Zabin Allah 😍

224 7 1
                                    

💘             💘                  💘
KADUNA garin gwabna
Kwance YAKE amma ba barci YAKE ba but idonsa a Rufe domin tun jiya DA Daddy Ya sanar masa yadda Suka yi DA parents din Fareey ya kasa samun nutsuwa,
Duk DA cewa Mummyn Da Daddyn sun Mai Kalamai Mai sanyaya zuciya,amma FA DA kamar wuya fitar Soyayyar Fareey a zuciyarsa farat daya Abu NE mawuyaci, kusan Idan zai iya tunawa Fareey ce first lover Dinsa a rayuwarsa domin bai cikah kula harkar Soyayyah ba a baya kafin haduwarshi DA ita, Kumah Yayi trying contact dinta DA safiyar nan baya shiga duk DA cewa Tun Jiyan YAKE yin hakan 😥
Flash back

Yammacin yau garin KADUNA an wuni NE cikin yanayina Sanyi-sanyi Don Haka garin tayi dadi GA mazauna cikinta su Ameen Suna packer  motorcycle dinsu a kofar gidan abokin nasu yayin DA fareedah suka fito Don tafiya Mariya kanwar sa'id kumah kawa GA su fareedah take musu rakiya ta tsaya sukayi gaisuwa DA abokan brother ta Anan NE fa Allah ya Yi ikonsa domin Ameeen kallonsa yana GA fareedah yaji gaba daya ta mishi har a ransa itama dai DA Alamar ta kyassa tun DA ya kamata Tana kallonsa a hakan dai ya Bari suka wuce bai furta ba, bayan sun shigo dakin sa'eed NE ana fira sai Ameen YAKE tambayarsa ko ya Waye ta shi dai FA ga  Matar aure, sa'eed DA fawwas me za sui in ba tsokanarsa ba cos shi din Fa a tun tashinsu baya DA wata budurwa Don har  tsonarsa suke wai ko aljanace ta aure shi sa'eed yace sai dai FA ka Kira Mariya Kaji daga gareta Donni ban cikah shiga harkar WA'yannan yaran ba.
To fa Hakan akai Kafin Ameen ya bar gidansu sa'eed sai DA yaji komai game DA fareedar daga gurin Mariya har DA karban contact dinta, yana komawa gida ya kirata ya Yi bayanin Kansa daga nan Suka Zanta
kan kace me Wata kakkarfan soyayyace ta shiga tsakanin Ameen  DA Fareey duk DA mahaifiyarta Bata so don ita a tsarinta ya'yanta sai masu kudi, amma dake Fareey na sonsa sai take ta kakkare shi domin so DA dama Idan yazo bayan ya tafi sabuwar takan tambayeta Me ya kawo ko tace kinga irinta ai da wani ne da munga abin arziki  amma kin likewa Wanda ko abinda zai Baki baya dashi,ita kumah Fareey DA Wani lokacin koda Ameeen din ya Bayar a ganinta kankantar abin ke hanata nunawa  Idan zata kwatanta Dana sauran DA kumah Gudun kushensu sabuwar DA kawartah zabba'u domin Tana da Samari da suke kashe Mata kudi duk da kankantarta Don a lokacin(she is just 16) Shima Ameen  Wata ran yakan Yi mamakin budewar idon Nata amma sai ya aje hakan akan wayewace kawai(so kenan), wata rana Ameeen yazo Suna cikin zancensu sai ga kawartah zabba'u Tana zuwa suka gaisa ta kare mai kallo a