KASAITATTUN MATA
(Labarin mata ukku)©
BILKISU BILYAMINU11
Yayi mashi jagora har wajan Abdulwaheed, sun gaisa cikin mutunci da kamala saboda irin shigar da Saleem yayi dole za'a dauka akwai dattaku cikin duniyarshi.
"Ranka shi dadi ina da labarin yanda kake fidda kayanka daga fannune da dama, kuma da nazo sai na kara gasgata ka abinda mutane ke fada. gaskiya kana kukari wajan kamanta gaskiya babu ha'inci a lamuranka"
"Nagode" Abdul waheed yace mashi, yana cigaba da danna computer dake gabanshi.
"Akwai wata kanwata da take neman aiki irin na kampani haka, ban sani ba ku kana da bukatar daukar ma'aikata?"
"Meta ka ranta?"
"Ina tunanin Accounting ne"
"Zamu gana da ita idan ta cancanta sai mu bata gurbi a ma'aikatar"
"Zan fada mata kuwa insha Allahu, ammm kayan gine gine nake so, Amman Ku zan iya ganin samfur?"
Tashi Abdulwaheed yayi yace"Sosai ma kuwa, bari ka gani"
Wata na'ura dake jikin bango ya danna, sai kuwa abubuwan da suka shafi kayan ginin gida suka bayyana kuwanne da ingancinshi da kudinshi, yaga kayan masu inganci masu kyau da karko, daga bisani kuma ya tabbatar mashi da a wajanshi zai sayi kumai idan ya tashi.
Sun bar magana zai kawo kanwarshi gobe idan Allah ya kaimu, sallama sukayi da zummar sai ya ganshi goben insha Allahu.
Bayan ya fito ya Shiga mota, ya kira Aisha Beauty ya fada mata yanda sukayi da Abdulwaheed.
*_Kaduna 2:54pm_*
Nuwaira ta gama shirya yanda zata tahu da yarinyar nan gidanta saboda duk yanda tayi tunanin hakura da ita amman ta kasa, cikin shigar alfarma ta yima gidan saida abincin tsinke, duk wanda ya ganta yasan babbar mace ce kumai yaji idan ka dauke kudi da aji.
Daya daga cikin kujerun wajan ta samu ta zauna, yarane masu shekaru kamar na waccan yarinyar suketa kaiwa da kawowa amman bataga ku kiyar yarinyar ba, minti goma suka shige babu alamarta, hakuri dai ta karayi, wata daga cikinsu ta iso inda take tace"Aunty gashi ki duba abinda zan kawo maki"
Bin yarinyar tayi da kallo, daga bisani tace"Wata yarinya nake nema, bansani ba ku tana nan?"
"Wacece Aunty?"
"Bansan yazan bayyanata ki gane ba, amman dai fara ce sosai kuma tana da tsayi, kawai dai tana da kyau and kuma bata da hayaniya"
Bansan wa kike magana ba akwai ma'aikata masu kyau a nan wajan, sannan akwai farare sosai"
Idanuwanta ta dauka ta dinga zagaye dakin cin abincin, kamar daga sama yarinyar ta tahu kawo ma wani saurayi abincin,idanuwa ta tsora mata, tana mata kallan kurulla, hannu saurayin yakai ya taba nata hannun bayan ta aje mashi abincin saman tebur, kamar zata mutu haka taji, cikin hanzari ta tashi ta isa inda suke, yarinyar tana kiciniyar kwace hannunta amman yaki sakinta su yake ya sadata da jikinshi amman ta tuge, kamar a mafarki yaje saukar marin daya gigita mutanan dake wajan, saboda kuma wacece ta dauku dala babu gammu saboda wanda ta maran bata san kushi waye ba.
Idanuwa ya kankance yace"Lallai kin daukar ma kanki bala'i da kudinki, wallahil azeem saina maki hukunci da mafi girman abinda kika aikata a kaina.
Tsayuwa ta gyara sannan ta aje dubanta a fuskar yarinyar ta danyi rama kadan, dauke kanta tayi sannan tace"A duk kewayen nan wajan uban waye ubanka? Idan wata takama kake da iskanci, to albishirinka, kai yarone sai kazo"
Baki ya saki da yaga ta tsaya tana surfa mashi zallar rashin mutunci, zai fada mata ku wanene ubanshi sannan zai maida mata hankalinta saboda ya ga alamar kanta yana rawa, dariya yayi sannan yace"AMINU IBRAHIM MALUMFASHI shine ubana, kinsan kuwa kin dauku ma kanki mutuwa da kudinki"
Tsaki Nuwaira tayi tace"Allah ya tsine ma shasha irin ubanka"
Idanuwa ya zaro yana mamakin wacece itan, waya ta daga, ta saka cikin lasifika ta ajeye saman teburin gabanshi, daga can bangaran aka dauka.
"Ranki ya dade babbar yarinya kina lokaci, ya akaine?"
"Ganinka nake sanyi yanzo a Sahaf Restaurant ina nufin yanzo"
"Ina wani gaggarumin aiki a office amman wallahi dole zan barshi inzo kiran gimbiya da kanta"
"Kuma ina bukatar kudin da suka kai darajar miliyan biyu"
"To zan maki sending yanzo"
"Kada ka fara kash nake bukata"
"Angama gimbiyar mata"
®Nagarta writers association.
