page 45

732 33 0
                                    

*silah*
*na khairat up*
*45*

Yadda haisam ya fada haka aka yi ta makarantarsu ya biya ya dauko shi suka dau hanyan kt ba wanda suka fadawa abunda ya faru
   Yana hanya sayyada ta kira shi a waya yana gani yaki dauka 

Bayan tafiyan hour biyu da wasu yan mintuna suka shiga unguwar su noufal
  Tana ko bakin kofar gida a zaune kan kujera fara gefenta da jakar kaya kamar yadda ya fada mata tayi.

Dariya ma ta basu ji wani iko na Allah

Da sauri ta matso kusa dasu ta ce gani yaya muje lafiya dai ko?

Uhm.lafiya mana shigo dayko kayan daukowa tayi tasa a baya ita ma ta zauna a bayan

Su biyu suna hirar su amma bata sa musu baki amma ranta fal haushi ya zama su raina mata hankali suna hirar su tana cikin damuwan ina mijin ta tsaki ta buga ta dauke kan ta daga ganin su ta juya kan ta gefe se kuma ta fashe musu da kuka
  Ke meye ?
Ba ku ne ba
Muka miki me?
Ya ina cikin damuwa zaku min shiru kuma ku kuna hirar ku a tsakanin ku.

Ta fada tana shashe'ka
  Yi hakuri to mun yi shiru iya rigima kin ji mun daina hirar
Ni ku fada min ina ya noufal din yake?
Ah ah ki dakata mana muje gida tukuna kar ki sa na yi watsi dake a nan titin
  Tayi kwafa tace ya JB kana jin sa ko amma kayi masa shiru
  Haisam ya isa dan Allah kayi shiru ka llalaba man ita kaji ko
Naji kin ci darajar JB wallahi
  Naji din ta fada tana mintsinan shi a gefen wuya me katon kai
  Hehe irin na mijin ki ?

Hararan shi tayi shi kuma ya dafa goshin sa yace u guys will never reform (ku dai baza ku fasa halin ku ba)

🍡🍡🍡🍡🍡🍡🍡🍡

Gidan hajiya suka sauka tana daki tana shirya kaya cikin drower ta jiyo muruyar haisam
  Ta leqa kai kuma ina kaje tun dazu nake neman ka muna ta kiran ka kaki dauka dan rainin ha....
  Hajiya chill wallahi kt muka je nida JB
  Kt yin me?
*Dear*muka dauko
Kuka dauko *Dear* kuma?
Eh
Lafiya?
Eh to amma zan fada miki se anjima
Kar ka ce min noufal ne ya sako ta?
Kash kinji ki hajiya ko daya matsala aka samu babba shi ne muke son muyi solving tukuna yanzu haka ma anjima kadan zamu tafi abuja
  Abuja?
Eh hajiya
Wai dan kaniyar ka ina wasa da kai ne me ya faru nace?

Sosa kan shi yayi ya koma ya kullo kofar ya zaunar da ita kan kujerar dakin yana facing din ta hannayen ta ya riko ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce hajiya ya noufal ne suka yi accident a hanyan su ta dawowa daga tafiya
  Innalillahi wa inna illahir raju'un
Ta dinga fada accident kuma ? Yana lafiya dai ko

Eh to shi ne zamu je mu gani amma yadda authorities suka fada biyu sun mutu hudun suna asibitin amma ban san waye ke asibiti ba waye kuma ya mutu so se mun je mun gani mun tabbatar shi yasa muka dawo da ita gida kar taji a wani gun kema kar ki fadawa kowa se mun tabbatar tukuna

Gumi da hawaye ke mata zarya kawai ta dinga nanata duk wata addua data zo mata a baki ta kasa kwakwaran motsi ni kuma tawa kaddarar kennan?

Mikewa yayi yace bara muje kar mu rasa flight ko mu samu goslow a hanya

Wai kai yadda ma kake fada kaman baka damu ba haisam ji ka so calm

Hajiya kennan kiyi hakuri ya zan yi na rasa ya hilal ai bazan so rasa ya noufal ba ina cikin damuwa da dimuwa amma ni din namiji ne bazan iya nuna muku gazawata ba dole na zama jarumi kan wannan harkar in na karaya ai akwai matsla ba me kwantar muku da hankali kennan

Rungume shi tayi tana kuka ya ce ya isa hajiya da yardar Allah ya noufal na nan a raye ki mana addua ki kuma saisaita kan ki kar ta gane wani abun.

Shi kennan haisam Allah ya kai ku lafiya
Amin hajiya
Share hawayen ki muje falo tare
To.

Da kyar ta hada nutsuwar ta tana fara'a ta fita falon tana lale lale da yar waje na sannun ku da zuwa ya hanya?

Alhamdulilahi hajiya kin dade a ciki ko wannan ne ya tsare ki da hira kin san halin shi yafi parrot

Dariya tayi shi kuma ya dungure mata kai banda lokacin ki hajiya bara muje mu dawo to a dawo lafiya

Ya JB ka tafi da ear piece ka sa a kunne saboda su o'o!

Bakin ta ya ja da karfi ya fyalle a guje

Ahhh zaka sani sena fada ma yaya in ya dawo u ll pay wallahi

Hajiya kallon ta kawai ta dinga yi tace ke kin ga yadda kika yi kuwa  kin je asibiti kuwa

Uhm uhm lafiya ta kalou hajiya ban jin komai
Hmm shi kennan shiga kiyi wanka kizo kici abinci

To hajiya da zan samu wainar fulawa ma da yaji 

To kar ki damu zan miki da kai na  ma jeki yi wankan.

SilaWhere stories live. Discover now