*ABU IRFAN*
( *love story 2018*)© *Khadeeja ahmad*
® *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(Home of expert & perfect writers)💡
💕 24 💕WATTPADD @ *Deejaht Ahmad*
#Ur vote n comment means alot to me
#onelove**
Kai ko mo take a tsakan kanin d'akin ta, yau weekends kamata yayi kamal ya zamana a gida amma ina ya tafi har yanzu be dawo ba? i need to apologies in har ina son mijina which i really do daidai lokacin wayar ta tayi ringing,"Hello mom"
Daga d'aya 'bangaren ta ansa
"hamdy be prepare to.."
'Karar motar da taji yasa ta dakatar dabita
"hold on mom ina zuwa" tashi tayi ta le'ka window inda ta hango deejah ta fito sanye da ba'kar abaya ta shiga motar kamal sun fita.Wani irin ihu ta saki har se da mom ta janye wayar a kunnenta
"Lafiya hamdy??"
"Mom kinga...kinga ya d'auke ta sun fita sun barni ni kad'ai, wayyo Allah na shiga uku, mom kin ja min wullahi duk laifin ki ne if to say ban biki nijar ba and stick to your stupid plan da duk haka bata faru ba"
kuka take tun 'karfi, mom kuwa takaici be bari tayi magana ba se ma wayar da ta zame a hannun ta ta fad'i, zuciya na 'kuna ta tashi ta zari gyalenta daidai d'akin masu aiki ta tsaya ta d'aga murya"Saudatu!! saudatu"
"Na'am"
ta ansa daga ciki kan daga baya ta fito ta tsugunna
"Inaso zan fita idan alhaji ya dawo ki san abinda zaki fad'a mishi dan ta yiwu se dare zan shigo"
Saurin kallonta tayi "to hajiya Allah yasa dai lafiya"
"Ita ta kawo haka" ta bata ansa a 'kafule fuuu ta wuce ta barta a dur'kushe numfashi ta sauke daidai lokacin ta hango bilkisa da usman sun jero , tuni ta nemi 'bacin ran ta rasa da d'an sauri suka nufo ta bilkisa kuwa har da d'an tsallenta ta na zuwa ta fad'a jikin ta
"Hajia inno ta sannu da gida"Murmushi tayi yayin da usman kuwa 'kasa ya tsugunna yana gaida ita
"Kayya tashi tashi tsaye haba usman na hana ka dur'kuson nan ka'ki ko?"
Sosa kai yayi ba tare da yace komai ba, ta cigama
"Ita gaisuwa ko da ba a tsugunna ba gaisuwa ce, se dai al'ada data bi jikin mu na cewa dole a tsugunna dan nuna girmama wa ko kuma a rissina, nagode kwarai da baka duba mud'in ba ko wane ba face masu ai..."Saurin katse ta yayi
"Dan darajar Allah inno ki bar maganar nan damu daku duk d'aya muke bamu da bambamci, kuma a tunani na ko ba bilkisa ke d'in tamkar mahaifiya kike a gare ni""Hakane Allah yayi muku albarka ta juya kan bilkisa da tayi lakur a kafad'arta
"To mage sarkin bin laushi maza aje ayi wanka aci abinci lokacin islamiyya na gabatowa"Kunya taji tasa hannyenta biyu ta rufe fuska
"Kai inno"Dariya inno tayi irin ta manya, usman yace
"Inno dama daddy yace na fad'a miki za suzo sa rana"Jin haka ai a guje bilkisa ta gudu cikin d'aki
"To madallah babu komai ai amma kamata yayi ka samu alhaji da zancen tunda shine matsayin mahaifi a gareta""Eh shine yace na fad'a miki tukunna"
"Ba komai ka shaida mishi duk yanda sukayi daidai ne"
Sallama yayi mata tare da godiya.***
HospitalKuka sosai take tana rirri'ke Kamal
"Shush baby ki bar kuka insha'Allahu she will be fine"

YOU ARE READING
ABU IRFAN
RomanceABU IRFAN is my world i vow to love him till eternity... Inason ki deejah bazan ta'ba dena fad'a miki hakan ba... Na rantse ko ina masarsarar mutuwa se na ga bayan zaman kamal da deeja...