Mutanen india an dawo

347 14 0
                                    

Kaduna state
UNGUWAR SARKI
Gidan alhaji Abdulrahman m. Kanam, ko'iina ka kallah cikin gidan zaka ga ahalin gidan karankatab dinsu cikin hidindimu suke daga ma'aikatan har masu house din, kowa yana iya kokarinsa domin nuna kwazonsa da farin cikinsa na dawowar daya daga cikin yaran gidan da ya tafi karatu tun tsawon shekaru shiddah cir a kasar India sai dai iyayensa ke zuwa duba shi a wasu lokutan kuma jefi-jefi yakan zo yau dai anyi me gaba daya domin ya kare karatunsa na cardiologist (likitan zuciya)
Su Nuraydah iyayen iyawa sai up&down take yi brother zai dawo2,duk tabi ta mammane bango dakinsa da katika masu dauke da kalaman barka da zuwa masu kyau da tsada,murnanta ma ai da biyu CE to mana tunda zauji 2 b din NATA tare da Ameen din suke kuma dama anyi akan tare za'a sha bikinsu Dana Ameen,
Mummynsu kuwa ai fadinma yadda take farin cikin dawowarsa ai bata miyaun bakine domin ko Daddy dake murnar dawowar magajinsa bai kai mummyn ba Abu daya ke sawa take rage zumudin saboda maganarsa da fareedah Wanda ita mummyn she's not supporting the thing, tunda iyayen fareedan dama itan sai a hankali but tunda uban gayyar yace yaji ya kuma gani ai shi kenan itama sai ta Dora da Allah sanya alkhairy kawai
Wannan kenan
5:30 pm dai-dai lokacin an kammala komai saura jiran isowar bakin Wanda a lokacin mummy ta sha gayunta kamar ba itace ta haifi su Al'ameen din ba ta fito cas da itah, zuwa tayi gurin dinning domin dudduba arrangements din da aka yi, domin tabbatar da komai ya zama intact dama su Ameeen da khaleel kusan halayyarsu na son abincin gargajiya yazo daya bare an Dade ba'a hadu ba(da traditional food din FA😁)shi yasa mummyn ta jagoranci tawagan kitchen din ta zauna ta tsantsara musu tuwon shinkafa da miyar taushe (na ma dan leko muku miyar ai readers ga ta nan ma kar ayi Baku☺)
MIYAR TAUSHE
Nama
Kabewa
Busasshen kifi
Yakuwa
Kayan miya(tattasai,tomatoes, albasa da taruhu)
Gyada ta miya
Cray fish
Seasoning/benny
Manja
Daddawa(ra'ayi)
Da farko ta wanke kabewarta kafin ta feraye bawon ta ciccire harzar cikin ta slicing naman kabewar,ta koma kan kifin ta cire kaya dama wasu abubuwa na jiki Mara amfani sannan ta zuba tafasasshen ruwa akai ta ajiye a side, ta gyara kayan miyarta ta markada tare da crayfish da gyadar bayan ta soya sama-sama ta wanke naman ta Dora tare da kabewa(pumpkin) da kayan kamshi da dandano ta bari suka nuna na mintoci5 sannan ta kara ruwa kadan har naman tayi laushi tayi mashing(mussuke)kabewar ta zuba markadaddan gyadarta da ta soya su sama-sama akan kabewar ta motsa ta zuba daddawa ki kara maggi idan bata ji ba,sannan naga ta rage wutar yanaci kasa-kasa zaki iya kara ruwa idan tayi kauri sannan ta zuba gayayyaki da ta wanke ta barsu for 3-4 sai naga ta sauke. (Ba don kar kuce INA kwadayi da nace miyaun bakina sai zillowa yake yi😋) amma dai naga wani hadaddar transparent jug da wani abu a cikin sa kamar zobo sai kuma Dana leka naga zobonne but da yankakkun fruits a cikin sa (oho wai ashe Chapman zobo Sunansa)haka naji Nuraydah ke cewa, wai! wannan shine wai garin dadi...

