*Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*Dedicated to *My Lovelly Momy*
*96-100*
*KARE GIDA DA ALQUR'ANI DA ZIKIRAI DA SALLAH: Yana Daga Cikin Abinda Ke Taimakawa Wajen Tarbiyyantar da Yara Shine tsare Gidan Ta Hanyar Yawan Karatun Alqur'ani da Zakirai Musammam Zikiran Safe da Yamma Da Kuma Yin Sallolin Nafila a Cikin Gidan.
Sabir kuwa a jin muryar da take magana da ita yasa nan da nan tsigar jikin sa ta mike.
Idon sa ya kada yai ja, lumshe ido yayi ya bude, ya ce,
"In in jiya da wa na ganki?"Yayi tambayar ba tare da yasan lokacin da ta fito ba.
Kallon sa tayi ta ga ya canja amman bata kawo komai ba. Dan haka ta ce,
"Ni da Yayanah ne!"Kai ya gyada kawai ya dauki waya yana dane dane.
Kallon sa tayi ta kuma narke murya ta ce,
"Naje?"Kallon ta ya tsaya yi, kafin ya ce,
"Kunyi waya da Maryam!"Kai itama kawai ta gyada masa. A zahirin gaskiya baya son ta tafi ta bar shi amman dole ta tafi.
Dan haka ya dinga mata tambayoyi. Sannan ya bata izinin tafiya.
Tana tashi ya bita da kallo har ta fita ta rufo kofar idon sa na kan ta.
Ido ya lumshe, yana me dafe zuciyar sa.
Tana komawa ta bawa Zainab labarin abinda ya faru da yadda suka hadu jiya.
Zainab dariya tayi ta ce,
"Wai ke baki gane wani abu ba."Asma'u ta ce,
"Me zan gane me ya faru?"Dariya kawai Zainab tayi ta ce,
"Allah bazan fada miki ba. In kin gano ka zo kiban labari."Share maganar Asma'u tayi dan ta san Zainab akwai jan rai an kana son abu.
Daga haka suka zauna aka shiga wani lecture din.
Karfe hudu dai dai Yaa Aslam yazo, kiran Asma'u yayi bata dauka ba. Yasan tana massalaci. Dan haka ya fito ya zauna daga kasan bishiya.
Yana zaune ya hango Sir Sabir ya taho a cikin motar sa.
Kallon ssa yayi ya dan saki tsaki sannan ya dauke idon sa. Ya rasa dalili shi dai kawai gayen bai masa ba.
Shima kuma ta bangaren Sir din ya ganshi sai dai shi a duk sanda suka hadu sai yaji wata faduwar gaba
Yana zaune a haka Munasha ta gano shi. Gunsa ta nufa tana canja salon takun ta.
A hankali ta karasa gun tai masa sallama. Dagowa yayi ya na kallon ta daga sama zuwa kasa.
Ita kuma sai gyara tsayuwa take. Baki ya yamutse, kamar yaga kashi ya dauke kai.
Wani iri taji amman duk da haka ta dake ta ce,
"Sannu fa!""Yauwah!"
Ya fada kamar bai san wanda yai maganar ba dan kansa yana can kallon gefe.Zatai magana kenan ya daga mata hannu. Sannan ya mike ya tsaya a gaban ta.
"Me kike nema ne?"
Ya tambaye ta yana juya mata baya,Kallon sa ta tsaya yi tana hadiyar yawu.
"Wallahi sai na dan dani zumar gayen nn."Ta fada a ranta. Tana kallon sa hadi da hadiyar yawu sai kace ta ga nama.

YOU ARE READING
Rayuwar Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔
FantasyLabari akan wata yarinya Asma'u wacce take shiga wani yanayi akan soyayya. Sun shaku sosai da Yayan ta amman daga baya ya barta. Komene dalili? Oho muje ciki dan jin shin tana auren sa ko kuwa.