sace aranta tace Ashe Fa ba a banza ba kawartah mayance ma Wannan guy din ba, duk da dai ba za'a ce masa kyakkyawa ba a ganin farko amma yana da zatin halitta musamman kwayar idonsa gasu manya kumah ga  kasumbarsa Mai daukan hankali, kumah a lokacin Sanye yake cikin wata yadi mai kalar navy blue da black cover shoe , kayan yayi masa kyau Don har Nuraydah tana tsokanarsa da cewa yau kam brother niyyar Mallake auntynah Kai   wannan irin gayu haka, yace na nawa kumah Yana Dariya ya wuce, tofa ga alamar itama zabby ta Fada.
Anan dai Ameen  ya  yanke Cewar zai Mai DA ita makaranta domin shekaru biyu kenan  DA barinta tun lokacin DA suka Kai js3 zasu Rubuta jsce kumah babu kudin, shi kenan ta sallame sai dai Idan Samari suka bata kudi sabuwa ta lallaba ta su cinye ko da ta nuna cewa Tana son Tarawa domin komawa makaranta sai ta nuna Mata cewa Kar ta Damu Idan Allah  ya bata miji Mai kudi zai maida ita(wai ai yanzu zamani ya hutar DA iyaye Samari Ne zasu ke daukan Resposibilities din yarinyar da suke so, ni ko nace Anya ba tunanin sabuwa bace ba kawai?)  A haka dai Ameeen  yake ta dawainiya Dasu fareedah dai-dai  karfinsa amma sabuwa a kullum Tana rainawa zabba'u Tana dada zugata akan Ameen har dai lokacin Rubuta ssce yayi Fareey ta Rubuta. albarkacin pharmacy DA Daddy Ya bude ma Ameeen din da shine dai YAKE ta dawainiya da ita domin akwai lokacin da yayi Requesting kudi gurin Daddyn kan Cewar zai Yi ma fareedah register zata Fara zuwa kadpoly, Anan ne Daddy Yasan DA maganar wata fareedah amma da Daddyn Ya nuna Masa yana so zasu je da abokansa suga juna da iyayen fareedah sai Ameen ya nuna shifa ba yanzu ba tukunnah karatu YAKE so itama kumah zata sami Damar yin nata.
Tun lokacin da Ameen  din ya Kai Nuraydah gidansu Fareedah bayan ta dawo take baiwa Mummyn labarin cewar gidansu Fa basu da tarbiyah.
tun a lokacin Mummyn taso Hana Ameen  amma ya nuna Mata shifa sai fareedah hakan yasah ta kyale shi, Ahaka yake ta dawainiya da ita Dan ko da ya tafi karatun Ma yana tura mata sako don ya bude mata account tun lokacin da zai tafi karatu a Indian, 
Ahaka har fareedah ta Fara zuwa kadpoly a lokacin Samari iri-iri ke gareta manyan maza DA Matasa,ganin Haka yasah mahaifiyarta hure mata Kunne kan cewa tayi kokari ta Tara abin duniya Kafin lokacin da zata Rasa wannan Damar, domin yanzu NE kasuwarta ke ci. da labari ya sami Al'ameen din kan Cewa fareedah ta bude rayuwa ta Tara samari ya Kirata yana mita karyatawa tayi Tama nuna Masa ita Fa daga  gida sai makaranta, bata zuwa ko ina.Nan suka koma dai-dai  Hmm! Mace kenan😥 Cewar Ameeen
A Haka sai DA Ameen din ya Kai 2 days yana zazzabin Rasa fareedah 

