TUSHIYA.,

221 20 1
                                    

🌳🌳🌳

        *TUSHIYA... ( life story)*
            🌳🌳🌳

✏📖
     *FIKHRAH WRITERS ASSOCIATION*

BY
Hasana Zakariyya Maidaru *(Sanah Shahada)*

Page 5-6
Mama ta dalla mata harara kana ta yi murmushi ta ce "Waye kuma Boby da ba zaki iya daga wayarsa a gabana ba?"

  "Ai da na san ba shi  ba ne ba zan daga ba mama!" Ta ce tana gyara bacin ran da ta yabawa fuskarta kada ya kufce.

Mama ta yi dariya ta koma kan gujerar da ta taso tana cewa "Ban gane ba, shi murmushin da kika yi da farko menene sanadinsa?"

  Bushira ta yi 'karamin tsaki cikin salon bacin ranta ta ce"To ni da na dauka Ya Ahmad  ne? Ashe wani ne ma"

  "To na ji shi din waye da har kika yi saving number ɗinsa amma ki ke kashe masa waya?"

  "Wani dan ajinmu ne yake damu na" ta amsa mata.

  Murmushi mama ta yi ta ce"Ko dai Siriki zan yi ne?"

  Bata ce komai ba ta tashi tsaye sannan ta ce "Ni dai na tafi daki barci nake ji"

  Ta shige dakin tana daddanna waya. Tana shiga kan katifa ta fada ta kwanta rigingine ta kara wayar a kunnenta da alama kira ta yi.

Ta sa daya hannunta ta janyo filo ta rungume "Hello Yayana" ta ce alamun an daga kiran nata.

  Daga can bangaren aka amsa da cewa "Kanwata na yi laifi ko?"

Ta zaro idanu "Wanne irin laifi kuma?" Ta tambaye shi.

  "Na ga an kashe min waya ne shi ne na ce ko laifi na yi in bada hakuri"

  Ta yi dariya "Ba ka laifi a wajena, muna magana da Mama ne"

  Daga can falo kuwa Mama dariya ta yi tace "Yar banza na san kiranshi zata yi shi ne wai barci zata yi"
   Ko a jikinta ta juya tana murmushi.

  "Assalamu Alaikum!" Aka yi sallama a bakin falon.

  Da sauri Mama ta kalli kofar tana cewa "Wa nake gani kamar Safiyya? Oh yar nan dama kina nan?"

Wacce aka kira da Safiyya ta yi murmushi ta zauna a kasa tana cewa "Ina nan wallahi Mama karatu ne ya rike mu ina son shigowa, amma na san halin mutumiyar ko na zo bata nan ko kuma mu rabu dotse a hannun riga"

  Mama ta yi dariya "Ai ku kam sai dai Allah, yanzu ma a kasan za ki zauna ko? Ni har na gaji da ce miki kina zama akan kujera in kin shigo"

Safiyya ta sunkuyar da kai "Nan ma ya yi Mama, tana nan kuwa?" Ta tambayeta.

  Mama ta harari kofar dakin Bushira ta ce "Hmm Bishira ko yar iska, tana ciki yanzu ta tashi ta shiga hira da saurayi"

  Safiyya ta bata rai kamar zata yi kuka ta ce"Ki yi hakuri Mama ki daina fada mata wadannn kalmomi kina nema mata shiriya saboda bakinki mai zafi ke a kanta kuma kin ga..."

   Cikin sauri Mama ta daga mata hannu tare da cewa "Dakata haka! Ce miki na yi baki nake mata ko kuma ance miki ita din ba a shirye take ba? Ki kiyaye ni da wannan kinibibin naki!"

   Safiyya ta sake sunkuyar da kanta kasa ta ce"Ki yi hakuri Mama!" ta tashi ta nufi dakin Bushira.

** **
   Safiyya ita ma jika ce a Gidan Gado 'yar gidan Gwaggo Hadiza ce wadda ta mutu ta barta.

   Mama tana matukar son Safiyya dan ta so ma a bata ta shayar da ita aka hanata.

