TUSHIY...

1K 60 12
                                    

🌳🌳🌳

*TUSHIYA...*
               🌳🌳🌳

Hassanah Zakariyya Maidaru
      *Sanaah Shahada*

✏📖
       *FIKHRA WRITERS ASSOCIATION*

     PAGE 1...

"Ai kuwa kamar a dokar makarantun da basu wuce sakandare ba na san akwai hana zuwa da waya ko?"

  Ko dagowa bata yi ta kalleshi ba in banda sake muskutawa ma da tayi tana ci gaba da danna wayarta ka rantse bata ji korafin nashi ba.
"To ko dai makarantarku dabance?"Ya sake tambayarta da alamu a cikin muryarshi ya fara kaiwa makura a fusata.
Ta ajiye wayar a kan cinyarta ta harari keyarsa sai aka yi sa a suka hada idanu ta madubin adaidaita sahun,ko dar bata ji ta dora da rashin mutuncin da ta ke niyyar sauke masa
"To an fada maka shi sanin naka wahayi ne da ba za a iya gogewa ba? To wai ma ina ruwanka da ni ne da zaka takura min da tambayoyi haka?" ta ja tsaki.

Ya juyo ya kalleta a fusace yace "Eh lallai baki da kunya! Daga tambaya zaki min dibar albarka? To ki kiyaye ni bana daukar raini!"

Ta ja tsaki tana kara wayar a kunnenta tace "Jirani in gaba waya sai ka nuna min ko kai waye a rashin mutunci"
Tsawon sakanni ta fara magana a wayar "Sweet khady mai yasa baki shigo school ba yau?...Ayya sorry sannu fa bari in wuto erea din naku in duba ki...ok sai na shigo din...Bye" Ta sauke wayar,ta kalli mai adaidatan tace"Allah ya taimake ka ba gida zan yi ba da sai na sa yan kayinmu sun koya maka hankali wallahi! Da ka gane tsakanin ni da kai waye baya daukan raini.Sauke ni a nan na samu wani abin hawan da bai da sa ido ko?"

  Ya gangara gefen titi ya tsaida mashin din ba tare da yace mata komai ba ya mika hannu "Bani kudi na to" yace da ita.

Tana gogarin goya jakarta a gefen kafada irin yadda maza suke yi idan suna goye da jaka yar goyo,ta sunkuya tana karkade dan kajeran siket din makarantarta wanda safa ta kawowa guiwa ya samu tagomashin rufe mata jiki.
  "Ko ba zaki biyani ba?" Ya tambayeta

Ta dago ta kalleshi "Aikin me ka min da zan biyaka har kana min ihu aka? munyi da kai idan ka kaini gida zan baka 150 kuma baka kaini ba sai in baka kudi saboda saratu ce ta haife ni? To wai ma duka tafiyar minti nawa muka yi? Kawai ka ware malam!"

Ya kashe mashin din ya fito ya tsaya a gabanta "Wallahi sai kin bani kudina kinji na rantse! Idan ba haka ba in miki wulakancin da baki taba tunani ba,ke karamar mara kunya ce wallahi!"

Ta sa hannu a aljihun jakarta daga gefe ta dauko naira talatin ta mika masa "Ungo." tace masa.

Yabi kudin shakeke da kallo kana yace "Baki isa na karbi wannan ba yasin,sai kin cika min kudina zan karba ko na keta miki mutunci"

Ta maida kudin jaka ta kalleshi tsaf tace"Bafa keta mutuncinka nake tsoro ba yasa na baka,bana son bata lokaci ne,amma ba dan haka ba wallahi ban ki naci kwalarka mu doku ba dan ka tabbatar nima ba mutunci ne dani ba balle ka samu na yagawar" Ta fara tafiya.

Ya janyo karamin hijabin makarantar tata sai gashi a hannunsa dama iyakarsa kirji.

Ta juyo a fusace ta daga hannu zata mareshi ta ji an rike mata hannu,ta waiga wani mutum wanda bata san lokacin da ya wanzu a wajen ba ma da har zai hanata daukar matakin da tayi niyya.

Ya mata kwarjini a idanu da ta maida marin kanshi,ta sauke hannunta kasa lakwas!

"Haba dan uwa ina kai ina rigima da mace?macen ma,karama da bata wuce kanwar kanwarka ba?" Mutumin ya fada.

Mai adaidaitan yayai kwafa kana yace"Ban so ka hanata dora hannu a fuskata ba wallahi da yau ta raina kanta,bayan na lallasa ta ta kwana a bayan kanta"

Ta zaburo da jin maganarsa tana cewa "Kai ne bakon zuwa police station ni ai gida ne ka tambayi kowa a unguwarmu kaji gidanmu basa tsoron zuwa kotu ma ba police station ba"

"Kanwata dan Allah kiyi hakuri kiyi shiru kinji?"

Ba karamin kashe mata jiki yayi ba da ya kirata kanwarsa hakan yasa dole tayi shiru hade da sunkuyar da kanta saboda wata kunyarsa da taji ta rufeta yanzu.

Bayan mai adaidaitan ya masa bayani ya dauko naira dubu ya mika masa"Karbi wannan ka tafi,dan Allah kayi hakuri ba a biyewa yara musamman ma mace kaji!"

"Dauki kudinka ka kawo canji kuma" Tace dashi tana mai gwalo.

Ya harereta "Kizo ki sa karfi ki kwata,mara kunyar kawai!"

Jama'ar da suka cika wajen yan kallo suka fara silalewa daya bayan daya ganin abin kallon ya kare.

*** *** ***
"Ya sunanki ne 'kanwata?" Saurayin daya raba musu fada ya tambayeta bayan sun shiga motarshi zai kaita gidansu Khady.

  Ta kalli gefe "Suna na Hafsa,amma ana kirana da Bushira saboda sunan mahaifiyar Abbana aka sa min" ta amsa masa.

Dafe da sikiyari hannu biyu ba tare da ya kalleta ba yace"Hafsat ko Bushira wanne zan kiraki da shi?"

"Bushira shi ne sunan da na fi so"

"Is ok.Ni kuma sunana Ahmad,ana kirana da BOBY,fatan zan samu alfarma in zama yayanki."

ta gyada kai.

  2 loading...

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now