72

3.7K 205 6
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
             *~(UMMU AMAN)~*




72




Wani mahaukacin bugu suka yiwa k'ofar dayasa ta b'alle,
babban cikin su yasa yaransa su shiga ciki su yo masa waje da mutanen gidan,
su Zainab na k'ok'arin b'uya aka banko k'ofar d'akin da k'arfin tsiya,
zagaye su 'yan fashin sukayi da bindigogi suka tusa k'eyarsu zuwa parlor inda babban su yake zaune ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya,
da k'arfi aka durk'usar da su Mannir a gabansa,
sai da ya gama k'are musu kallo kafin yace " ina kud'in daka shigo dasu jiya?

Yayi maganar cikin izza da wulak'anci,
cikin rawar baki Mannir yace " ni ban shigo da wani kud'i jiya ba,
gyara zamansa yayi sannan yace " kaga ba wani abu ne ya kawo mu ba,
ba kuma b'ata lokaci ne ya kawo mu ba, bana san raina ya b'aci,
kuma bana san nayi loosing control d'ina dan idan nayi komai yana iya faruwa,
amma idan ka bamu salin alin zamu tafi batare da munyi muku komai ba,
da ka bamu da tuni munyi tafiyar mu, amma idan kace zaka tsaya b'ata mana lokaci kayi mana gardama wallahi sai nayi maka hukunci mai tsananin gaske,
ta yadda har ka mutu kana nadama da dana sani,
cikin kuka Zainab ta kalle shi tace " dan girman Allah ka rufa mana asiri ka basu duk abinda suke so,
koma nawane ka basu su tafi kamar yadda suka ce please tayi maganar cikin rikitaccan kuka,
cikin tsuma Mannir yace " wallahi babu kud'i a gidan nan,
sai dai idan  check zan rubuta muku,
ko kuma nayi muku transfer ta Bank,,
wani mahaukacin mari shugaban 'yan fashin ya maka masa,
cikin matsanancin fushi yace " kama rai na mana hankali, to ka shiga hankalinka dan kaga ina binka cikin sauk'i da lallashi,
zan baka dama ta k'arshe, na kuma yi maka tambaya ta k'arshe wacce daga ita komai yana iya faruwa,
ina kud'in daka shigo dasu gida?

Sugaban 'yan fashin ya kuma tambayar Mannir,,
cikin tsuma Mannir yace " wallahi tallahi ba kud'i a gidan nan,
amma  ku cake gidan kaf idan har kun gani ku d'auka,
kallan d'aya daga cikin 'yan fashin babban su yayi sannan yace " jeka kira shi,
ba musu  ya fita, bai dad'e da fita ba suka dawo tare da mai gadin gidan,
kai Mannir ya d'aga yana kallan maigadin gidan,
shugaban 'yan fashi ya kalli Mannir yace " waye wannan?

" A tunaninka shi mutumin kirki ne?

"Ko kana tsammanin aikin gadi kawai yake?

" To idan baka sani ba, yau ka sani shi d'an fashi ne, kuma duk gidajan da akayiwa fashi a unguwar nan shi ne,,
da sauri Mannir ya d'ago kai yana kallan mai gadinsa da suka shafe 20yrs tare,
tun da yayi aure yake masa aikin gadi bai kuma tab'a canza shi ba,
cike da mamaki Mannir ke kallansa, cikin rawar murya yace " Dauda kai ne?

"Dama kai mugu ne mai fuska biyu azzalumi maci ama...... tauuuuuuu,
Mannir yaji an kuma maka masa wani gigitaccan marin , take hancinsa da bakinsa suka fashe,
wanda ya mari Mannir yace " kai ka isa ka tsaya a gaban mu kana zagin Ogan mu,
idan baka sani ba, ka sani shine leader mu, (Oga) kuma shine Master dan haka ka kama kanka,
murmushi Dauda mai gadi yayi sannan ya zauna akan sofa had'i da hard'e k'afa d'aya kan d'aya,
ya kalli Mannir yace " Mannir nine shugaban gaba d'aya 'yan fashin dake Kano State,
ko lokacin daka d'auke ni aiki, a fashi da makami na nake,
kuma abinda yasa nazo gadi gidan nan saboda nayi fashi a gidan,
kasan meya hanani duk tsayin shekarun nan?

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now