Shafi na 27-28

158 14 5
                                    

🌳🌳🌳
   *TUSHIYA...(Life story)*
      🌳🌳🌳

  By *Sanaah Zakariyya  Shahada*

✏📖 *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

  Shafi na *27-28*

  🌳
  A cikin gida ma tunanin abin take yi 'me wannan mutunin yake nufi da ni? Nima zai raina min hankali ne na yarda da shi? ' ta ce a zuciyarta.

   "Kai ba zai iyu ba wallahi!" Ta fad'a fili.

   Tashi ta yi tana gewaye daki. Wata zuciya ce ta bata shawara kawai ta yi caji ta rabu da wannan tunanin.

  Bata tsaya wani tunanin ba ta dauki kudi ta fita.

  Tana cikin chemist din ta ji wayarta tana ring ta zarota daga aljihun wandonta. Bobby ne.

   Ta d'aga " 'Kanwata 'yan gidanmu sun ce nan da kwana uku za su zo gidanku"

  Ihun farin ciki ta saka sannan ta ce"Kai amma na ji dadi yaayana! Allah ya nuna min wannan rana."

  Suka dan tattauna sannan ta kashe wayar ta maida ita aljihu ta maida earpiese dinta kunne.

   Ta karbi abinda ta zo siye ta tafi gida a yanayin da kowa ya ganta sai ya gane tana cikin farin ciki.

  Tana shiga gida ta yi d'akin Mama tana 'kwala mata kira.

"Mama! Mama! Fito ki ji wani abin farin ciki" ta shiga dakin ta ga bata ciki ta fito tsakar gida tana ci gaba da kiranta.

  Daga bandaki ta ga fitowarta . Ta ajiye butar hannunta "Lafiya ke kuma kike min wannan kira kamar wadda ta warke daga makanta?

  Da gudu Bushira ta rungumeta ta rada mata a kunne. Da sauri mama ta dagota tana dariya "Ayyiriri! Allah ya yi aure da maras kwabo, makiya sai ku mutu" ta saketa tana juyi a tsakar gida Bushira tana tayata kamar irin yarabawan nan.

  A wannan daren ta yi caji sosai dan da ta kwanta barci ko motsi bata yi ba sai da gari ya waye dama bata fiya yin sallar asubah ba.

  *** *** ***
Bushira da mama sun shiga damuwa ganin har kwana hudu ba iyayen Bobby babu labarinsu ga Alhaji sai shirin aure yake har an bugo kati an fante gidan 'yan uwa na nesa sun fara zuwa.

  Ita kam har ta gaji da neman layinsa baya dagawa ta tura masa text ba reply gaba daya ta rasa ma yadda za ta yi.

  Ta kira su Khady ma bata samu wata gamsasshiyar kulawa ba dan Khady ma kashe mata wayarma ta yi, ita sai ta ji ma kamar tsaki ta yi kafin ta kashe din.

  Tana zaune gefen katifarta tana aiki d'aya (kiran Boby da tura masa sako) a karo na ba adadi ta ji ya daga wayar.

  Ta dafe 'kirjinta kafin ya ce komai ta fashe masa da kuka "Yaayana me na maka? Mai yasa ba ka dauki wayata ba?"

  Cikin sanyin murya ya ce "Ki yi hakuri 'kanwata kinji"

  Ta toshe bakinta da hannu ta samu ta hana sabon kukan fitowa "Ka fada min mai yasa?"

  "Babanmu ne ya ce ba zan aure ki ba 'kanwata ki yi hakuri"

  Bata san lokacin da ta mike tsaye ba sai ganinta ta yi a tsaye. "Ka ce me!? To saboda me?" Me na masa?"

  "Magana ce mai tsayi ki bari idan muka hadu zan miki bayani"

"Kawai ka fada min idan kana so hankali na ya kwanta. Me na masa?"

"Ba shi kika yiwa ba,  'kaninsa wanda shi yake wakiltar komai namu shi kika yiwa. Bayan na je na masa bayanin ki da gidanku sai yace zai yi bincike, to bayan ya binciko yace wai kin taba masa rashin kunya wata rana har kika nemi ki zage shi a wani kantin saida kayan shafa a gefen layinku"

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now