KISHI KUMALLON MATA.. 😍😅😫

434 14 3
                                    

Gidan Alhaji Shurayhu🏠
Cikin parlour Wasu Mata NE su biyu zaune Suna kallon tashar Startimes(chanal din dadin kowa) Shamsiyya ta dubi Dayan MATAR tace "maman kamal, ni dai wannan rawan Kan nan da Abbah ke Yi akan auren nan damuna yake Yi, amma ke ko a jikinki" Wanda aka Kira da maman bilal ta Kalli Shamsiyya tace"HMmm! Shamsiyya kenan to ko yana Damuna na Isa hanawa NE?abinda ba yau na Saba gani ba ai shi Alhaji aduk lokacin da zai Kara aure Haka dabi'arsa take,amma abinda yasah kike damuwa ke saboda tunda ya auro ki bai Yi wani auren ba sai wannan Karon shi yasah kike Kallon shi a sabon Abu"
Shamsiyya cikin Jin Zafi a ranta tace"Cab! Lallai kam a ganshe ki ni dai kam bazan dauki wannan rainin wayon nasa ba,mace ce kamata zai auro bata fini da komai ba ehe😏" Dariya maman bilal ta kyalkyala Kafin tace"Allah Sarki ta yaro Kyau take bata karko, in banda abinki waya fada Miki Cewar hargagi yana tsai da rawan kan namiji Idan ya tashi Kara aure?ai abinda hakuri bai Bayar ba rashinsa Ma bazai Bayar ba bare Alhaji Fa mutum ne Mai 'dokin Sabon abu,domin Haka ina shawartarki da kiyi hakuri mu jure komai sai kiga har yazo ya wuce bamu San Ana Yi ba koda ya miki ciwo ki daure zai wuce" zunbura baki Shamsiyya tayi a zuciyarta Kuwa Tana fadin wannan wace irin zuciyace da ita Bata kishin mijintah)
Shamsiyyar tace "amma maman kamal kina kallon rashin adalcinsa karara ko tun Kafin tazo, yaushe Rabon mutumin nan da dawowa gida da wuri?tun Fa da aka saka Ranar bikin nan wa ya sani Ma ko tare suke wuni da ita a kasuwar,nifa wallahi bazai kawo mana 'yar duniya ba tazo Tana min kallon banza ba in kyaleta ba sai dai mu goga juna" ciki k'uluwa MAMAN bilal ta dube ta tace 😏 "ai sai kiyi kuma shi dai ba fasawa zai Yi ba,kin ga kuwa kece da cutuwa shi Kuwa ko a jikinsa, kuma yadda kike daddaurE masa fuska ai ke kike korarsa, kuma zan Kira Inna in sanar da ita duk haukar da kike Yi, kuma bazan gaji da baki shawara ba kamar yadda Na alkarwanta ma innah"(kunji fa Mata kishiyace Fa take damuwa da kishiyarta kamar 'yar u wanta, abangaren Shamsiyya Ma Hakance domin aduk aure-auren da Alhajin yake Yi Shamsiyyar ce ta zauna da ita lafiya)
Shamsiyyar na jin cewa za'a fada ma innarta ta nemi nutsuwarta ta dawo dashi amma fa kishin nan yana nan,
Wani tadin suka koma.
4:30pm
Matan gidan NE Suke zaune a tsakar gida sun dau wankansu tsab dasu. can gefe yaran gidan NE ke wasanninsu, a dai-dai wannan lokacin NE suka tsinkayi sallamah daga waje Shamsiyya ta dubi yaran tace "wai ku bakwa jin ana sallamah NE? Babban cikinsu ya sukwano a guje ya tafi Dubowa tare suka shigo da yaron da Usman(yaron Shagon Alhajin NE) dauke yake da akwatuna iri daya babbah da karami ya dire a gaban Shamsiyya domin lokacin maman Kamal ta tafi kitchen dubo Girkin da take Yi.
