*LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*Dedicated to *My lovelly Mum*
*31-35*
*Ba abinda zzan ce da masoya karanta littafai na sai godiya mai tarin yawa.*
*A gaskiya ina alfahari da ku. Allah ubangiji ya bar zumunci. Ina kaunar ku saboda Allah*Zama yayi shima yai murmushin kawai.
Mami ce ta sauko. Hira suka dan taba sannan yai masu sallama ya tafi.
Zuciyar fal da tunanin Asma'u. Yana kaunar Asma'u son Asma'u yai masa wani irin kamu.
Asma'u kuwa tana shiga daki ta fada kan gado.
Ido ta lumshe ba wanda ya fado mata sai Yaa Aslam, Ta jima tana juyi duk ranta ba dadi sannan ta mike ta shiga cire kaya.
Tana gamawa ta fada bandaki wanka ta fara. Tana gama wa ta tayi alwala.
Sai da ta shirya cikin kayan baccin ta dogon wando da riga fare tas sannan ta tada sallah. Ta jima tana addu'a kan Allah ya kawo mata dauki sannan ta Mikewa jiki a sanyaye ta bude firij.
Lemo ta dauko ta koma kan gado ta zauna. Wayar ta ta dauka ta latsa number Yaa Buhari.
Da sauri ya dauka. Murya ta shagwabe ta ce,
"Yaya shine ka manta dani ko?"Murmushi yayi ya ce,
"Tayaya zan manta dake Sis. Na ta neman number ki ke da wife ban same ku ba."Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,
"To Yaya Ya hanya yasu Momy da Dady.""Suna lafiya. Ince kuma kuna lafiya."
Kai ta gyada masa."Asma'u me yake dumun ki?"
Dan yaji muryar ta ba dai dai ba.Damuwar ta tai kokarin kawar wa sannan ta danyi murmushin karfin hali ta ce,
"Ba komai.""Kin tabbata?"
ya tambaye ta.Kai ta gyada masa. Yace
"To sai da safe."Sukai sallama. Kwanciyya tayi tana tunanin Sir Sabir kuma.
"To tinda na rasa Ya Aslam me yasa ba zan karbi duk wanda ya so ni ba. Sir Sabir bai da makusa. Yana da kyau ga ilimi ga addini ga nutsuwa me kuma zan nema bayan nan."
Tayi juyi, ta kuma fadin,
"Duk da haka dai ina son Yaa Aslam ko ba komai Yaa Aslam yayanah ne,"Hawaye ne ya zubo mata. Ta jima tana kuka sannan ya mike tayo alwala ta tada sallah.
Ta jima tana kai kukan ta gun Allah. Sannan ta hau karatun Alkur'ani.
Har akai sallah asuba tana kan sallaya. Wanka ta kara yi sannan ta dawo ta tada sallah.
Tana idar wa ta fada kan gado sai a lokacin wani bacci mai nauyi ya dauke ta.
Mami tinda ta tashi bata ga Asma'u ba ta leko ta tadda tana bacci ta sauka kasa kawai. Dan tasan ba zata aiki ba tinda bata sauko ba.
Aiki tayi ta hada musu break sannan ta yi wanka.
Har karfe biyu Asma'u bata sauko ba. Mami Ta hau sama ta dubo ta yafi sau uku amman bacci take kuma jikin ta ba zazzabi.
Wannan ne yasa Hankalin Mami ya dan kwanta.
Karfe biyu da rabi Zainab ta karaso gidan. Mami ta gani zaune a falo.

YOU ARE READING
Rayuwar Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔
FantasyLabari akan wata yarinya Asma'u wacce take shiga wani yanayi akan soyayya. Sun shaku sosai da Yayan ta amman daga baya ya barta. Komene dalili? Oho muje ciki dan jin shin tana auren sa ko kuwa.