SOMIN TABI

2.7K 180 14
                                    

*KASAITATTUN MATA*
(Labarin mata ukku)

               ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

                 ©
*BILKISU BILYAMINU*

              *14*

     *_Bauchi_*

     Jallabiya ta saka mai ruwan kasa ta saukar mata bar kasa sannan ta yane kanta da dankwalin jallabiyar iyakar kyau tayi musamman da yake bata cika kwaliya ba kumai nata simple sai tayi maaifar yin kyau na fitar hankali, sosai take da kyau mai burgrwa, yar karamar jikka ta dauka mai kalar gwaldin ta saka wayoyinta ciki, sannan ta saka kalolin turaraukan da sunkai kala goma ciki babu na banza, kamshi mai dadi me tashi a dukkan sassan jikinta, waya ta daga ta kira Saleem tace"kai kawai nake jira, na gama kumai"
   Wayar ta kashe da cikin jikkarta wata wayar tavfara kuka tana Neman again gaggawa, said a ta tsinke aka kara kira sannan ta buds jikkar ta dauku sunan data gani saman wayar ne yasa tayi tsaki ta maida wayar cikin jikkar, baki ta taba tace"Namamjo wanda bai iya rayuwa sai da mace, maye kawai"
   Kuka wayar take amman bata daga ba, tabkwana da sanin bazai daina kiranta ba had sai ta daga,tsaki ta kara yi sannan ta fidda dukka wayoyin ta ajeye bayan ta kashe gaba dayansu, kada ya bata mata mission dinta dan bada wasa ta dauki hidimar wannan karan ba, a gaba daya rayuwarta wannan ne aiki na biyu da take hango waharshi, Amman kumai wata zuciya na fada mata cewa ai kina da kyau kuma kina da ilimi kada kisama ranki akwai wahala zaki nasara.
   Wayar dake hannunta ta fara kuka, ta duba sai taga Saleem ne, tashi tayi sannan ta kara gyara fuskarta ta kara baza turaranta mai daukar hankali ta fito ta rufe dakin, sannan ta wurga card din cikin jikkar ta.
    A harabar hotel din ta iske Saleem yana jiranta cikin izza tace mashi"Ina ka samu wannan motar"
   "Haya na amsu ta, kinsan naje a matsayin babban mutum mai dala a hannu kinga kuwa dole ya tabbatar da haka"
    Baki ta taba tace"Aikinka na kyau"
   Dariya yayi yq shiga motar itama ta shiga suka kama hanyar da zata sadasu da Abdulwaheed and son's Nig limited"Nawa ka amsu motar?"
    "Dubu goma awa biyar"
    "Zan maida maka, kumai ai na kudi ne tunda nima kudin zan amsa"
   Sun isa aka bude masu gate suka shiga,  wani dan daki suka fara isa kafin sannan wani matashin saurayi yayi masu iso wajan shi, da sallama suka shiga, sassanyar iskar ac ya buge hancinta da wani daddadan turare mai kwantar da hankali da sanya zuciya nishadi, idanuwanta ta dauka ta aza bisa wani tangamemen hutun da ya kusa mamaye rabin bangwan wajan, shine shida wata kyakykyawar mata da yara biyu mace da namiji, kallo data zaka ma potan ka fahimci akwai kyarkyawar rayuwa da siyayyar juna a zukatan wadan da suke jikin photan.
   "Bismilla kuna iya zama"
   Wannan kalmarce ta doki dodan kunnanta, idanuwanta ta aje saman tashi sosai taje faduwar gaba, kyakykyawa mai kyau na daukar hankali, yana da kyan da batasan ya zata misaltashi ba, a hankali ta lashe leben kasan bakinta, sannan ta nemu natsuwa ta azama kanta.
   Cikin wata sigar yaudara tace"ina wuni"
   Bai dago kanshi ba, yana cigaba da dannan computer dake gabanashi yace"ya kike?"
    Banza tai dashi bata kara tankashi ba saboda tasan shima yana wasa ne saboda bata mu'amala da isarshin namiji mai gadara da isa, idan har ita bayi isaba to babu namijin da zata yadda yayi mata haka.
    Kallanta Saleem yayi, ta zungura mashi baki alamar ya kura bayani, gyara zama Saleem yayi yace"Ranka ya dadi kamar yanda mukayi da kai zan kawo maka kanwata, to Allah yayi gamu gabanka"
    Bai dagu kaiba har yanzo yana aikin gabanshi yace"Eh, nagane, to yanzo tazo da shirin kumai ko?"
    "Lamar wani shiri ranka ya dade?"
    "Kamar takardu haka da kuma shirin ganawa da Wanda zai mata interview"
    "Eh tazo da kumai kuma a shirye take"
    
    "Ok, zata Ibrahim, bari in mashi magana sai Ku sauka kasa kume kinan zai nemeka sai ka bashi number dinka, ka gane ai"
   "Na gane ranka ya dade"
    Kanshi ya dago da niyyar ganin sabuwar ma'aikaciyar, idanuwanshi suka chakuda da nata, wani shork sukaji gaba dayansu, sosai ya kadu da ganin halittar dake gabanshi, murmushin mugunta ta jefa mashi sannan ta yi luuu da idanuwa kamar tanajin bacci, da sauri ya dauke idanshi daga kanta yace"Kuna iya tafiya"
    A hankali tace"mungode fa ranka ya dade"
   Kallanshi ya kara ajewa saitin fuskarta, wane murmushin ta kara dukanshi da shi, kanshi ya dauke sannan ya sake ajiyar zuciya mai karfin gaske bayan ya tabbatar da sun fita, tsaki yayi sannan ya kuma aikinshi.
   Kasa suka sauka, bayan sun iske Ibrahim din ganin zubin Aisha Beauty yasa bai tambayi kumai daga gareta ba yace ta tafi kawai zai shaida mashi ta cancanta, saboda duk gayun Ibrahim amman a gaban Aisha saida ya raina kanshi musamman data tasashi da mayun idanuwanta tana aika maahi da mayaudarin murmushi.
   



KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now