Ashe tare suke da Alhajin aiko Shamsiyya Daure fuskarta tayi tamau ta masa Barka da dawowa, Alhajin yace "ina 'yar uwakki? ta Mike ta nufi kitchen ba tare da ta bashi amsa ba, shi Kuwa Binta yayi da kallo take ya ji wata.....Shamsiyyar(domin tana Kai shi wata duniya a duk lokacin ya kasance tare da ita) da Yi ma maman Kamal 'din "sannu da aiki, sannan tace "Abba ya dawo Fa, Yana Kira" tare suka fito maman Kamal da cup ita kuma Tana dauke da jug, Gaida shi maman kamal tayi sannan ta Sami kan dayar kujerar ta zauna duka Suna zazzaune
Alhajin yayi gyaran murya sannan ya Fara da fadin "Kamar yadda Na sanar da kune Abaya Cewar zan Kara muku abokyar zamah,
Lokaci yana matsowa shi yassa NAke so inji ko kuna DA bukatar Wasu abubuwan domin shirye-shiryen ku, GA akwatuna nan ke zulai ki dau NA saman(karamar)ke kuma Shamsiyya ki dauki NA Kasan sai yara kuma gobe sa'eed zai zo ya gwadasu(dinkuna)amma fa ku  sassauto da bukatunku Don bani da kudi"
H.Zulai tace "muna godiya Allah ya sa ayi lfy MU zauna lfy"
Cikin jin Dadi Alhajin ya dubeta sannan ya Amsa da "Amiiiin" aransa Kuwa yana Mai jin dadin yadda a kullum take bashi support  Idan ya tashi Kara aure DA hakurkurun DA take Yi a zamantakewar su da Matan DA YAKE aurowa a baya,domin a Wasu lokutan MA sai ana Saura kwanaki YAKE gaya MATA amma haka take jurewa sai dai tayi irin Addu'ar DA a kullum take masa yayi aure-aure a baya ya kuma walakantata amma haka take jurewa(gashi yanzu ta Fara cin nasarar hakurinta)
Shamsiyya Kuwa godiya Kawai tayi ta wuce Ita a dole kishi nan FA yana nukurkusarta(alh Kuwa Binta yayi da idon Don shigarta ta Kusa sanyashi..!Don dama a duk aure-auren sa bai Taba auro ya ita ba Don a cewarsa Ta Iya gado 🙈 gata yarinya karama) wai Ashe FA fankam-fankam ba shine Kilishi ba,
H. Zulai Kuwa ta Fada Duniyar tunanin yadda zamansu DA fareedah zai kaya tunda labari yana zuwa musu daga yaran shagon Alhajin cewa fareedah FA Gogaggiyace ga Boko ta zauna,(tsoron ta da Addu'ar ta irin wahalhalun DA Tasha a baya kada Allah ya karah jarabtanta dasu) ta Mike ta biyo Shamsiyya har dakinta ta Same ta Tana kuka
Ta kamo hannunta ta zaunar DA ita tace "haba Shamsiyya wannan kukan me zata magance miki,kawai kizo MU zauna mu tsara abinda zata fisshe MU domin tunda har Allah ya sa Alhajin ya Fara tsaituwa to kar muyi wasa DA damarmu yanzu tunda ke dama kin Iya dinki ni kuma NA iya hada sweater DA kayan Sanyi sai muyi magana Alhajin ya sayo mana mashinan dinki DA tsakar Don zama bashi yuwuwa babu sana'a,kuma ina Kara Jan hankalinki daki saukaka kishin nan sai ya wahalar dake kawai a banza.
JOS PLATEAU STATE
Mufeedah ce zaune a parlour Suna chatting DA anty fateemah
Anty Fateee "my sis ya batun kanin nawa NE(shamsudden)?