Din! din!! alamar karar kiran waya naji INA juyowa naga Ashe mummyn CE ke kiran waya aiko tsit nayi domin dauko muku rahoto yadda ta dace
daga jos mummy da mufeey suna hirarsu a parlour kira ya shigo wayar mummyn bayan ta received ta fara da sallama fuskar kowa nensu da murmuashi suka gaisa mummyn kd take fada mata cewar yau fa Dr Al'ameen yana hanyar zuwa 9ja mummyn jos cikin nuna farin ck tace Allah ya dawo da su lfy,Mufeey da raydah ke waya duk ta cikawa mufeey kunne da surutun Dr Muhammad Fawwas dinta zai dawo suna haka raydah taji karar horn nan ta katse wayar tayo hanyar get a 360 aiko su dinne Ameen yana fitowa ta dafe shi kamar wata yar babyn shi kuma sai jin dadi yake yau ga shi ga 'yar sis dinsa ta sauko ta koma gurin Fawwas Wanda shi tun dz idonsa ke akan matarsa sai ayyana abubuwa yake a ransa game da surar raydwas dinsa, itama yadda kuka San idonta zai fado saboda kallon juna da suke .tuni Daddy da Ameen dama wasu dake compound din sun wuce sai masoyan kawai ke nan can kuwa cikin gida mummy sai bin Ameen take da kallo kamar wata sabuwar halittah suka gaisa cike da so da kulawa nan aka zazzauna don cin abinci ai Ameen zobon nan ya fara sha don shi din mutuminsa ne Nuraydah CE tayi serving din kowa dake gurin baka jin komai a gurin sai karan spoons tunda magana idan ana cin abinci bai dace ba,
Dr Muhammad Fawwas ya wuce gidansu ya rage Daddy da Ameen sai su hubayrah da sauran kannen Ameen din shima Ameen mikewa yayi side dinsa hannunsa rike da jacket din saman longslev din dake jikinsa yana cewa "mum-Dad bari na Dan huta pls"
Daddy ya kalli mummy ta kallesa yace "to alhamdulillahi, muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar saura kuma maganar tambayo aurensa kinga sai ya Dade cika cikakken mutum ko khareemah" mummy tace "sosai ma kuwa,amma da zaku ji shawarata da ya nemi wata domin wannan da yake ta dawainiyarnan da ita ba alkhairinsa bane Daddyn sabeer" Dan jimawa yayi kamar baya gurin kafin yace "to reemah idan muka CE zamu yi haka a yanzu kinga mun zama kananan mutane domin kuwa mun San juna tsakaninmu da iyayen yarinyar nan tunda kan maganar nan sau biyu muke zuwa gidansu da su alhaji Buhari, kuma danmu yana son ta duk da bai dace ba a matsayinmu na iyayensa mu kyale shi yayi aure a irin gidan to amma yanzu tsakaninmu da hakan sai addu'a Allah ya tabbatar da hakan idan alkhairi CE ga dukkanmu ya shirye ita yarinyar" "Amiiin" mummy ta amsa.
Nuraydah tana can dakinta manne da waya a kunne a shan soyayya like no 2morrow
7 days later
Su Daddy da friends dinsa suka shirya zuwa unguwar shanu gidansu fareedah domin tsai da ranar auren tunda din Ameen ya dawo, shima uban gayyar kuwa a dokance yake Allah-Allah yake aje a dawo yaji feedback(makaranta duk da cewa ban Baku labarin fareedar a farko ba amma Ku a fahimtarku me zai faru)?
