ABU IRFAN

1.1K 85 0
                                    

*ABU IRFAN*
( *love story 2018*)

© *Khadeeja ahmad*

® *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
    (Home of expert & perfect writers)💡

        
                 💕 11 💕

*2:30pm*

Dropping d'insu yayi a gida ya ja mota zuwa red bricks, da sallama suka shiga gidan da gudu sukayi sama suna daf da 'kofar shiga d'akin ta fito hannu ta shiga tafawa
  "Oh ni Abu wai yaushe ne yaran nan zaku san kun girma?, ke yanzu Idan  ita tayi gudu ke kya fara da wannan tatsitsin cikin salan ki jawa kanki wani abun"
  Tsuru tsuru sukayi sanin cewar basu kyauta ba
"We r sorry mami" suka fad'a tare had'e da hugging d'inta,
  "Uhm haka dai fad'a a fatar baki ba, aikatawar ce wahala, ni ku d'agani muje ciki" dariya sukayi hannayensu cikin nata suka koma d'akin, nan suka zube kan makeken Italian bed family size suka shiga hira.

***
Hankalin sa baki d'aya na kan driving d'in da yake jefi jefi yakan sa musu baki cikin hirar siyasar da suke wanda Abba ke karantawa cikin jaridar punch idonsa ma'kale da medicated glass,  Alhaji kuma na baya  yana duba wasu takardu, jin sunyi shiru yasa shi dad'a 'karar radio yana sauraren quiz d'in da ake shiryawa a tashar freedom radio cikin harshen turanci.

   Du'ke yake gaban hajiya tamkar me d'aukan karatu yana sauraren fad'an da take mishi
  "Hashim  yanzu da hankalin ku kuka biyewa shirmen yarinyar nan wacce addini be ratsa ta ba ko 'kalilan? Me zaku cewa da ubangijinku Idan kun koma? To billahil azim tun wuri ku nemi gafarar ubangiji ko dake shi sakaran abokin naka ma ba lallai yagane abunda ake jiye masa ba"

"Hajiya tuni kamal ya dawo kan hanya dan shine ma ya tilastani zuwa acewar sa bazaki saurareshi ba"

"Taya zan sauraresa, ko dake da yaso ai ze sanar min da haka tun kafin abin yakai ga haka Dan Alhaji ya d'au fushi badan zuwan Abba ba da Allah kad'ai yasan hukuncin da ze mishi, amma karku damu after jin abinda kace I'll make sure I make him understand, I'll make him understand tuggu irin na mace Dan banajin haka tabar yaron nan"

"Nima dai hajiya ba abinda bezo mind d'ina ba amma Dan Allah ki fahimtar da Alhaji"

"Uhmm, to bakomai zan yi iya bakin 'ko'kari na"

'Kasa yayi da kai
'To hajiy mungode"
"Bakomai Hashim Allah yayi muku albarka, inaso koda yaushe zakuyi Abu Ku rin'ka tuntu'ar manya,  Dan abinda babba ze hango yaro baya ta'ba hangowa ko da kuwa ze hau dutsin dala"

"Hakane hajia mun gode 'kwarai Allah yaja da rai"

Dariya tayi da cewa"Ameen"

Har ya kai 'kofa ya jiyo
"Aff amm hajiya na manta..."
Ta katseshi

  "Dawo ciki mana ka tsaya bakin 'kofa??"
Sum sum sum ya koma gefen 'kafarta ya zauna zuciyar sa na wani bugu dan besan da wace fuska zata kalli zancen nasa ba.

"Hajiya dama..."

***
Cikin takunsa na 'kasaita ya nufa cikin gidan jiki a mace, tun a hanyar dawowar su daga farm house yake fad'uwar gaba he don't know why karatun Qur'ani ya rin'ka rerawa a hankali har kawowa yanzu.

Kafad'ar shi yaji an dafo d'ago kai yayi idonsa suka sauka cikin na Abba, Abba ya kad'a kai
   "Ya dai mutumin?"
Murmushi yayi
  "Abba ba komai kawai de inaji nane ba daidai ba"
D'an dukan bayanshi yayi
"Khairan insha'Allah, ka yawaita salatin nabiyy"
Girgiza kai yay alamar toh   suka jera tamkar abokai zuwa cikin gidan.

  Tun bayan isha'i take kiransa a ways almost 12missed call be d'aga ba be kuma kira dan har yanzu wani tu'ku'ki yake ji saboda abinda tayi mishi da safe kafin ya fita, jin kiran yayi yawa yasa ya kashe wayar ya maida hankali kan hirar sa da Abba lokacin su hajiya da Alhaji suka shigo falon, bayan hajiya tayiwa Abba sannu da zuwa ta juya dan komawa
  "Hmm..nace Idan  ka gama ka sameni a ciki"
Sanin cewa dashi take kamar dama jira yake yayi saurin mi'kewa dan gujewa kallon da yaga Alhaji na mishi, saida safe yayi musu ya mara mata baya.

