzu". Na wuce ta na shiga dakin, na ganshi yana ta bacci kuma ko daga yanayin yadda yake numfashi na fahimci aikin da aka yi masa ya saukaka masa numfashin sosai. Na zauna a kujerar kusa da gadon na kama hannunsa tare da sauke ajjiyar zuciya nace "I love you so much Daddy. And everything is going to be alright" amma ni kaina da na fada sai naji ban yarda da abinda nace ba, saboda a kasan zuciya ta ina jin cewa, this is only the beginning, saboda zuwa yanzu na fahimci cewa "tragedy" is another name for my family.

SafiyyahWhere stories live. Discover now