So gamuwar jini

606 24 0
                                    

Jos plateau state(home of peace and tourism)
UNGUWAR BAUCHI ROAD
* * * * * *
Kicin-kicin tayi da fuska tana shirin sakin kuka a yanayi na shagwaba,don bata cika son jin zance da brother Abubukar dinnan yake mata ba,duk sanda zasu zauna sai ya kawo zance abokinsa brother shamsuddeen,ba sau daya ba ba biyu ba take nunawa a fuskanta idan ya kawo zancen amma baya ganewa,amma dai yau sai ta fito ta fada masa gaskiyarta game da bro-shamsu.
Abubakar yace "wlh mufy idan da ace zaki fahimci shamsu kamar yadda nayi kuma ki karbi soyayyarsa kamar yadda yake so, da kin yi dacen miji,domin shamsu mutumin kirki ne ko a cikin friends dina bani da tamkarsa kema kin sani but bazan so ayi miki dole ba tunda bakya sonsa shike nan insha Allah na daina miki maganarsa daga yau zan kuma same shi na bashi hakuri nasan zai fahimceni Allah ya kawo miki wani nagari" mufeedah ji tayi gaba ki daya tausayin shamsu da kunyar ya Abubakar a take suka mata diran sauri a zuciya, ta kama hannun ya Abubakar tana cewa"yawwah my-bros,nagode da hakan amma kayi hakuri na rashin accepting soyayyar abokinka da banyi ba bawai ya shamsun ne naki ba No kawai futurelife dina nake hanga a tare dashi saboda hajiyarsu bata da dadi kaga kar a zo ana bata zumunci,yanzu ga matar yaya kamal kai kanka sheda ne na yadda hajiyar ke matsa wa rayuwarta,ni kuma INA son samun peaceful marriage life in my future life" ajiyar zuciya Abubakar ya sauke tare da cewa "OK na fahimce ki my sis bari na tafi masallaci yanzu 1:20pm"
Mummy CE ta fito daga dakinta tana sanye da hijabi da alamar ta idar da sallah kenan,ta kalle su cikin so da kauna tace "dariyar me ake yi ince dai ba zancen mu da mijina ake yi ba?(saboda gidansu gaskiya akwai barkwanci tsakanin yaran da parents dinsu)zo mufeynah ki fada min me kuke cewa da bros din na ki? Cikin murmushe mufeedah tace" A'a mummy ba haka bane wani maganar dabam muke yi na sirri ko bros? Ta juyo tana kallon ya abubakar suka daara gaba dayansu har mummyn, mummy tace "to in tayi wari ai har dakina zanji sirrin nima" Abubakar yace "ai mummy sai dai tayi kamshi" mummy tace"wai Baffah ya maganar aikinkun dai,naji shirui kwana biyu"? Abubakar yace "jiya munyi maganar da shamsun yake cewa Dad dinsa yana nan yana akan hakan Ku dai cigaba da mana addu'ah,insha Allahu za'a dace" mummyn tace"addu'a CE kullum a tsakaninmu Allah yasa albarka a al'amuranmu baki dayanmu" da amiin suka amsa duka, Ya baffa ya tashi zai fita ya juyo ya kalli mufeedah yace"yawwa mymufey ya ma sunan text-book diñ naki? Mufeedah tace "Home economic for ssec"
3:30 pm mufeedah CE zaune a parlor tana karatu ta wayarta sai ji tayi sallamar Bestyn ta(za'eemah) bayan ta wuce dakin mummy ta gayar da ita mummy ta tambaye ta ya gidansu, ta koma gurin mufey suka wuce dakin mufeey,nan a ka fara wata chapter kamar kullum idan aka hadu.
Mufeedah ta dubi za'eemah cikin sigan tsokana tace"ni dai ba zan gaji da fada miki cewaa kina kara kyau da kiba ba besty,ko tunanin abunda ke gabanki ma bakya yi meye sirrin my aminiyas? Suka dara tare da tafawa
Za'eemah tace"sirrin kike son ji to kar ki damu zan koyar dake a gaba amma yanzu abunda yake tafe dani shine Barrister fa ya dameni da zancen alhaji ma'aruf,amma na CE ya bari in same ki mu zanta saura kadan Dana amsa masa da cewaa kin amince,don INA son naga ranar aurenmu yazo a dai-dai ko kuma idan akayi nawa da wata ayi naki amma kowa yazo sai kice ke kaza,haba kawata me tsoron kishiya" suka darah mufeey tace"Hmm! My-eemah, kema kin sani na so hakan amma muna namu ne Allah yana nasa,(kuma nasan shine dai-dai) yau ko na ki ko naso idan Allah yayi mai matar zan aura I can't change it,beside ma kin sani Daddynmu yana aurar da yaransa mata ne daga sun gama candy kuma idan banda ya shamsu duk samarina masu mata ne duk da cewaa halayyar bai zama daya ba amma most of matan zamanin nan masu zafin kishi ne ni kuma al'amarin it really scared me,kawai dai kiyi min addu'ar Allah ya bani miji nagari but batun alh Ma'aruf ki CE masa yayi hakuri ya sami wata" sosai maganarta yayi weak din jikin za'eemah cikin jin tausayin kawarta tace" Allah ya kawo nagari,amma kema mufeey kina da matukar tsurewa akan abu, yanzu ni din ke shedah CE na abubuwan da yake faruwa tsakanina da matar barrister amma wlh ko 'dar bana ji saboda mijinta ke gabana ba ita ba,babu irin warning din da bata cutting min ba amma kullum kara sonsa nake yi kuma shima haka,ki fawwalawa Allah komai insha Allahu anything will be alright, kuma alh. ma'aruf bayi da matsala domin kuwa a cikin dalilan da ya sanya yake son kara aure akwai na rashin zaman lafiyan da basa yi a tsakaninsu duk da cewaa yanzu an raba masu muhalli amma yace baya wata daya a cikin kwanciyar hankali don ko a gurin bikin daginsa suka hadu sai an raba su fada(haba mata)" mufeey tace "ato kinma ji kenan to me zai kai mufeedah irin wannan gidan ai sai dai kaddara, amma no mufeedah bani da jarumtar zama da irin wadannan matan,mu ma bar wannan zancen kawai me ake ciki game da ranar candy dinmu? Ya kamata jibi Monday idan muka hadu a tsaida maganar kawai ayita ta kare kuma ga na bikinku ke da Rash ana candy da 1week NATA ke kuma 3weeks after candy wai! akwai fa dawainiya a gabanmu muna wannan ga wancan amma fa anko kala uku-uku zamu yi na candy kuma bibbiyui ko ya? kika CE ga maganar na candy amma dai shaa ma hadu jibin"

AL'AMARIN KISHI...Where stories live. Discover now