The Choices

814 70 18
                                    

For sponsorship,

contact 0704 203 0419 on whatsap

or

send a dm to my Instagram page

https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ==

Save my business number

0704 203 0419

and say hi on whatsap dan inyi saving naku.

Please, dan Allah, abeg, ban da kira

*Her🧕🏻*

Har dare yayi na kwanta bacci babu wanda ya kara shigowa gurina babu kuma wanda ya neme ni sai Mommy da ta shigo ta matsa min  naci abinci sannan nasha prenatal vitamins dina. Tun da na tashi da assuba kuwa nayi wankana na shirya na saka jilbab ɗin da nake fatan zai rage nuna wa mutane cikin da yake jikina. Dama kayana a hade suke ban fito da su daga jaka ba, duk abinda na fito da shi kuma nayi deciding cewa ba zan tafi dashi ba dan bani da karfi na jiki dana zuciya da zan iya yin wani abu akai.

Na koma na kwanta a kan gado na nannade jikina da jilbab ɗin, na rufe idona da fatan bacci zai dauke ni ko na samu na ɗan rage ciwon da kaina yake yi min, amma sai dai a maimakon bacci, memories ne suka yi ta overlapping a cikin kaina, memories of yarintata, memories of relationships dina da family dina a da da kuma a yanzu, memories din Gidado and all the hopes we had for a future together, and the memories of daren da ya lalata komai a rayuwa ta, daren last birthday din Gidado.

Na tashi zaune tare da dafe kaina da hannayena ina jin yana barazanar tarwatsewa. Sai kuma na daga kaina sama ina kallon hoton da yake facing ɗin gadona, hoton mahaifiyata a kwance akan gadon asibiti rike da yar jaririya a hannunta, fuskarta cike da tsantsar farin ciki. Nayi ajjiyar zuciya, ina ma dai rayuwa tana da control button, ina ma dai zan iya rewinding komai na koma yar jaririya na cigaba da jin dumin mahaifiyata, inama.......

Sai nace a fili kamar mai magana da ta cikin hoton. "you set me up to be devoured by the blood thirsty vultures, yanzu gashi sun kassara rayuwata" nayi tsaki na juyawa hoton baya, sai kuma na sake juyawa nace "I miss you though".

Knocking din da naji a bakin kofa ya saka na dawo da dubana kan kofar sannan na kalli agogo, 7:35. "Yes?" Nace ina gyara hijab dina tare da sake haɗe fuska. Sai dai kuma ana bude kofar yanayin fuska ta ya juya zuwa murmushi. At last, someone I can talk to, someone who truly loves me.

Suka shigo a tare suma fuskokin su dauke da murmushi, na bude musu hannayena amma maimakon su fada jikina kamar kullum sai suka zauna a sides dina sannan suka rungume ni a tare. Nayi ajjiyar zuciya ina kara rungumar su jikina, ina jin yadda suka kara girma duk su biyun, a tsaho yanzu duk sun kere ni.

"Yan biyun yaya Fiyya, I am glad you made it. Ina ta jin babu dadi na dauka ba zan ganku ba har mu tafi".

Hassan ya dago kansa daga kafada ta yace "kinga gudun da muka yi a mota kuwa? Mommy tace mu hakura mu zauna tunda jiya ma evening paper mukayi amma muka dage sai da muka zo dan mu ganki kafin ki tafi"

Hussain yace "Mommy tace zaki jima baki dawo kasar nan ba, haka ne? Amma zamu iya zuwa mu kai miki ziyara in mun gama waec ko?".

Na gyada kai nace "duk sanda kuke son ganin mu kuyi min magana ko kuyi wa Daddy magana, za'a siya muku ticket ku tafi. And anything you need, ko menene, ku kira ni ku gaya min".

Suka gyada kai a tare, Hassan yace "but this is not fair, Daddy is not being fair to you. Me yasa zai miki aure yanzu? Mommy tace aure zai yi miki da yaya Mustapha. Yaya Mustapha fa for God's sake. It shouldn't be. Kamata yayi a barki kiyi healing, ki kuma samu wanda kike so ku fahimci juna sannan sai kiyi aure"  na kalle shi ina murmushi nace "all that sounds so good. Amma kuma ba haka Daddy ya zaba ba, and I am sure Daddy ba zai zaba min abinda zai cutar da ni ba, da abinda ka fada ɗin shine zai fi min dai dai I am sure Daddy shi zai zaba min, you should be kinder to him".

SafiyyahWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu