'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*38
Murmushi Hajiya Lailah tayi cike da kissa ta shafo gefen fuskar shi tace " FAHAD ne yake son yin aure dan har munje gidan su yarinyar, baka ga yarinyar ba kyakykyawa gata da hankali da tarbiyyar, da sauri Sanata Sambo yace " what da gaske kikeyi koda wasa kike yi, murmushi ta kuma yi tayi wani farrrr da ido tace " wallahi da gaske nake maka sunanan yarinyar Kausar, cike da murna ya mik'e tsaye da ita a hannunsa yana zagaye d'akin yana cewa " Alhamdulillah nima na kusa samun jika ya fad'a yana k'ok'arin had'e bakin su.
Cikin dabara ta zame jikinta daga nashi dan yanzu Hajiya Lailah ta gama zama rik'akk'iyar 'yar lesbian kwata-kwata bata sha'awar d'a namiji idan tana k'aunar mutuwarta to tana k'aunar Sanata Sambo ya tab'a ta, dan shi kansa har mamakin yadda ta canja gaba d'aya yake dan yasan Hajiya Lailah da shegiyar jarabar tsiya da naci akan sex amma yanzu kwata-kwata bama tasan ya tab'a ta da farko-farko ya d'auka zuciya tayi dashi shiyasa shima ya shareta bai wani bi ta kanta ba, amma yanzu al'amarinta ya fara bashi mamaki gami da tsoro, amma shi a ransa hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba, dan zai samu damar wolewarsa da matan banzan sa yadda ransa yake so, shi hakan ya fiye masa shima ya huta da shegen macinta da jarabarta, bayan ta zame jikinta ta kallo shi ido cikin ido tana sakar mishi murmushi tace " Alhaji bacci nake ji ta fad'a tana k'ok'arin kwanciya murmushi yace " ni kuma bana ji dan so nake ma muyi wasa, da k'arfi gabanta ya fad'a dan bata so ko tafin hannunta namiji ya rik'e ji takeyi kamar wuta saboda tsananin zafi.
Shiko Sanata Sambo yayi hakan ne danya k'ureta yaga iya gudun ruwanta, a hankali ya mik'a hannunsa ya fara shafo mata jikinta, yana bata hot romance amma ita jin jikinta take kamar yana watsa mata wuta saboda tsananin zafi da zugin da jikinta ke mata, jin ya dage ne yasa ta mik'ewa da sauri tace " Alhaji bari na shiga toilet na fito da sauri shima ya mik'e had'i da rungumo ta ta baya yace " nima toilet d'in zan shiga ya fad'a yana sakar mata murmushi wanda ita tasan ma'anar murmushin ganin haka yasata daurewa ta bada kai bori ya hau.
Washe gari da safe Sanata Sambo ya sanar da wasu daga cikin 'yan uwnsa da abokanan sa da daddare zasu rakashi nemarwa Fahad aure, bayan sallahr ishsha motocin su Sanata sukayi parking a k'ofar gidan su Kausar, bayan anyi musu suka shiga, k'anin Sanata Sambo ne yayi magana bayan sun gama gaisawa " mun zo kan maganar yarinyar wajenka da yaron wajen mu, murmushi k'anin Malam yace " badamuwa mun san da maganar, nan dai suka tsayar da maganar auren da ranar auren akan juma'a mai zuwa za'a d'aura auren nan da kwana shida kenan, kafin su Sanata Sambo su yafi sai da sukayi komai na al'ada da farillah tun daga kan su kud'in auren aure kudin nagani inaso, kud'in gaisuwar iyaye da kud'in sadaki gaba d'aya suka had'a suka bada dubu d'ari biyar 500k.
Washe garin ranar Malam ya kira Kausar da Ummanta suka zauna a gabansa sai da ya niffasa sannan ya kira sunanta " Kausar a hankali ta d'ago kanta had'i da cewa " na'am, sai da ya d'auki d'an lokaci sannan yace " Kausar ina so na sanar dake wata magana amma ina tsoro dan ban san yadda zaki karb'e ta ba,, amma ya zama dole na sanar dake, Kausar kin san dai nine mahaifin ki bazan kuma tab'a cutar dake ba dan nafi kowa sanki naki kowa sanin zafinki da darajarki, bazan tab'a kaiki inda za'a cutar dake ba, bazan tab'a kuma had'aki da wanda zai cutar dake ba, nasan kuma ke kanki kinsan hakan, nasan duk hukuncin dana yanke akanki bazaki tab'a k'in yi min biyayya ba, dan haka nake son sanar dake ranar juma'ar nan mai zuwa nan da kwana biyar d'aurin auren ki dan na bada aureki da k'arfi k'irjinta yayi muguwar bugawa, a firgice ta d'ago kai ta kalli Malam da Ummanta ganin duk ita suke kallo yasata saurin yin k'asa da kanta.

YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...