31

4.8K 312 11
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

~NA~

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*

31

Idris driver na zuwa uncompleted building d'in da ita ya tsaya cikin alamar tsoro da firgici had'i da mummunan tashin hankali ya fara magana " Hajiya kin tab'a taimako na dan haka bazan tab'a bari ina gani wani mummunan abu ya same ki ba, da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro memory card ya mik'a mata yace " gashi idan kinje gida ki nutsu ki gani kinji duk shirin da Mukhtar keyi a kanki yana ciki, sannan ya k'ara da cewa " a kowanne lokaci kina iya jin ance maki na mutu to ba mutuwar Allah da Annabi bace dan Mukhtar yana neman rayuwata akan wannan memory, yana kaiwa nan bai tsaya ya jira abinda zata ce ba ya fita da gudu a matuk'ar firgice, a tsaye ya barta tana ta zancen zuci yayinda da hawaye sai ambaliya yake yi a fuskarta, dakyar ta iya jan k'afarta zuwa inda mota take ta shiga, koda suka isa gida a parlor ta iske Mukhtar bata tsaya bin ta kansa ba ta shige d'aki had'i da danna key.

Jikinta na rawa ta saka memory a wayarta ta kunna ta fara kallon abinda ke cikin, iyakar tashin hankali kan Teemah ta shige shi, jikinta ya shiga rawa had'i da kerrma cikin tsoro da mummunan tashin hankali taci gaba da kallon video, Mukhtar ta gani tsirarar Allah yana aikata zina da wata zankad'ed'iyar budurwa bayan sun gama aikata masha'arsu budurwar ta kwanta a saman k'irjinsa tana shafo fuskarsa a hankali ta d'aga kai tana duban sa, ido d'aya Mukhtar ya kanne mata yace " ''yan mata ya akayi ne?

Murmushi tayi had'i da yin wani farrr da ido sannan tace " yanzu duk irin soyayyar nan da mukeyi amma bazaka aure ne ba? "Inji wa yace bazan aure ki ba? "gani nayi da ido na ai ba sai an fad'a min Teemah zaka aura ba, "what Mukhtar yace had'i da mik'ewa zaune yana kallanta yace " God forbid na aure ni wallahi ko mata sun k'are a duniya ni kuwa mezanyi da ita, wanne dare ne jemage bai gani ba, tun Teemah tana 14yrs nake kusantarta, haba ke ko abinci ne ai yaci ace ka gaji dashi haka, nayi amfani da ita ne dan cikar burina, dan ni babu abinda bazan iya akan kud'i ba, ke ni in tak'aice miki magana idan ta kama ma na kashe Teemah to tabbas zan kawar da ita daga doran duniya abu mai sauk'in ne na tsinke mata numfashin ta matuk'ar naga zata bani ciwon kai, " a firgice budurwar ta d'ago tana kallan Mukhtar tace " kai my dear yanzu zaka iya kashe Teemah?

Murmushi yayi irin nasu na cikakkun 'yan bariki sannan yace "ke nifa tunda nake a duniya ban tab'a ganin mace irin Teemah, shegiya mahaukaciya kawai ita in banda bata da cikekken hankali yama za'ayi tayi tunanin zan aure ta bayan naga irin abinda tayiwa Zaid ni karan hauka ne ya cije ni zan aure ta, ni ma idan ta samu wani wanda tafi sanshi akayi na abu mafi sauk'i ne tayi min irin abinda tayiwa tsohon mijinta.

"To yanzu meye target d'inka akanta? shiru Mukhtar ya d'anyi sannan ya kalli busurwar yace " kinga dai har yanzu ban bata kasonta ba, ina lallab'a ne dan mu rabu lafiya kin san fa halin karuwai, idan ta gane mai nake nufi da ita komai yana iya faruwa, dan haka nake son tsara komai a hankali, ta yadda bazata tab'a fahimtar komai ba, wani mahaukacin kuka Teemah ta saki had'i da buga wayar da bango aiko take wayar ta tarwatse, durk'ushewa tayi a wajen tana wani irin mahaukacin kuka mai cin rai, sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta shiga bathroom ta watsa ruwa, ta canja kaya, ta zube a gado ta fara tunanin neman mafita, dan yau Teemah ko parlor bata fito ba balle tabi takan abinci.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now