62

331 7 4
                                        


Part 62

*My heartfelt condolences to the entire citizens of Borno state, Maiduguri precisely. Ubangiji Allah ya kiyaye gaba, ya baku hakuri da juriyar cin wannan jarabawar. We feel your pain and we're praying for your safety and well-being*


Kusan kwana nayi ina tunanin maganganun da Anty ta fada min, tabbas ko shakka Babu abin da ta fada gaskiya ne Amma na rasa yadda zanyi na ji sonta cikin zuciya ta, na dai hakura Kuma na yafe mata but Anty will forever be my Mamaa. Ana kokarin shiga sallah Anty ta tashe ni Dan nayi sallar, na tashi na wuce toilet nayi alwala sannan na fito nayi sallah kafin na gama Azhar bacci ya dauke ni. Bani na tashi ba se wajen takwas da rabi, jiki na duk ciwo saboda a kasa na kwanta. Kafin na fito nayi wanka na shirya cikin lace coffee dinkin doguwar Riga, ina fitowa parlor Doctor na shigowa, ya kalle ni Yana sakar min murmushin, goodness I missed him na ayyana a Raina, na gaishe shi ya karaso ya zauna Yana tambaya ta yadda na tashi da Kuma abin da nake son ci, nace masa kaza me yaji nake so, ya gyada kan shi tare da tabbatar min zai kawo min yanzun har ya mike zai fita yace

"Oops bamu gaisa da Anty ba"

Na mike a hankali na shiga kitchen, Wanda kamshi tafasowar spaghetti yasa na fito da gudu saboda zuciya ta da ta fara hautsinawa zanyi amai, cikin sauri ya ruko ni Yana fadin

"Haeee what's up?"

Na kwace jiki na daga nashi ina toshe hannci na, Hakan yasa ya fahimci ko kamshin turaren shi ne bana so, Anty ta fito Jin kakarin amai na a toilet din parlor, saboda shiga ta kitchen din tana cikin store dakko Abu, da damuwa ta karaso kofar toilet din, lokacin na gama Yana wanke min fuska, ta girgiza kai kawai ta koma parlon tana jiran mu, Muna fitowa suka gaisa da Doctor da yace zaije ya kawo min kaza, ta dubeni yadda nayi lakwas akan sofa tace

"Shi take so?"

Da sauri na gyada Kai nace

"Da yaji da yawa!"

Tayi murmushi tace

"Bara nayi mata, idan ta huta kuje ku gaida Hajiya, anjima da Rana se muje wajen Ummiey ko?"

Da sauri ya kalle ni Yana murmushi yace

"Anty ta yadda"

Ta gyada masa Kai tana masa alamar ya bar maganar Dan har na cona Baki, da dariya ya zauna a kasan carpet Yana fadin

"I'm proud of you Babes, is good to give her a chance"

Na Kara Bata fuska nace

"Ni fa dan Anty zanje na gaishe ta Amma na yafe mata"

Yayi murmushi yace

"Munyi waya da Anty Rabi'ah jiya nace mata kina da ciki"

Idanu na na bude sosae nace

"Me yasa?"

Yace

"Saboda kinsan se munje an bamu shawarar how to take precautions kada baby dinmu ya zama HIV positive ko?"

Haka ne fa, ai ni wallahi na manta ma, saboda yadda hankali na yake a kwance, na manta akwai Wani kalubalen da zamu fuskanta a gaban mu. Na saki ajiyar zuciya idanu na suna cikowa da kwalla nace

"Allah yasa babyn mu yazo free"

Ya shfa Kai na yace

"As long as kina Shan magani, we will have HIV free kids, it's up to you love"

Na gyada Kai saboda nasan Hakan, Amma dai I need reassurance. Munje wajen Ummaah mun gaishe ta, bayan ta yimin tayin Kunu nace mata ai bazan Sha ba, shi da kan shi ya fada mata ai anjima zamu wuce wajen Ummiey tayi murna sosae ta Kara min nasiha tace

HAIRAN🔥💥♥️Where stories live. Discover now