   Tun da Safiyya ta taso jininta ya hadu da na Bushira da ita kadai take wasa koda za su yi fada basa dadewa suke shiryawa.

   Halinsu ya banbanta matuka ita Safiyya yarinya ce mai son addini komai nata cikin sanyi take yin shi, bata dauki duniya da zafi ba.

  Sabanin Bushira da bata cika zuwa islamiyya ba, koda ma ta je bata maida kai a kan karatun da ake musu gata da girman kai da isa.

  Safiyya tana da farin jini a cikin jama'a addininta yasa take burge mutane da dama.

** **

Safiyya na shiga dakin Bishira ta zauna a bakin katifar, ita kuwa bata ma san da zuwanta ba tana faman waya, sai da Safiyya ta d'ala mata duka a cinya ta yi wata 'kara ta wurgar da wayar ta tarwate a kan tayil.

   Ta bi wayar da kallo sannan ta janyo ragamar kallonta inda ta ji dukan, wata ashar ta saki tana cewa "Safiyya wannan wanne irin wulakanci ne za ki dake ni haka? Tana sosa wajen.

   Safiyya ta yi tsaki ta ce "Ke de wallahi Bushira sam ba kya ji, yanzu irin wannan shigar ta kamace ki a matsayinki na budurwa?"

  Bushira ta bi jikin nata da kallo kamar tana son shaida kayan da ta saka ko kuma an sauya mata wani bata sani ba?
   Ta tashi tana had'a wayarta "Arammi kafin ki gayyato min nasiharki bai kamata kwakwalwarki ta manta a gidan Ubana nake da zama ba, za ki iya tuno duka gidannan muharramai na ne? Na san kwololuwar wa'azinki baya wuce haka"
Ta dawo ta zauna a gefenta.

    Safiyya ta dafa kafad'arta cikin taushin murya ta ce "Kwakwalwa ta ba zata yi makuwar manta haka ba, amma ki sani addini bai yarda da shiga mai bayyana tsiraici ba koda kuwa ga muharraminka ne, matukar ba ga Mijinka ba ne. Bushira ki sauya dan Allah ki watsar da tsintacciyar d'abi'ar nan, ke Musulma ce!"

  "To na ji! Yanzu dai mai ya kawo ki? Dan kin ce ba zaki sake zuwa wajena ba idan ba da wani muhimmin abu ba, menene?"

  Safiyya  ta girgiza kai "Kwarai na ce haka, sai dai jinin 'yan uwantaka ba zai barni ba, abubuwa biyu ne suka shigo da ni a yau. Na farko ina so in baki shawara ki koma Islamiyya kin ga Azumi yana tahowa, na biyu kuma na zo ki bani shawara kan wata matsala da ta sha min kai take neman tafiya da ruhi na. Bushira damuwa tana neman ta cinye nutsuwata" ta fashe da kuka.

   Jikin Bushira yayi sanyi matuka, bata taba ganin Safiyya ta yiwa damuwa kuka ba, tana da juriya da danne abubuwa 'Lallai wannan babban al'amari ne' ta ce a zuciyarta.
A fili kuma sai ta ce "Mu ajiye magana ta farko mu shawo kan matsalarki tukunna, ya girman wannan matsala take da ta hankado hawaye daga idanunki 'yar uwata?"

   "Matsalar soyayya ce Bushira, ashe abinda ke ajiye kirjina nake zaton dutse ne, ashe tsoka ce da gudan jini, ashe littafan larabawan da nake karantawa nake ganin sun yi ne domin nishadi yana zama gaske? Ashe wannan matsala tana shake wuyan kowa ma wai har malamai da masu sarauta? Ashe..." sauran maganar ta ma'kale a cikinta saboda kukan da ya ci karfinta.

  Bushira ta kama hannunta ta ce"Ba na dauko mana abinci sai ki warware min abinda ke akwai"

  Ta tashi ta fita.

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now