TUSHIYA... Page 29-30

416 24 10
                                    

🥦🥦🥦
TUSHIYA...
      By
Sanah Shahada.

FIKRAH WRITERS ASSOCIATION 📚

*Page 29-30.*

Nan fa 'yan biki suka yi kanta aka cicci'beta aka yi daki da ita tana numfarfashi.

  Ruwa mai sanyi wata 'kawar mama ta bata ta sha. Ta sau'ke ajiyar zuciya ta raba idanunta kan wadanda suka zagayeta 'karshe ta tsaida idanta akan Mama sai kawai ta fashe da kuka "Mama da gaske kunnuwa na sun jiyo auren Ramadan da Safiyya aka yi? dan Allah ki gaggauta 'karyata su"

  Mama ta matso kusa da ita ta kamata "Kin kulle min kai gaba daya fa, shin ba farin ciki ya kamata mu nuna ba? Ko mantawa kika yi?"

  Ta girgiza kai "Ban manta ba Mama amma wallahi yau na shiga ukun da ban taba shiga ba na cuci kaina Mama!" ta kara 'kan'kameta tana kuka.

   Matan da suke kansu sai rike haba suke cike da mamaki suka fara janyewa suna fita masu son jin kwakwaf kuwa suka tsaya wasu ma har da zama.

     ***
A 'kofar gida kuwa sai aka kama kallon-kallo jin abinda mai shelan ya fada.

Da sauri Hamza ya nufe shi yana ce masa Bushira ce ba Safiyya ba. Kawu Hassan ne ya zo ya janye shi yana jaddada masa haka ne ba kuskure ya fada ba da Safiyya aka daura.

"Yaushe aka sauya kawu?" Ya tambaye shi.

"Muma yau da safe Alhaji ya fad'a mana ya ce kada mu sanar muku idan an d'aura kwa ji"

  Hamza ya girgiza kai ya tafi wajen ango yana murmushin yake.

  "Wai me yake faruwa ne Hamza?"

  "Abinda ka ji dai shi ne yake faruwa"

  Ya yi tsaki ya d'an kalli gefenshi "Idan dai daidai na ji to kuwa ba zai iyu ba taya za a dinga juyani kamar mota? Wannan fa zuciyata ce"

  Umar ya kama hannunshi suka koma gefe.

"Nutsu Ramadan kada jama'a su fahimci abinda ke faruwa"

  Ya masa wani kallo na ina ruwa na ya ce "Su fahimta mana sai me? Ni dai damuwata nake duba. Kun san Allah idan aka ce lalle wannan auren aka daura da ni to kuwa a take zan saketa!"

   Rarrashinsa suka dinga yi suka ce ya bari a watse sai su ji ya abin yake.

   ***
Da gudu Safiyya ta yi d'akin Yaabi jin abinda ta jiyo.

  Ta sameta da mutane ta fad'a jikinta tana kuka "Yaabi dama ana mafarki da rana kuma a tsaye? Wai fa da ni aka d'aura auren kin ta'ba jin inda aka yi haka?"

Yaabi ta dafa kanta "Kwantar da hankalinki Safiya, Allah ya yi dake za a yi haka al'amarin Allah yaje, je ki fara shiri anjima za a kai ki"

Ta d'ago ta kalleta ba tare da tace komai ba ta tashi ta shige uwar d'aki.

   Sabon kuka ta girka da ta shiga d'akin gani take mafarki take zuwa anjima kadan zata tashi.

   Gaba d'aya fa gidan biki ya rikice mutane sai tambaya su ke me yake faruwa amare biyu sai kuka suke an rasa gane kan su.

  Ramadan d'aki ya shiga ya dafe kai abokanshi zai bashi baki suke duka yai musu shiru ya kasa cewa komai.

    Aunty Asiya Yaya a wajen Ango wadda ta zo tun daga 'kasar waje ta kamo amarya ta fara gyarata, amarya tana kuka ana gyarata abokan wasa sai tsokanarta suke.

Maman Bushira ta kasa gane kanta ta mata tambayar duniyar nan taki magana sai kuka take 'karshe ta yi fushi ta rabu da ita.

  Alh.Baba ya kirawo Ramadan a d'akin ba'kin shi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 14, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now