11

5.7K 252 3
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

          ~NA~

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO  UNDER AGES , SU KARANTA BA'''


~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*

11

K'orafin ku ya karb'o masoya na, in sha zan ci gaba da posting a WhatsApp, amma sai na fara yi a wattpad.

Da k'arfi k'irjinsa ya buga dammmm!  ya kalli Yasmeen, Fahad, Kaudar...

Sai ya maida kallon sa ga Al'amin, murmushi yayi yace " yana nan , " to yana ina?  cewar Al'amin, a fusace Abdul yace " yana nan nace mak.....  A'a a fad'a musu gaskiyar lamari cewar Fahad,  "no Fahad inji Abdul, dafa kafard'ar Abdul Fahad yayi ya k'ura masa ido ya langwab'ar da kai yana yi masa alamar please, murmushi Abdul yayi yace " Ok.

Fahad ya d'ora da cewa " ni ne *HAIDAR* ya b'oye muku ne sakamon maganar fyad'en Aisha, shiyasa ya sakaya sunana, amma magana ta gaskiya nine HAIDAR, kuma ainihin sunana FAHAD ne ba HAIDAR ba, sannan bani kad'ai SANATA SAMBO ya haifa ba mu uku ya haifa, nine babba sai gani na, shine HAIDAR, amma bashi ne na cikin labarin Abdul ba, ni ne acikin labarin Abdul, sai k'anwa ta Zakiyyah, sai Momyn mu, sannan gaba d'ayan mu uwar mu d'aya uban mu d'aya.

" zaku ji sauran labarin dangina idan matata Kausar zata bada labarinta, sannan Sanata Sambo yana nan a raye, yanzu baya komai sai aikin Allah, yana amfani da dukiyar sa ne wajen yiwa musulci da musalmai hidima.

"Ya  b'oye sauran yaran nasa ne, saboda yanayin siyasa, hakan ne yasa bai bayyanawa duniya k'anne na ba, sai bayan da komai ya zama dai-dai hankali ya kwanta sannan ya bayyanawa duniya su.

Bayan Fahad ya gama bayanin ne, ya kalli sauran jama'ar yace " zamu je muyi sallah idan mun dawo sai muci gaba, Khamal ne fara bada nasa labarin.

Duk suka mik'e suka shiga cikin *6'S STARS* Hotel, bayan sunci abinci sunyi sallah suka d'an huta sannan suka dawo, bayan komai ya dai-daita Fahad ya kalli Khamal yace " oya start , murmushi Khamal yayi ya suma.

*LABARIN KHAMAL*

Ainahin sunana Khamaludden Ahmad, haifaffaan garin Kaduna ne unguwar rimi, mu biyu iyaye na suka haife mu, ni da k'anina HAMZA, tun muna yara iyaye mun suka mutu, a hannun kakarmu muka taso ita ce komai namu, bamusan kowa namu ba sai ita, kakar mu wacce muke kira da Hajiya ta d'auki san duniya ta d'ora mana, kasancewar mahaifin mu ne kawai d'an data haifa a duniya gashi kuma ya rasu.

" ni kuma na d'auki san duniya na d'orawa Hamza, dan gani nake kamar shine gata na, kasancewar bamu da kowa, duk abinda Hamza ke so to nima ina sanshi, haka duk abinda baya so nima bana sanshi, haka duk abinda ya gani yana so hankali na baya kwanciya sai naga ya mallake shi, idan da abinda nafi tsana a rayuwa ta shine b'acin ran Hamza.

"Kamar yadda nake san Hamza haka shima abin yake a b'angaren sa, koma ince yafi so na, fiye da yadda nake sanshi, dan ko ciwo na kwanta to shima sai yayi rashin lafiya ba k'aramar shakuwa ce a tsakanin mu, daga ni harshi babu mai aboki, mu biyu ne kawai muke rayuwar mu, har Allah yasa muka shiga jami'a, ni ina level 4 Hamza yana level 2.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now