ABU IRFAN 17

1K 85 2
                                    

*ABU IRFAN*
( *love story 2018*)

© *Khadeeja ahmad*

® *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
    (Home of expert & perfect writers)💡

         
                        💕 17  💕

WATTPADD @ *Deejaht Ahmad*
#Ur vote n comment means alot to me
#onelove

  *Important note:*
     Bazan ce na dena typing ba se dai inaso kumin uzuri dan bazaku ke samu akai akai ba due to some reasons Tnc u.

***
  Sumbatar goshinta tayi
  "Autan mami nima zanyi kewar ki, yanzu tashi maza ki shirya nasan sirikin nawa na tafe kada yazo baki kintsa ba"

Da sigar shagwa'ba tace
"Mami bafa lallai yazo ba fa"

mami tace
"Ja'ira da bansan halin shi bane, mutumin da tun da biki ya gabato baya kwana biyu be le'ko ba tun ina hanaki fita kada ya gane miki gyaran da ake har na ha'kura dad'inta dai Yana tazo gari tayi min maganin ku muga ta soyayya"

Rufe ido tayi da hannu
"Kai mami"

Mami da
tayi gaba tace "kyaji dashi dae yaran zamani se a bar ku"

  Cike da kunya ta koma jikin gadon ta jingina rungume da pillow zuciyarta fal tunanin angon nata.
  'Dala mata dukan da akayi ne yasa ta d'agowa had'e da fad'in
  "Wash hajiya da zafi fa.."ta sa hannu ta sosa wurin

   "Sorry dee naga kinyi nisane ina ta rafka miki kira baki ji ba, ki taimaka ki rage tunanin nan kar mukai amarya a 'kanjame ayi mana gori"

  "Hmm..hajiya kinsan dai tunani dole ne a gareni idan kikayi la'akari da state d'in danake ciki, kinsan ma wani abu??"

Ta na me gyara zama a bakin gadon tace
  "Sai kin fad'a"
"Hajiya ban ta'ba hirar makaran ta da kamal bafa"

  "Ko zan san mene dalili?"

  "Ni kaina banace ba, shaf abin ya kwanta min kuma maganar gaskiya inason ci gaba da karatu na" ta sauke numfashi,
    hajiya babba tace "amma kin so ki ganganci maganar gaskiya tun yau ba gobe ba ki masa magana kiji view d'insa saboda kisan madafarki, amma ya kike ganin yanayin sa yana son karatu?"

  "I can't say gaskiya tsakani na dashi kan maganar karatu kawai tun lokacin da na fad'a mishi i'm a graduate of bayero uni. Where i study BSc. Chemistry shikenan"

  "Did he say something bayan nan?"

  "Aa kawai cewa yayi Allah ya sa albarka blah blah blah"

  "To deedee bazan iya  ce miki ga ta'kamaimai abinda na gano game dashi ba amma idan kika duba he knows what it meant to be well educated banajin zaki samu matsala daga gare shi"

Komawa tayi da baya ta kwanta
  "Arghh...yeah haka nake tunani"

  Ta tashi da sauri idonta kan agogon dake manne jikin bango "laah na manta bara nayi sauri nayi wanka kafin ya 'karaso" ta fad'a toilet
  Knockn tayi bisa 'kofar tace "karki manta kiyi wanka da sabulun aunty yana.
   "Uhummm" ta ansa daga ciki

***
   she's sitting in there looking like an angel dat was sent down from the sky smiling so bright her cute chicks na ta glowing fararen jerarrun ha'kwaranta se haske mishi ido suke yayin da siraren lips d'inta ke ta 'kyallin sadau matte lipstick 'red,' ya sauke idanunshi kan zarazaran yatsun ta masu d'ankaren kyau tamkar ita tayi wa kanta se faman kare fuskar ta take ganin yacce ya zuba mata na mujiya wanda  farin security light ya taimaka mishi wajen dad'a haskaka mishi ita da ko ina na cikin garden d'in.

Kuma kallonshi tayi karaf sukayi 4eyes ta turo cukulin bakinta
   "Kana son korata da wannan idanuwan naka"

  Murmushi yayi wanda ya d'an fidda fararen ha'kwaren sa
  "Baby doll yakamata ace kin zama used to it cox u'll live with them"

ABU IRFANWhere stories live. Discover now