Mummyn tayi lallashi Daddynma yayi yanzu Nuraydah ce ke fagen lallasarsa kumah Ya Ma Dan samu lafawar damuwar
Karfe 10:pm a lokacin Daddy da Mummyn Suna parlour  Suna kallon news Suna kumah firarsu  mummy ta dubi  Daddy dake enjoying ruwan Lipton Dinsa Wanda Tasha kayan kamshi(na'a Na'am, citta,kaninfari,Kimba, masoro,lemon Gras etc,)har wani lum-lumshe Ido YAKE.saboda dadin shayin
Mummy Tace"Daddyn Nur, dama wata maganace dani kan halin da Ameeen ke ciki har yanzu ya  kasa sakin Ransa,shine nake son neman Hadin kanka ciki,       Ina sone dama in hada Ameeen din aure da 'yar uwarsa Mufeedah,shin ya ka gani?
Daddy Kuwa da jin hakan ya karah ma teansa Dadi, ya Dubi Mummyn yace tabbas Kinzo da magana kuma daga Ameeen  har Mufeedah na Sani babu Mai kin bin ummarninmu amma bari zanji daga 'Dan uwana tukunnah, Allah ya muku albarka dukanku"
cikin jin dadin Addu'ar Daddyn a gare su da kumah karban maganarta da Daddyn yayi ta amsa DA cewa "Amiiiin"ta dauki cup din da Yasha Lipton 🍵 din ta Fita dashi kitchen sannan ta Leka dakin Ameeen din domin duba yadda yake,Kuwa kwance ta Gansa yayi kamar Mai bacci amma ba baccin yake yi ba, cikin tausayin 'danta na Butulcin da fareedah da iyayenta su kayi masa tace"Ameeen  kayi tawakkali na Sani yaudara abace Mai ciwo ga Wanda akayi masa amma Idan yayi dauriya sai ya mance,wannan jurewar da zaka yi itace tawakkalin Wanda kumah dabi'ace ta mutanen kirki,fareedah Bata cutar da Kai ba kantah ta cutar saboda Haka ka fawwalawa Allah komai sai ka ga ya musalta maka da wacce tafi ta alkhairi  kayi hakuri Kai namiji ne kumah Kafi mu sanin illar saka damuwa a rai"
Al'ameeen ji yay zuciyarsa ta sassauto daga damuwar da take ciki,ya dubi Mummyn yace"insha Allahu  zan Yi hakan sai dai zai Yi wahala ne Mummy in mance komai a lokaci kankani irin hakan mun shaku da fareedah,sai dai kuyi ta Taimakamin da Addu'a kan Allah ya mantar Dani ita a rayuwana😢"
mummy tace"addu'a kullum Yinta Muke,kuma Insha Allahu wata ran Idan aka ambaci sunanta ma a indah kake sai kayi tunani Mai zurfi kafin ka gane wacece Ma hakan,sannan ni yanzu burina in ganka cikin kwanciyar hankali da walwalarka fiye Ma da baya, hakan zai sai Muma mu samu kwanciiyar hankali"
Al'ameeen ya Dago ya dubi Mummyn yana Mai kudurta mance fareedah Aransa, saboda ya Lura tun daga Ranar da ya Fara shiga damuwa walwalar gidansu ta ragu Donma Daddy Ya Na ta maza) yace"Mummy ku gafarce ni halin Dana saka ku,nima ba Ason Raina bane"
Mummy ta dago itama Idonta taf da hawaye tace"babu komai, wannan soyayyace da Allah ya hada tsakanninmu da ku,Allah dai ya mana jagoranci kan Al'amurorinmu"
"Amiiiin" Nuraydah da tun shigowar Mummyn itama ta shigo ta amsa, cikin nuna jin zafin 😕😓abinda fareedah tayi Ma 'Dan uwanta tace"Ni da ba Don Gudun zuciyarku ba da har gidansu zanje in musu rashin mutunci daga ita har iyayennata masu son abin duniya, ai Gara dama Allah ya bayyanata tun yanzu Kar wata ran sai ka aureta ta kashe mana Kai saboda kwadayin abin duniya,yanzu damuwata ka mance da wannan mayaudariyar ka nemi nutsassiya ka aura kumah muna nan Daku sai kunji yadda rayuwar auren ta da alh. Shurayhun zai kasance marrar rabo kawai😏"
Ficewa Mummyn tayi bayan sun masa sai da safe, cike da Kwarin guiwa kan kudirinta na hadin Aure tsakanin Mufeedah DA Ameeen din taje ta kwantar.
A can gidan su fareedah Kuwa shirye-shiryensu suke tayi duk da cewar fareedah takan yi tunanin Ameeen din a ranta da  'dan jin cewa basu kyauta masa ba amma  zugar da sabuwar ke mata ita dasu zabby yana tatsiri aranta.
Gidan alhj  Shurayhun

AL'AMARIN KISHI...Where stories live. Discover now