  Nasiha tayi mishi me kashe jiki har besan lokacin da yayi 'kwalla ba a hankali ya 'karasa jikinta ya rungumeta
  "Hajiyata nagode da kika fahimce ni"
Shafa lallausan gashin Kansa da yayi luf luf a kanshi tayi,
"Ka cigaba da neman yafiyar ubangiji"
Nodding yayi
Hajiya ta nisa tace
  "Kamilu zaka iya ri'ke mata biyu??"
Saurin d'agowa yayi daga jikinta dan be ta'ba expecting jin hakan ba, cikin rawar murya yace
  "Ah...a..am"
"Uhum?.."
'Kasa yayi da kanshi a hankali ya furta
"Eh hajiya amma bisa yardar ku"
Dariya tayi irin ta manya
"To kamilu kana ganin zaka iya kwatanta adalci tsakaninsu duba da yacce kake da hamdiya? Dan banason ka tashi ranar gobe 'kiyama da shanyayyen 'barin jiki"

Iska ya busar "insha'Allahu hajiya ta"
"To shikenan, Hashim ya Sanar mini yarinyar 'kanwar matarshi ce na kuma ji dad'i dan iyayen su manyan mutane ne nagartattu bani kuma da haufi da tarbiyya dan nasan Alhaji  Ahmad pantami tsayayye ne ko ta Ina ga taimakawa addini, gidan marayu, gajiyayyu da sauran su to nasan insha'Allahu bamu da damuwa na sanarwa da mahaifinka ya kuma ce ze duba maganar so duk yacce ake ciki zan sanar maka"

Hussaina tayi sallama idonta kan Kamal

"Yaya kamal ya hamdy tace na fad'a maka ka biya ta gidansu ka d'aukota Idan zaka wuce"

"What?? gidansu??" Sounding so tensed

  Gyad'a kai tayi "eh haka tace wai takira ka bata sameka ba"

Ransa ya sosu jijiyon kansa suka fito rad'a rad'a idonsa ya kad'a shin yaushe hamdy za tayi hankali ne.

"Kamilu"
"Na'am hajiyata"
"Tashi kaje dare nayi ka biya ka d'auko ta"
Girgiza kai yayi murya a raunane yace
"Saida safe"
"Allah ya kaimu, a rin'ka hakuri kaji"
Ya girgiza kai hussaina da jikinta yayi sanyi ganin sudden change d'in yayan nata taja 'kafa ta koma d'akinsu.

  Tunda suka shigo gidan kallon Inda take beyi ba, ko a jikinta sai ma kintsa jikinta tayi cikin wasu arnan nighty ta nufi d'akin shi handle ta murd'a taji gamgam alamun ansa key jiki a sanyaye ta juya sanin ko ta tsaya knocking ba bud'ewa ze ba.

  "Mtwww..mutum sai shegiyar zuciya"
Ta fad'a fuska a ya'kune kan ta wuce d'aki ta fad'a gado.

***
Tsintar kanta tayi cikin tsantsan farin ciki a ranta takasa gane dalili sede kuma ta ala'kanta hakan da zuwan da sukayi gida shekaran jiya da kuma statement d'in mami game da Kamal bugun zuciyanta ya dad'u har sae da ta dafe da hannu tare da runtse ido a hankali ta zira hannu kan chase drawer ta d'auki wayar ta dake faman ringing har ta katse wani kiran ya kuma shigowa murmushi ta saki lokacin da ta gan sunan me kiran "'kawata ni kad'ai" ta furta had'e da d'agawa ta kunna handsfree tare da yin sallama

   "Raihana 'kawata"

   "Aminiya ta ta kaina"

"Ke 'yar gari d'azu iyayen umar sun kawo 1mil. Kud'in nagani inaso"

Tashi tayi daga kwanciyar cike da farinciki tace
"Kai 'kawata amma nayi miki murna Allah ya Sanya alkhairi, ubangiji yasa ayi damu dan Allah kiyi wa aunty Allah sanya alheri kafin nazo"

"Amin 'kawata saura kema insha'Allahu Mr right ya kusa kawo wa duk da nasan 'kila ma ya kawo shegen zurfin cikinki baze bari ki sanar dani ba" ta 'karashe a wani dry sound.

  Murmushi kawai tayi tare da basar da zancen suka shiga hirar yaushe gamo, deep down inside her she really want to spill it out to her very bestfriend but batasan meyasa ta kasa ba, 'what is the hurry for abinda yau kwana biyu kenan ko nemana beyi ba' ta ayyana a ranta, koma dai mene u I know am in his heart cox his eyes and body says it all wani kyakkyawan murmushi tayi tuna scene d'in da sukayi making few days ago. Da wannan tunanin bacci ya 'barawo ya sace ta cike da mafarkin her one and only *Kamal*    

*dia is d edited chappy*

© *Kdeey* 😊

ABU IRFANWhere stories live. Discover now