Page 11-15 Auren Yaa Aslam da Pretty

322 19 0
                                    

*LABARIN RAYUWAR*
     *Asma'u Husnah*

*part 2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*Last page nayi mistaking wajen page number zan sa 6-10 na saka 11-15 ayi hakuri wannan shine 11-15 wancan 6-10 ne nagode*

MASOYA MASU BIBIYAR WANNANN LABARIN NAGODE KWARAI DA GASKE. ALLAH BAR ZUMUNCI. COMMENT DIN KU NA DADA MIN KWARIN GWIWA NAGODE.

*11-15*

Kuka ta kuma fashewa da shi ta ce,
"Meyasa? meyasa? Meyasa yaa Aslam? Me nayi maka da na cancanci haka."

Ta kuma fashe wa da kuka dan har numfashi ta na sarkewa.

Mami ce ta fito ta tadda ta a hankalin da take ciki.

Da sauri ta karassa gun ta. Ina har numfashin ta ya dauke

Da sauri Mami ta kira suka tafi da Asma'u asibiti.

Aslam kuwa ana can yau daurin aure. Duk da yau take ranar farin ciki a gunsa amman sai akasin haka.

Dan damuwa sosai ya shiga na tinawa da tini da Asma'u ake daura auren nasu.

Duk yadda yaso yai farin ciki ya kasa. Abokan sa kuwa dayawa duk basu je daurin auren ba dan ya riga ya koya musu son Amsa'u.

Dukkan su mamaki suke sosai. Wasu kuma haushin Pretty suke ji.

Wasu daga cikin abokan sa su suka hallaci daurin auren.

Bayan an gama reception ya koma gida ne ya kwanta a daki.

Ba abinda yake gani sai Asma'u da ke masa murmushi.

Ido ya lumshe, ya rasa me yake damun sa.

Gani yake kamar a mafarki wai ya auri Pretty. Mamaki yake sosai amman kuma sai wani abu ya dauke hankalin sa daga wannan.

Haka da dare aka kai amarya gidan ta. Dan Mami ta ce bazai saka kowa a gidan da ya gina dan Asma'u ba.

Wani daga cikin gidan shi yasa aka gyara akai wa Pretty kafin kayan ta.

Amarya kamar ba amarya ba dan mayafi ma a kafada ta yafa aka raka ta gidan ta.

Aslam kuwa lokacin yana gida a kwance ya rasa me zai yi.

Mami da kanta taje ta same shi a daki.

Duk da ganin yanayin da yake ya bata tausayi amman hakan bai sa ta ce,
"Ka tashi ka tafi gidan ka. Ga amaryar ka can an kai maka ita."

Shiru yayi kamar bazai yi magana ba. Sai kuma ya sauko daga kan gadon ya durkusa a gaban ta ya ce,
"Momy dan Allah ki yafe min. Momy wallahi ban san abinda yake damu na ba."

Kai Momy ta dauke, Kuka ya saka yana nema yafiyar Momy.

Kallon sa tayi ta tausaya masa ta ce,
"Ba komai kaje Allah bada zaman lafiya. Amman har ga Allah bana son auren nan naka."

Kin sakin ta tayi sai da Momy ta daga sa tace,
"Kaje ka shirya dare nayi."

Mikewa yayi ya shiga bandaki. Ya fito ya shirya cikin sky blue din shadda. Yayi masifar kyau.

Wanka da turare yayi sannan ya fita falo.

Momy bata nan dan haka yayi bangaren ta. Ko da ya taba kofar a rufe take.

Dan haka ya juya ya fice, motar sa ya dauka ya fice daga gidan.

Gidan shi ya wuce kai tsaya. Gidan ne babba wanda yake dauke da babban falo sai kofa da take kallon gabas ita ce in an bude za a shiga bangaren Pretty, Da katon falo sai bed room guda biyu da kitchen da bandaki.

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now