ABU IRFAN 18

1.1K 86 3
                                    

*ABU IRFAN*
( *love story 2018*)

© *Khadeeja ahmad*

® *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
    (Home of expert & perfect writers)💡

         
                        💕 18  💕

WATTPADD @ *Deejaht Ahmad*
#Ur vote n comment means alot to me
#onelove

***
   "Deedee maza tashi ga ruwan wanka can na had'a miki mu zamu je dubiyar abokiyar zaman ki"

   Zumbur ta tashi zaune,
"Aunty yana wai dagaske zuwa za kuyi?"

"Ah ah banda abinki abinda zumunci ya riga ya 'kullu to ko me za a fasa, ni maza tashi da Allah ki watsa ruwan kada ya huce idan kin kintsa ki wa lamtana magana na sa ta d'imamo miki tuwo saboda kisha maganin nan kinsan an fiso asha da 'kosashshan ciki saboda drowsiness"

   A kasalance ta gyad'a kai tare da 'ko'karin kwanciya, aunty yana da harta kai 'kofa ta waigo
   "Deeja zan sa'ba miki matsawar na dawo na tarar bakiyi abinda nace ba"

  "Huh! Ok aunty insha'Allah"
"H...hh b..ba zaki ce su gaidah.. shi ba"
cewar hajiya babba da ta banko 'kofa tana haki da alama gudu ta sha, aunty yana ta kai mata duka
  "To mara ta ido ance miki itama irinki ce"
   Dariya sukayi ta wuce suna mata a dawo lafiya .
    Rausayawa take tana juyi "aminiyas my wedding mate tashi ki tayani juyi..my habeebi my oumri is on his way back to nigeria for our wedding"
   Gyara zama rayi had'e da jingina jikin gado ta juya kwayar idonta
   "Amma na taya ki murna 'yar uwa"
    Hajiya babba da baki ya'ki rufuwa ta zauna gefenta
  "Wash Allah ai wullahi nayi mutu'kar farin ciki lokacin da aunty hauwa ke sanar dani har tukwicin katin waya na bata"
  Deejah ta zaro ido
  "Ahh..ke kuwa a yanzu banda ranar da ze zama mallakina ai ba labarin da yafi wannan dad'i, yanzu dai tashi ki watsa ruwa kar aunty yana ta dawo ki ja min laifin ya dawo kaina ban shirya d'aukan fad'a ba"
Gira ta d'aga ta saukar da 'kafafunta 'kasa kenan taji 'karar message bud'ewa tayi ta karanta murmushi ya mamaye face d'inta.
 
  "Ya dai amarsu?"
"Kamal ne"
  "Ya jikin matarsa kuwa?"
Ta d'aga kafad'a "i dunno sha ba muyi magana ba"
Wani kallon mamaki hajiya babba ta yi mata
  "Kar ki 'bata wayonki mana ya ina miki kallon wise ashe u r opposite ke da ya kamata ki kirashi ki kwantar mishi da number 8"
Ta had'e fuska
  "Ni kuma? Matar sace fa ba lafiya"
    "Ohh wait? Kar ki zama cikin jahilan matan nan mana wanda kishi ke rufe ma ido, ki amfani da ilimin ki se kace ba mace ba abeg call him yanzu tun kafin ki shiga wankan nan naki da sai ki shekara kafin ki fito"

Sorry face tayi
  "Ni wlh wlh.."

Fizge wayar hajiya babba tayi ta shiga dialling number Kamal.

***
Dr mahfuz ya zare medicated gilashin dake manne a fuskar sa ya cigaba  da rattabo musu bayanai

     "Hawan jini ne da damuwa suka had'ar mata so ba damar muyi mata aiki a 'kafar har se jinin ya sauka"
   Hankali tashe kamal ya zira hannu cikin lallausar sumar kanshi
   "Ba matsala Dr amma yaushe kake ganin ze iya sauka?"
    "Anytime ze iya zama yanzu anjima gobe kwana d'aya, sati, wata."

  Ya tashi tsaye bayan sunyi musabaha ya fita inda su hajiya da hashim suke ya nufa.
   Muryarta ta ziyarci kunnen shi yayinda ta cika d'akin fam da bala'inta daga wurin da yake yana iya jiyo mugayen kalaman dake fita a bakinta ransa ne yayi mugun 'baci lokacin daya isa d'akin ya tarar da fuskokin da yake jin nauyi sunyi jugum jugum yayin da ya sauke rinannun idanun shi a kanta wanda 'bacin rai ya maida su jazur, mara lafiyar da ake jinya kuma na zaune hawaye na bin fuskar ta, dame zata ji da ciwo ko da damuwar dake nu'kur'kusar zuciyar ta.
  
  Murya na rawa yace da hajiyar sa
"Hajiya zamu iya tafiya ya nuna mata hanya"
  Kallo d'aya ta mishi ta d'auki jakarta jiki a sanyaye suka fita haka inna matar megadi da suka zo tare da hajiya itama ta bi bayan su.

ABU IRFANDove le storie prendono vita. Scoprilo ora