HAIRAN 🥰♥️😭💔
No. 5
Ayshatuuu
*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 👇🏼👇🏼👇🏼
https://wa.link/fnx1ev
*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.
https://vm.tiktok.com/ZMrhL6Ljy/
Contact her on WhatsApp👇🏼👇🏼👇🏼
https://wa.link/nuv5fy"Duk ranar da kuka gan shi yaje makarantar Ina so ku kamo min shi na gani"
Dattijon malamin ya fadawa daliban shi bayan sun zo sun fada Masa daya daga cikin su Yana zuwa makarantar Boko, a wancan lokacin dattijon malamin Yana ganin hakan matsayin kafirci da Kuma yahudanci. Dan haka ya Basu damar duk lokacin da suka ga yaron ya dawo ko zai tafi makarantar to su kamo shi su kawo Masa, shi daya se mahillicin shi yasan me zai yiwa yaron. A cikin aji da ko kadan basu da yawa, gaba daya basufi su goma ba cikin ajin, saboda yadda iyaye suka ki bada hadin Kai wajen ganin yaron su sun shiga makarantar ta zamani wato Boko. Baturiyar malamar Dake tsaye Gabon black board tana koya musu darasi ta dubi daya daga cikin students din ta Dake gyangyadi, cikin harshen turanci tace
"Ibrahim bacci kake yau ma?"
Yayi firgigit ya tashi Yana mutsuka idanun shi, ba tare da ta sake ce Masa komai ba ta cigaba da darasin ta, bayan ta Kamalla tace masa ya biyo ta zuwa office din su, haka yabi bayan ta suka Isa office din, kusan dukkan su turawa ne se kabilu uku se wani bahaushe a zaune, ta karasa wajen bahaushen ta fara fada Masa cikin turanci
"Wannan yaron, kamar Yana da damuwa, Ina so ka taimaka kayi magana da shi, idan ma zuwa ne mu samu iyayen shi duk se muyi!"
Malam Idi ya dubi Ibrahim yace
" Ibrahim ya akai kake bacci a aji?"
Ibrahim yayi shiru ba tare da yasan abin da zai fada ba, se ya danyi masa fada daga karshe yace ya tafi aji. Ko da aka tashi banda sauri Babu abin da yake yi saboda lokacin karatu ya kusa Kuma yasan idan yayi fashi ko latti Malam zai saka garada su Dake shi, Yana ta sauri Dan ya samu ya Isa akan lokaci kawai se ji yayi an cafke shi, kafin yayi yunkurin guduwa Yara sa'oin shi su kusan biyar sukai Masa kofar rago suka kama shi, Yana ta bubbuge amma Ina sarkin yawa yafi sarkin karfi, su kuwa murna suke kamar Wanda suka kamo kifin da yafi kowanne girma a gasar Arugungu fishing festival! Haka suka Isa makarantar, duk yawanci almajiran sun taru wasu ma har suna kokarin fara rubutu, aka dire shi a gaban malam, ko kafin ma malam yace Masa komai se da ya saka aka lallasa Masa jikin sa kafin yayi Masa gargadi akan idan ya sake zuwa wannan makarantar ta kafirai zai ga abin da zaiyi masa. Kwana biyu Ibrahim ya dauke kada daga zuwa makaranta, da yaga kurar ta lafa se ya cigaba da zuwa abun shi a boye kamar yadda ya saba, seda aka kusan shafe watanni kafin yaran suka Kara ganin shi a assembly sun zo wucewar, Suka Kara komawa suka sanar da malam, a wannan karon kuwa Malam kawai se ya kori Ibrahim daga makarantar shi.

YOU ARE READING
HAIRAN🔥💥♥️
General FictionTunda Anty ta fara magana, Prof yake kallon ta, idan ka kalle shi ba zaka taba fahimtar a yanayin da yake ciki ba, ba zaka fahimci emotions din shi ba, Amma yadda yake kallon Anty, da yadda ya bata dukkan hankalin shi, Abu ne da zai tabbatar maka ce...