Mufeedah "ANTY ai an Riga an wuce nan, bro Baffa ya Riga da ya fahimtar dashi kuma yama  Hakura yanzu "
Anty fateemah "amma Sis DA baki hakuri da shamsun ba kawai tunda ba tare Zaki zauna DA hajiyar ba, Da kin yarda dashi ko Don faranta ransu Mummyn"
Mufeedah "anty ku dai rinka Yi min Addu'ar Allah ya kawo min Miji nagari kawai"
ANTY fateemah "😥 cikin tausayawa tace  Muna tayi kullum mufeey ta Allah ya kawo muje mu kwashi shoki 💃
Dukansu sukai dariya
Anty fateemah "kuna Gama bikin Za'eemah ki tattaro kizo mana Don su esham sunyi missing dinki, ko da shike MA daga kadunah gurin bikin Raydah kawai sai mu wuce Gombe kawai Musha zamanmu,goodnight sis GA Barrister ya shigo"
Mufeedah "OK sweet dreams my sis"
Ta ajiye waya ta shiga bayi domin dauro alwala, Tana fitowa taji karar shigowar message(whatsapp)
Raydah ce
Raydah hi! Sis
Mufeey "Amarya 2b"
Nuraydah "mufeey wai baki ji me ya Sami brother Ameen bane ba?
Mufeedah "lnnalillahi,me ya same shi?
Nuraydah "duba dp Na kiga wani Abu"
Mufeedah 🙄"kamar brother Ameen,amma wannan da alamar majinyacine,bar zacen Dp ke dai sanar Dani me ya sami myblood?
Nuraydah "ai abinda ya same shi yanada nasaba da dpn,a Haka mah ya Fara recovering kenan,ai wlh Allah  sai nuna Ma fareedah karshen ta tun Anan duniya,fareeedah DA iyayenta sune silar mayar min da Dan Uwana  haka saboda abin duniya wai sun Mata miji"
Mufeedah "Hasbunallahu wani'imall wakil, amma wadannan mutanen nan  basu da kirki yanzu sai daya sha wahala da ita ya maidata mutum shine zasu mana tukuici da Butulci?to Allah ya basa hakuri ya sa hakan shine mafi alkhairi,domin ni dama tun farko wannan fareedar tasa ba taimin ba ta Cika raina mutane,basu dace ba dama domin shi humble NE ita kuma Mai jida kanta Allah  mantar dashi ita"
Nuraydah "Amiiiin, a gaidah min dukkan mutanen gidan tare da kawata eemah"
Mufeedah "OK duk zasu ji my regards to mummy daddy and everyone in the house"

5:50am
Za'eemah dake kwance taji wayar ta Yana Kara,ta dauka tare da duba numbern taga unknown number,tayi received tare da sallamah sannan ta saka a 🔊
a dayan side din Ba'a amsa sallamar ba aka Fara maganganu cikin fada-fada"Ba sallamarki nake son ji ba uxtaziya, gargadi nake son miki akan ki Rufa MA rayuwarki asiri ki Fita a harkar mijina tun kafin kizo KINA DA kin Sani. Idan Kunne Yaji....! Kib aka kashe wayar
Zainab dake gefen Za'eemah Wanda ta Farka tun a farkon Fara wayar ce ta Fara kuka Tana fadin wannan wace irin matace wai Akanta aka Fara kishiyace da zatake damun mutane duk yaufa Saura kwanaki NE ya rage kije ki isketa(auren)ta saduda mana😕
Duk DA Sanyin DA jikin Za'eemah yayi hakan bai sanyata nuna Ma zainab gazawarta ba. Cikin Dakiya ta Dubi Zainab din tace "haba sis sai Kace ba fulanin ba,ai Idan na nuna Mata barazanarta yana tsoratani zata dauka ta Sami yadda take sone kawai abinda a kullum Nake so dake ki Rufe min wannan Sirrin Kar ki Bari kowa ya San abinda take min hatta DA anty Nana Kada ki Sake taji"