Wani abin takaicin shine duk abinda iyayenta da ita suka shirya na fadawa iyayen Ameen din cewa an mata miji bata bari Ameen din ya gane komai ,dama ya kirata ya fada mata yaufa iyayensa zasu shigo tambayar ranar nuna masa tayi she's so happy with hakan fiye ma da shi. A can kuwa mahaifan fareedah bayan ta sheda musu cewar iyayensa zasu zo,babu kunya bare tuna baya suka saida cewar idan sun zo su CE masu sun Riga sun fidda mata miji saboda sun gaji da jira,
Ita kuwa fareedar har yanzu akwai burbushin son Ameen din ta a zuciyarta kawai dai fantamawar da suke yi ita da iyayenta da ingizarta da friends ke yi yasa take Dan mammance wasu abubuwa game da Halaccin da Al'ameen yai musu kab gidansu amma dake butuluce tana tuna abinda alhaji Shuraihu sai taji ya shafe na Al'ameen din
2:30 yai ma su Daddy a gidan su fareey kasantuwar basu ma da nisa an tarbe da hannu bibbiyu(saboda sahura cewa tayi su bisu a lallama saboda kar su bukaci dukiyan da Dan su ya kaso musu) bayan an gaggaisa alhaji Abbas ya koro dalilin zuwansu, amma wai babu ko kunya daya daga cikin abokan baban fareey din dama mahaifin NATA suka bude baki suke cewa"ai amma fareedar miji saboda dangin babanta daga kauye sun matsanta cewar ayi a mata aure ta yi babba da yawa,wai shine suka hadata da Dan uwanta (kunji 'yan bariki)
A zabure alhaji Zaharadden ya mike yana nuna yatsa ma mahaifin fareedah yace "amma Ku kananan mutane ne,marasa sanin ya kamata idan ba hakan ba zuwan mu yau shine na uku idan kun San hakan me yasa tun farko kuka jajirce kan cewa sai ta kammala karatunta Ashe Ku mayaudara ne" Daddyn da sauran abokansa sai hakuri suke basa nan dai akayi watsewar rashin jin dadi,A gefe kuwa sabuwa sai murna take yi tunda taji har suka tafi bata ji anyi maganar kudin da Ameen yayi speeding ma fareedar ma, sai ta fara zage-zagen karya wai an ai su suka jawo tunda yaron su ke son yarinya amma tayi ta jiransa amma yake ta Jan mata rai shi ya sa dangin babanta suka gaji suka nemo mata miji(borin kunya) ni ko nace dama dai ba Alhaji Shuraihu bane da kinci bulus sai kin koka da idonki, mu dai je zuwa READEARS
J.TOWN
YAU itace ranar graduation partyn su mufeey duk yan set dunsu maza da mata idan ka kallah zaka ga kowa cikin farin ciki da annashuwar wannan ranar barinma group dinsu Za'eemah sunfi kowa haduwa don sun sha gayu sosai barrister ya fito da su domin dukansu shidan nan sanye suke da red-skirt da tee-shirts mai Jan kwala da hannun ta kasan red sai rubutun jikin shin red anyi zanen batch din school din daga gefen rigar sannan ta bayan sunan kowaccensu ne jiki sai head red kar Ku so kuga wayannan baby's din ai hotuna anyi kamar ba gobe sannan ga gift da suka rarrabawa students da ma abokan arziki.
Ranar jumma'ah mufeey CE zaune saman gadon dakinta tana charting da Nuraydah Suna Gama chatting, tana shiga wani group a WhatsApp sai ga messages audio da hotunan wani Dan shekara da bai fi 2 ba tare da bayanin cewar kishiyar Babarsace wai ta tsastsaga masa jiki da reza(ni ko nace ko me wannan Dan tayin yayi)? AI Kuwa cikin kankanin lokaci har hawaye ya wanke fuskar Mufeedah a dai-dai lokacin Hunaydah DA Za'eemah Suka Doka sallamah a kofar dakin amma Bata iya dagowa ta kallesu ba duk DA ta amsa idanuwanta akan wayar dake hannunta.
Zaraf, Hunaydah ta fisge wayar domin ganin abinda ya saka friend dinta zubar hawaye Tana gani ta Mika MA Za'eemah tare da cewa "duba ki gani eemah, Kai! Allah Ya shiryi wadansu mata Duba Dan Allah wannan yaron Meye laifinsa wai Don kawai Allah ya halicce sa a da namiji shine wai Kishiyar mahaifiyarsa ta yayyanke masa jiki da Reza saboda Nata 'ya'yan Matane ji jahila" tsaki Za'eemah ta ja Kafin ta Dora DA cewa " Allah shi kyauta,idan banda macuciya kin Kori Uwarsa a gidan(best on sauraran Audion)to shi me ya tsare miki haba Mata kishi haukane? Why women why? Muka cikah son zuciyane" Mufeedah tace "bayan ta sauke ajiyar zuciya Nifa ire-iren abinda ke dada tsoratar Dani kenan a auren mijin wata, domin Idan kika Sami muguwa Idan ta nufi illatarki ta kasa sai ta illata miki jininki.Allah ka sa Mufi karfin zukatanmu" DA Amiiiin Suka amsa all tana shirin Rufe data messages Suka shigo photos din Anty Fateemah ce DA mijintah DA yaranta na Barka DA jumma'a Don dama takan turo MA Mufeedah nan FA aka koma kowa na fadin albarkacin bakinsa akan rayuwar auren Antyn nasu Suna Mai Addu'ar Allah ya basu irinta.
Hira ta koma kan bikin Za'eemah dake gabatowa

AL'AMARIN KISHI...Where stories live. Discover now