TUSHIYA...

291 27 4
                                    

🌳🌳🌳

  *TUSHIYA...*

            🌳🌳🌳
Hassanah Zakariyya Maidaru
        *Sanaah Shahada*

✏📖
      *FIKHRAH WRITERS ASSOCIATION*

      Page 2...
"Kanwata ga wata alfarmar kuma!" Boby yace da ita yana kallonta da gefen ido.

Ta jinjina kai tsawon mintuna biyu ta ce"Fadi yayana"

Yayai murmushi "Number dinki nake so dan karfafa zumunci"

Ta sa hannu ta dauki wayarsa da take caji a ta kalle shi ta ce"Zan sa maka,amma bana jure yawan kira ko surutu maras dalili"

Bai ce komai ba har ta gama ta ajiye wayar a inda ta d'auke ta.

Har suka je kofar gidansu Khady bai tanka mata ba haka itama bata sake cewa komai ba.

Ta kama murfin motar zata bude ta ya dafe jakar makarantarta da take kokarin dagawa da daya hannun. Ta juyo ta kalle shi ta yi murmushi "Ba mantawa nayi ba yayana,zan maka godiya"

"Ba muradina kenan ba!" Yace mata.

  Ta zaro ido kadan alamun mamaki,tayi murmushi hade da girgiza kai kadan na al'ajabi.

  "Ka adana muradanka tukun ni na gabatar da nawa. Na gode sosai" Ta had'a hannayenta biyu.

  Shima ya hade hannayensa biyu yace"Kada ki manta da yayanki"

  Ta jinjina kai alamar tabbatarwa ta yunkura zata fita ya sake danne jakar tare da yunkurin dauko wani abu daga aljihunsa.

Kudade ne masu yawa yasa mata a aljihun gefe na jakar "Kada kice ba zaki karba ba,haka kuma kada kiyi min godiya"

  Ta lumshe ido ta bude a lokaci daya,ba tare da tace komai ba ta bude motar ta fita.

  ***
Sassanyan kamshin turare ne ya fara dukan hancinta kafin sanyin A.C hade da zafin da ta dauko a harabar gida suka cajuda suka bata wani yanayi kamar na shigar zazzabi.

   Babban falon gidansu Khady kenan mai cike da kayan alatu daban-daban.Khady a luntsume cikin kujera da remote a hannunta na dama hannun hagun kuma lemo ne take sir'ba.

  Da shewar murna suka tari juna sannan suka zauna.

  Khady ta bata fuska "Tun dazu kika ce min gaki nan a kofar gida,amma sai yanzu kika shigo ko?"

  Bushira taja numfashi "Hmmm ke dai bari sis,wallahi gamo nayi da wata haja mai matukar daraja"
  Ta bata labarin yadda aka yi.

Khady ta bata hannu suka tafa tace"Da kyau sis,Allah yasa wannan haja ta kara daraja."

   Bushira ta kurbi lemon da ta zuba da kanta ta ajiye kofin tace "To amin dai,amma gaskiya ni ya gama yi min,na mace gaba daya,kinga hotonsa da na tura a wayarsa"

  Ta nuna mata hoton,ya dauka ne a bakin ruwa da wata farar  T-sheet mai adon blue da wanso 3quater shima blue,fuskarsa dauke da murmushi,idanunsa sun kara lumshewa kamar mai jin barci.

  Khady ta 'kura masa idanu har hasken wayar ya dauke bata kula Bushira ta mata magana bata ji ba sai da ta ta'ba ta tayi firgigit!

"Kin ga na shiga wani tunani kuma,ungo wayarki" Ta mika mata wayar.

  "Menene yake damunki kike zurfafa tunani haka? Ko matsalar Mommy ce har yanzu?" Bushira ta tambayeta

Tayi 'karamin tsaki "Ai kin san kullum cikin matsalarta nake,yau ma sun samu matsala da Daddy ne wai ta tafi garinsu,bari dai na sa Hauwa ta samo miki wani abu,na san daga makaranta kike akwai yunwa" Ta mi'ke ta fita ta wata kofa da take kallonsu wadda ita zata sada mutum da kitchen.

Bayan ta bada umarnin a kawowa Bushira wani abu ta dawo,ta dan kalli Bushira tace"Zata kawo miki,ina zuwa"

Ta shiga kofar da take bayan fallon,nan kuma bangarenta ne,kai tsaye dakin barcinta ta dosa tana shiga ta jibgu akan gado tayi rigingine. Idan ta rufe idanunta shi kawai take gani,ta bude idanunta tana sauke ajiyar zuciya kamar yaron da aka daka ya sha kuka ya kwanta barci.

   Bata san me zata kira wannan zuwa na Bushira ba,kaddara ko tsautsayi?

  Tsawan awa guda ta gaji da sake-saken da har yanzu bata tufka iyar da zata tseratar da ita ba ko guda daya. Ta tashi ta koma falon,tana shiga Bushira ta fara mata masifa "Wannan wanne irin abu ne sister? Kin zo kin jibgeni kin tafi,kin san fa dubaki na zo yi"

  Ta dafa kafadarta tana murmushi tace"Yi hakuri sis cikina ne ya kada na shiga toilet gudawa fa nake yi,kuma kin santa da gajiyar da gabbai shi ne na kwanta barci ya nemi daukata,kiyi hakuri"

  "Ba komai,ya gudawar?

   "Da sauki sosai"

Haka dai suka yi hirar babu wani armashi har Bushira ta tashi zata tafi gida "To sis sai goben idan kin samu shiga schl,zan biya gidansu Asma'u in fada mata baki da lafiya,kin san ita ba waya ce da ita ba"

  Khady tayi yake tana fama da abinda yake nukurkusarta a zuciya.

  "Na gode sosai sis ki gaida yan gidan"

   "Baki ce in gaida sabon yayana ba" Tayi dariya ta wuce bata lura da halin da fuskar Khady ta shiga ba da gudu tayi cikin gidan saboda wata hargutsa da cikinta yayi kamar mai shirin fito da d'a.

     3 Loading...

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now