Zainab tace "A'a anty a gaskiya ni Na gaji DA wannan ajiyar,gara NA sanar dasu mama Asan matakin daukawa Don wllh a labarin da aka bani na wannan Matar ya wuce yadda ni dake Muke dauka wannan Abu DA suke ta gargadi FA ba barazanace ba Haka NE domin akwai waata kawarsu DA akace a ranar DA mijinta ya kara aure a ranar Amaryan ta Kamu DA cutan barin jiki har Ta mutu Don Haka ki kyale mata mijintah domin ba shine autan mazajen Duniyar nan ba"😏
Za'eemah tace "ke dai ki Tayani da Addu'ar 'yar uwata ke shaidace Na yadda ni DA barrister Muke son juna,ta ina zan Fara cewa Mu rabu da shi bayan bazan iyaba muddin a hayyacina nake I can't  do without myzameed"
Zainab tace "to ko wllh sai dai ki zabi daya ko dai na  fadawa masu maman ko kumah in sanarma Yaya Hameed din amma bazan Yi shurui DA cuta ba kam"
Za'eemah tace "eh Naji amma a gaba ba yanzu ba,yanzun dai tashi MU wuce kitchen yau mun makara gurin breakfast"
Nan dai suka wuce kitchen Suna aikace-aikacensu Suna hirarrakinsu har suka kammala, nan DA nan  gidan ya dau kamshi Don Za'eemah FA gwanace gurin sarrafa girki(mata sai mu jajirce,don Kuwa Sirrin Mallakar miji  a shika-shikanta akwai Iya Girki ko bature ya San hakan domin yayi Karin maganar🍝)

9:oclock am
Barrister ke rike DA waya tun 7 YAKE kiran Za'eemah Ba'a dagawa yanzu MA gashi yana ta ringing Ba'a dagawa still,(ya Fara tunanin ko dai wani abinne ya sami Noor din nasa)sai yanzu MA tunanin Kira number Zainab ya zo masa
A dai-dai  lokacin Za'eemah ta shiga wanka Zainab cikin jin dadin tashin Za'eemah a gurin tayi receiving call din,suka gaisa
Barrister Yace "ina wifey NA take?
Zainab tace"gani"
Cikin barkwanci yace" original din Fa?
Zainab tace" ta shiga wanka"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin Alhamdulillah
Zainab tace "yawwa yaya Hameed akwai maganar DA nake bukatar muyi ni Da kai Kar ka Bari anty eemah taji"
Barrister Hameed yace "ina jinki madam"
Zainab tace"yaya akwai gagarumar matsalah Fa da ke shirin zama silar shiga tsakaninka da anty eemah(nan dai ta kwashe tun daga farkon abin har na yanzu ta fada masa da gargadin da Za'eemah ke Mata a tun farkon abin)a take Yaji wata zazzafar qaunar Noor(Za'eemah)ta sake Kama ransa Allah Sarki true love kenan in ba Haka ba duk wadannan gargadin)
Barrister Hameed yace "to yanzu Abinda nake so Dake shine kada ki fadama su maman amma ki fadama anty Nanan(zan MA kirata za muyi maganar)ni kuma zanji da ita Mai gayyar"
Barrister ya koma side din message ya Fara ma Za'eemah zafafan Kalamai NA sanyaya zuciya
Haba mynoor ina kike NE? sanyin idanuna Haskeenah, NA kiraki ba adadi baki dauka ba har hakan ya tsoratani yanzun Haka ma ina asibitin masoya domin zazzabin rashin Jin muryarki ya kamani,nasan duk abinda Zasu bani  ko yayi min a asibitin ba zai kawo mafita ba dole sai Kin zo da kanki Domin kece kwararriyar likitata, love you my queen l hope you are doing well and good 😘(hmm wadannan abubuwan sune suke matukar yin tasiri gurin dada rura wutar qaunar Barrister a zuciyar Za'eemah domin Idan Yana tare da ita komawa yake Yi Dan 30yrs)

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 22, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AL'AMARIN KISHI...Where stories live. Discover now