The Choices 2

730 60 17
                                    

For sponsorship,

contact 0704 203 0419 on whatsap

or

send a dm to my Instagram page

https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ==

Save my business number

0704 203 0419

and say hi on whatsap dan inyi saving naku.

Please, dan Allah, abeg, ban da kira


****.    ****.     ****.    ****.    ****.   ****
Awa 8 da rabi mukayi muna tafiya kafin mu isa garin Berlin, Germany. Daddy ya zaɓi Berlin ne saboda anan ne babban abokinsa Uncle Sufyan yake zaune da iyalinsa. Akwai kuma likitan da ya kware akan ciwon Daddy wanda zai kula dashi a tsahon lokacin da zamu zauna a can. It was almost 8 o'clock pm when we landed a birnin na kasar Germany. Already muka tarar da Uncle Sufyan da dansa Abdul suna jiran saukar mu a airport. Muna haduwa da su Uncle Sufyan ya tarbe ni da murmushi "Safiyya, as beautiful as ever" na sunkuyar da kaina ina murmushi sannan na gaishe shi, duk sanda muka hadu dashi haka yake yi min, ya amsa tare da miƙa wa Daddy hannu at the same time yana cewa "duk sanda na ga Safiyya sai na tuna da Safiya, a rear gem. Har yanzu banga mace irin ta ba. Allah ya kai rahama kabarin ta". Mommy tace "Ameen ya Rabbi. Safiyya is a photocopy of her ai" Daddy ya dago yana kallo na yace "anya kuwa, sunyi kama dai a fuska, amma hali kam basu da dangantaka" na kalle shi muka haɗa ido nayi sauri na mayar da ido na ƙasa.

Abu biyu na karanta a idon Daddy a lokacin, akwai grief, wanda duk sanda akayi maganar ta sai na ga yanayin sa ya chanja, wannan yana daga cikin abinda yake kara min fahimtar irin soyayyar da yayi mata, yadda har yanzu, more than 20 years da rasuwar ta, amma bai daina jin mutuwar ta ta ba.

Abu na biyu kuma wanda yafi daga min hankali shine disappointment. Daddy was really disappointed in me. Gani yake kamar duk duniya bashi da wani disappointment da ya wuce ni.

Naji duk gwuiwowina sun sage, kamar kullum naji babu abinda nake so irin barin duniyar. A lokacin babban concern dina shine Allah ya sa hijab dina ya boye cikina tunda bani da tabbas din hosts din mu sun san da maganar cikin or not.

Daga nan muka wuce zuwa inda suka ajjiye motar su, sai da muka je na fahimci cewa motoci biyu suka zo dasu. Daddy ya juyo yana kallona yace "ki shiga motar abdul ya kai ki gidan su ki huta, mu zamu wuce asibiti" na tsaya ina kallon sa idona yana cikowa da hawaye dan naso ace na bishi asibiti anyi komai a gabana, amma kasancewar yanzu bana iya yi masa musu sai nace "okay Daddy". Na tuna da Safiyyan da, da ace seven months back ne, da zan iya rusa kukan da zai tara masa mutane a airport din idan yace ba zan bishi ba. Da ba karamin aikina bane in zauna dirshan a kasa in rike kafafuwansa ina kuka da dukkan karfina, amma yanzu sai nayi taku biyu baya na tsaya ina kallon sa ina kokarin rine kuka na. Ina kallo aka saka Daddy a bayan mota daya, Mommy ta shiga kusa da shi, yaya Mustapha ya shiga gaba sannan Uncle Sufyan ya zauna a drivers seat, aka barni a gefe ina rarraba ido.

Mommy ta sauke glass ta ce min "ki kwanta ki huta in kunje, ki sha maganin ki kuma, zan zo gidan in anjima" na gyada mata kai, Daddy kam ko kallo na bai yi ba suka tafi.

Sai da motar su ta bar gurin sannan Abdul ya ce min "okay. Daddy's girl. Nasan yanzu zaki kama kuka. Let me take you home tun kafin ki rikice min". Na goge hawayen da ya fito tare da ƙirƙirar murmushi nace "I am not crying" yace "of cause you are not. Maybe someone is cutting onions around".

Ya bude min kofar motarsa na shiga sannan ya rufe ya zagaya ya shiga side din driver muka dauki hanya. A hanya yana ta kokarin nuna min gurare amma ni bani da wani interest akan buildings and monuments dinsu, rayuwa ta kawai nake lissafa wa. Har sai da muka yi packing a gaban gidan su sannan ya juyo yana kallona yace "Safiyya, I want to use this opportunity da muke alone muyi magana. Magana nake so muyi as civilized people. Daddy na yace wai sun fara magana da Daddyn ki cewa akwai yiwuwar zasu yi mana aure" yayi shiru yana so yaga reaction daga gare ni sai yaga babu komai, ya cigaba, "so you knows about it kenan. Look, I want you to understand cewa I have nothing against you as a person, I like you. You are very beautiful and intelligent and I am very sure that akwai maza da yawa da suke layi suna son ki zabe su as your life partner. You can have any man you want. Wannan yasa na kasa gane dalilin su Daddy na bullo da wannan maganar. Gaskiya ni dai I don't want arrange marriage. Na fi son inyi aure for love. And I am sure ke ma haka. I know yadda daddyn ki yake son ki ba zai taba yi miki dole ba, and that's why I am begging you. Please idan an tambaye ki kice ba kya sona kamar yadda nima zanyi kokarin nunawa nawa daddyn haka. Let's join hands and fight this battle together. In kika yi min haka I will forever be grateful to you. I am sure kema kina da wanda kike so and I don't want to be the reason da zai saka a raba ku".

SafiyyahWhere stories live. Discover now