DAUKAR FANSA

2.1K 173 5
                                    

        ayi min hakuri dan Allah, ina sane daku ayuka suke sha min kai, nasan kuna fahimta ta ai

   best regard to, BILƘISU BILYMINU

ina sanku fisabilillahi  


         Club ɗin gaba ɗaya ya turnuƙe da hayaƙi, daga wai-wai da hayaƙin shesha da dai sauran abubuwan dake haddasa matsala idan an kurasu a cikin cikin ɗan adam, a  tsanake take tafiya har ta isa inda babu cikuwar mutane kujera ta samu ta zauna ita ɗaya sannan ta gyara zaman ƙatan tabaran da ta ɓoye idanuwanta ciki,  cingum ta fidda ta wurga cikin bakinta sannan ta fara taunawa tana kallan kuwa ɗaya bayan ɗaya cikin ɓoyayyan gilashinta,  a duniyar Minal wannan shine abu mafi girman da take ƙauna a gaba ɗaya duniyarta.  taga tana tsola tsiyarta san rai, sannan ta ɓata kuɗi kamar ita ta ƙerasu,  to hakarta ta kusa cimma ruwa,  zuciyarta ce ta ɗauketa ta kaita can wata duniyar tunani take ya za'ayi ta zama kamar Nuwaira idan da hali ma tana da buƙatar tafita juya kuɗi ta zama kuma ƙasaitacciyar mace,  dan tasan ta fita kyau da zubi na bada sako kuda gaban ustaz ne, bata tunanin kumai a duniyarta yanzo.  Ummanta ta mutu,  Baffanta kuma baya santa asali ma shida Baba Laritu sukayi sanadin barinta gidansu,  tasan bata da kuwa kuma bata san inda zata ga wani wanda zai ce shi dangin tane,  zuwa yanzo ma bata tunanin kumawa gida dan shi kanshi gidan yanzo bata iya rayuwa cikinshi musamman data tabbatar da ɗan adam yana da yanci har haka, Amman kuma kafin ya kai irin wannan matsayin data fara bude ido ciki sai ya sha wahala,  dan ko kusa da manta wahalar da tasha hannun Nuwaira kafin ta maidata yar hannun ƴar Harka irin haka tasha wahala,  iyakar azaba ta ɗan ɗana,  dan bata taɓa tunanin akwai mahalukin da zata barshi ya tura mata hannu a inda ita kanta a da bata san amfaninshi ba idan ya wuce fitsari kawai. Amman zuwa yanzo tasan yana da amfani sosai kuma shine abinda ya kawo mata  wannan ɗaukaka data faɗa yanzo,  ku babu kumai ma yanzo jin abun take kamar yafi zuma dadi.  A takaice ma yanzo tasan barin wannan abun wani nakasune a gaba ɗaya duniyarta (turƙashi lallai MATA kuna cikin bula'i,  shin ana barinshi watau maɗigo Amman sai ankai ruwa rana,  shiyasa gudun kada ayi kada a fara dan barinshi abune wanda ake tursasuwa sannan kuma sai an hada Jin ɗacin zuciya Allah ya kiyashemu wannan rayuwa masuyi kuma Allah ya fiddasu kuma ya shiryesu idan ba masu shiryewa bane Allah ya fiddasu cikin al'umma salihai kuma mumina)

          Faskeken agogon hannunta ta duba tana ƙissima minteka ashirin suka rage mata ta tafi,  domin tana san zuwa ta siya abubuwan da take da buƙata a wata super maket da suka taɓa zuwa da Nuwaira,  tukunyar sheshan aka kawo mata gyara zama tayi sannan ta fara zuka tana fisarwa gwanin ban mamaki,  a yangance take kumai saboda jinkanta take wata irin halitta mai mutunci da daraja da tsada.

           Cikin takon isa da ƙasaita yake tafiya zama yayi cikin kujerar dake ɗaya daga kujerun wajan,  ƙafa ɗaya ya ɗaura saman ɗaya sannan ya dinga wurga idanuwanshi inda duk yasan zai hango babbar cika,  dan yau a sama yake sosai yake buƙatar wadda zai huta da ita a cikin daran wannan ranar, idanuwanshi ya ɗauka daga can lungun da ya hangeta,  Namijine mai aji da kuɗi sannan ba kasafai mace ke bashi sha'awa ba,  sai idan ta kasance ɗaya daga cikin wadan da yake jin zai iya hada ƙwazanshi dasu, a tsarin rayuwarshi babu soyayya tun sanda akayi  breaking heart  dinshi yayi imani bazai ƙara san wata ba,  wasu lukutan ma mata haushi suke bashi idan ya gansu a kewayanshi, leɓen saman bakinshi ya lasa sannan ya kira ɗaya daga cikin mamallaka aikin wajan yace"Ina kiran waccen yarinyar"

         "Ok bari a faɗa mata, Oga Mainasara" tuƙeƙen ma'aikacin wajan ya faɗa.

          Da matukar azama yake ɗaga ƙafafuwanshi yana ajesu a inda yayi imani zasu kaishi har inda Minal take.

         "Am Hajiya Oga Mainasara yana magana dake"

          Sai data zuƙe shesha sannan ta fisa mashi hayaƙin a saman fuska,  ɗan ja yayi da baya sannan ya gyara zama,  glass dinta ta sauke daga idanuwanta sannan ta saka idan ta cikin mashi tace"Na maka kama da karuwa a nan wajan ne?"

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now