'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*15
Da kyar da taimakon Allah Hamza ya samu ya fizgo numfashinsa, a hankali a hankali yake bud'e idonsa harya samu yayi controlling kansa, dan baya son koda wasa Khamal ya fuskanci akwai wani abu tsakanin sa da Fateeha, ya daure ya doje yayi kamar ba wani abu, amma acan k'ark'ashin zuciyar sa ji yake kamar ya mutu da sauri k'irjinsa ke bugawa, mak'ogwaron sa ya bushe bakinsa ya rinka yi masa d'aci.
Itako Fateeha bama tasan Allah yayi ruwansa ba, gaba d'aya hankalinta yana kan Khamal, kwata-kwata bata cikin nutsuwar ta, sosai ta matsa daf dashi ta yadda kowannen su yana iya jiyo numfashin juna cikin sanyin murya tace " please Khamal karka barni, kai kanka kasan ina sanka, karka d'ora min laifin daba nawa ba, ya d'an matsa baya kad'an yana aika mata wani irin kallo, yace " kinga please ki tafi gida, kai ta shiga girgiza masa cikin kuka tace " a'a Khamal please karka barni, bazan iya jure rashin ka ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi, ni kaina bansan ina yi maka wannan mugun son ba sai yanzu, Khamal kaine ruhi ne, idan ka barni tamkar ka tafi da rahi nane kabar gangar jiki na.
" Tunda nake ban tab'a yiwa iyaye na musu ko gardama na sai akanka duk abinda suka umarce bana yi musu gardama hakan ne ma yasa Dady ya yanke ranar aure na ba tare daya shawarce ni ba, cikin muguwar razana Khamal ya d'ago kai ka kalle ta, aiko karaf suka had'a ido, alama tayi masa da idonta na eh, taci gaba da cewa amma a kanka na kunya Dady na tubure nace a'a, akan ka nak'i yi masa biyayya, na bijire masa, yanzu haka Dady ko magana baya man, a kanka farin ciki da kwanciyar hanklin da iyaye na suka gina shekara da shekaru ke neman gujewa dan yanzu haka Momy da Dady neman rabuwa suke.
" Ashe duk tarin maganganun dakake fad'a min ba gaskiya, kasha fad'a min nice rauwarka, nice farin cikin ka, nice duniyarka, kace duk runtsi duk bazaka tab'a rabuwa da ni ba, Idan kasan baka sona mai yasa kace kana so, idan kasan bazaka iya rayuwa dani ba mai yasa ka koyamin yadda bazan iya rayuwa ba kai ba, idan kasan bazaka d'orewa so na ba mai yasa zaka koyar dani yadda zan soka, mai yasa Khamal mai yasa ta durk'usa a k'asa ta fashe da kula mai cin rai.
A matsayi na na mace mai kunya, daraja, k'ima, da Allah yayi min, na yarda jan aji na, na tako har gidan ku, amma duk da haka bazaka hak'ura ba, kai wanne irin mutum ne marar adalci wanda kansa kawai ya sani, baka damu da damuwar wani ba, taka damuwar kawai ka sani, wacce irin zuciya kake da ita mai kafiya marar yafiya.
Jikin Khamal yayi mugun yin sanyi, zuciyar sa ta harba da k'arfi, yayin da yake jin santa na k'ara ratsa ko'ina na jikinsa yana bin kowacce jijiya ta jikinsa yana bin jininsa, ya runtse idanunwa da gam, k'aunarta na fizgarsa zuwa gare ta.
Hamza ko zama yayi kamar ba mutum ya, ya sandare a waje d'aya, babu abinda zuciyar keyi sai bugawa, k'irjinsa nayi masa zafi, ji yake kamar ya mutu, dakyar yake iya controlling kansa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata tsage, a gaban idon sa macen dayafi fiye da kowacce mace a duniya ke kukan son Yayar sa uwa d'aya uba d'aya, wanda duk duniya bashi da kamar sa, a hankali ya share siririn hawayen daya zubo masa.

YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...