Mother

660 41 11
                                    

For sponsorship,

contact 0704 203 0419 on whatsap

or

send a dm to my Instagram page

https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ==

Save my business number

0704 203 0419

and say hi on whatsap dan inyi saving naku.

Please, dan Allah, abeg, ban da kira

Free page......

Knocking kofa ne da dawo dashi daga tunanin da yake yi. Ya mike ya koma kan kujera ya zauna yace "yes". Mama ce ta turo kofar amma sai ta tsaya daga bakin kofa tana karewa dakin kallo tace "ina Al'ameen ɗin? Ko ya fita bai yi min sallama ba" Gidado yace "ya fita, maybe ba kya kusa" ta karasa shigowa da bacin rai a fuskarta tace "ko bana kusa ai sai ya neme ni, saurin me yake yi? Ni fa na kira shi kuma sai ya tafi ba tare da na sallame shi ba" Gidado bai ce komai ba amma ya san shi ya jawowa Al'ameen wannan fadan tunda shi yace kar ya gaya mata maganar da suka yi, ya san kuma Al'ameen ya gudu ne dan baya so ta tambaye shi ya suka yi.

Ta shigo ta zauna akan gado tana kallon sa tace "ya jikin?" Ya ajiye carbin hannunsa tare da safa addu'a a fuskarsa yace "da sauki Mama, kar ki damu da ni. Zan je asibiti anjima" ta bata rai "in kaje asibitin me zaka ce musu? Ji nake dazu da na tambaye ka abinda yake damunka cewa kayi kwakwalwar ka ce take ciwo, haka zaka ce musu a asibitin? ta yaya zaka ce kar in damu? Ki yadda ka koma cikin kwana biyu, me yasa ba zan damu ba? Akan ka aka fara faɗa da budurwa ne wai?"

Gidado ya dago kai yana kallon ta, ya bude baki sai kuma ya mayar ya rufe. Shi bai san me zai ce mata ba. Baya son ya gaya mata abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya saboda baya son ta tsani Safiyyan, duk kuwa da cewa bata san ta ba. Wannan shine zurfin soyayyar da yake yi mata.

Yin shiru sa ya saka ranta ya kara baci. "Kai ba zaka gaya min ba kuma shima dana turo ya tambaye ka ya tafi bai gaya min ba. Wani abu ne mai muni ya faru? Ko wani laifin ka aikata kake boye min?" Yayi saurin girgiza kai tare da bude ido "no, Mama babu abinda nayi fa. Babu abinda ya faru, kawai bana jin dadi ne. Kuma zanje asibiti in an jima".

Ta dauki wayarsa daga kasa ta mika masa tace "idan har babu wani abu da ya faru kira Safiyya ka bani ita mu gaisa" ya rike wayar yana jujjuya ta. "Bata kasar, kiran ba zai shiga ba" tace "WhatsApp call nko? Shima ba zai shiga ba? Ko kuma da ta tafi wata kasar a matsayin ka na mai neman aurenta bata baka layin da take amfani da shi a can ba?"

Ya ajiye wayar akan cinyarsa tare da sunkuyar da idonsa kasa, abubuwa da yawa suna yawo a ransa. Ta kuma daukan wayar and kafin ya fahimci me yake faruwa sai ta kama hannunsa ta saka fingerprint dinsa ta bude wayar. Ya dago kai da sauri yana kallon ta, trying to process abinda yaje faruwa "Mama! Mama Please don't!" Ta juyo tana kallon sa tace "ko zaka kwace wayar ne? Ko kuma akwai abinda kake boyewa ne wanda baka son in gani? I cannot just seat idle and watch you turn into this, sai dai in abinda yafi karfina ne".
Yayi shiru tare da saka hannu biyu ya dafe kansa, shi dai yasan babu wani abin ashsha da yake cikin wayarsa wanda ba zai iya budewa a gaban ta ba, abu daya ne baya so ta gani wanda kuma ya san shine abinda take after, chats dinsa da Safiyya.

Tun shekaran jiya Safiyya tayi blocking din calls dinsa, amma kuma ta manta bata yi blocking dinsa a WhatsApp ba, wanda dama shine kadai social media app din da yake yi anan ne kuma suka fi yin hira. Tun shekaran jiyan kuma yake tura mata sakonni, amma ya fahimci kamar data dinta a kashe take gaba daya dan sakonnin basa zuwa gare ta, amma hakan bai hana shi rubuta wa ba, hakan bai hana shi gaya mata duk abinda yake zuciyarsa ba, all the things that he wanted to say to her, hoping that zata bude ta karanta ko da ba yanzu ba ne ba. Ya tabbatar kuma idan Mama ta karanta sakonnin zata fahimci gaskiya abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya, zata fahimci cewa Safiyya matar aure ce kuma har tana dauke da ciki.

Safiyyahजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें