*ABU IRFAN*
( *love story 2018*)© *Khadeeja ahmad*
® *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(Home of expert & perfect writers)💡
💕 19 💕WATTPADD @ *Deejaht Ahmad*
#Ur vote n comment means alot to me
#onelove***
Sanator bazallah ya gyara zaman shi tare da sauke idanun shi kan malam me buzu dake tankwashe 'kafafu kan ya nisa yace
"Wato malam hamza kai kad'ai nake iya bud'ewa cikina kaji ka kuma bani shawara, to yau ma dai bisa matsalar 'yar waje na ce da na shaida maka shekaranjiya"
"Oh toh toh hamdiyya ba?"
"Eh ita, wato bansan meke faruwa ba haka kuma na rasa wanda zai sanar min ko ban fad'a maka ba kasan halin 'yar uwar taka dai (mom) cikin kaso d'ari a maganar ta dakyar ka samu gaskiya d'aya, to kuma wurin mijin nata har ila yau ba wata kwakwkwarar magana da suka shaida min kai yanzu haka ma bana samun mahaifinshi a waya ko shima har yau banji daga bakin shi ba shine nake so ka bani shawara me ne ne abin yi dan gaskiya ina neman mafita ne kuma ni da kai mun san halin Alhaji yaro hakq zalika iyalansa an yi musu kyakkyawar shaida "Malam me buzu ya jinjina kai
"To Alhaji naji bayanan to sai dai inaso ka bamu lokaci zuwa gobe naje na dawo duk abinda na gano zan shaida maka idan yaso sai mu san tufkar da za muyi wa bakin zaran"
"Hakane madallah hakan yayi shiyasa nake jin dad'in al'amuranka, yanzu ne zaka nemo min solution"
"Da yin Allah ba ai komai se da yin ubangiji haka zalika Alhaji ina me dad'a baka baki kan hajiyar ayi ha'kuri da halayenta nasani kana 'ko'kari Allah ya 'kara d'aukaka"
"Amin amin ai an zama jiki bakomai nagode da shawarwari"
"To bakomai ni bari na koma dan ina tunanin ba'ki da yamma"
Senator ya zira hannu cikin aljihu "a haba ba komai ga wannan a yi cefane zan sanar da driver ya sauke ka gida"
Hannu biyu yasa tare da rissinawa ya kar'ba yana mishi addu'a.Daga cikin gidan senator kuwa...
Wayar ta da ke 'kara alamun kira ya shigo ta d'auka tare da 'kaga ta a kunne ta shiga magana da wani yare bayan ta gama ta kalli hamdy wearing a weaked smile
"Ki shirya asubar fari zamu kama hanyar nijar"
"Nijar kuma mom me zamuyi a can?"
Ta kyabe baki
"Well inason kwato miki hakkin ki ne ganin 'kiri 'kiri za a nemi nakasta miki rayuwa da wata shegiya kishiya"
"Oh Mom shiyasa nake sonki amma what abt my leg"
"Karki damu tunda har kina iya takawa i guess zaki iya jure zama ai, kedai ki kasance cikin shiri bari naje na tsara tsohonki"Ta fice daga d'akin
Baya ta koma idonta a ceiling murmushi take saki a fili tace"U'll regret sanin kamal, kamal nawa ne nawa ne ni kad'ai dan ni kad'ai aka yo shi"
***
A yau laraba ake sani a lalle jama'a sai tururuwa suke yi ta ko ina, 'kawayen hajiya babba da suke matsayin 'kawayena dan kuwa bani da 'kawa tun bayan barin khadija muhammad wacce take aminiyata tun yarinta garin kano ta koma meduguri daga can kuma ta wuce UK karatu ban kuma ji daka gareta ba, sai few of my classmates daka islamiyyar da nayi, abokan arzi'ki na nesa dana kusa duk sun hallara sai shewa ke tashi ga abinci nan kala kala da drinks sai ciye ciye ake, daman mami musamman ta hayo kwararrun masu abinci har a 'kare hidimar biki.Zuwa yamma mu da 'yammata muka wuce gidan ya Aisha dan yin bridal shower this is my idea cox i loved dis event inda a kayi decorating harabar gidan da fitulu da roses komai a gurin pink nan muka sha games irinsu truth or dare da rawa har zuwa 12:40am sannan kowa ya nemi makwanci a part d'in ya Aisha dan nan ta bar mana ta gudu turaka.
Washegari bikin al'ada mukayi wato wushe wushe inda aka nad'a mu cikin jajayen lafayoyi wuyanmu,hannu, kafa da kunne duk sunsha gwala gwalai, sai arnd 5:00pm aka tashi a gajiye li'kis na shiga toilet na cika bath tub da ruwan zafi daidai jikina na gasa jikina sosai kafin nayi wanka na fito na kwanta dan hutawa kafin fulani night d'in da su aunty soffy suka shirya mana.
Ringing d'in waya ta ce ta fargar da ni daga d'an 'barawon baccin da ya sace ni hannu nasa na janyo ta nayi answering had'e da sallama muryar da naji ta doki dodon kunne na ce ta sani yin farr na bud'e ido cox ever since aka fara bikin nan i'v never heard from him

YOU ARE READING
ABU IRFAN
RomanceABU IRFAN is my world i vow to love him till eternity... Inason ki deejah bazan ta'ba dena fad'a miki hakan ba... Na rantse ko ina masarsarar mutuwa se na ga bayan zaman kamal da deeja...