chapter 9

1.3K 80 0
                                    

💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
💗💗💗💗💗💗💗

        
      Written By;FOULANI CERDIYA
       &
KHAIRAT UP

      Wattpad@ khairi-muhd

        "9"

Tunda Maisha ta samu rauninnan Yah Muh ya dawo yana d'an lallab'ata kuma komai take so shi zai mata badan komai ba sedan karta tona asirin shi yasa tsallen data ji ciwon.

      Yau Friday kowa ya shirya saboda zasuje gidan Baba ta chiranchi dama aladar gidance duk jumaa suna zuwa.

      "Maisha kiyi hak'uri ki zauna, in yaso sai a kaiki daga baya".
    Yah Muh ne yake maganar sakamakon rigimar datasa na ita sai taje.
      " Yaufa kwananki uku dajin ciwon nan kada kije ki fama."

       Turo baki gaba tayi tare da juya kanta gefen dabata kallonsa tace"ni wallahi in bazaa dani ba sai na fad'awa Abbana".

     Ransh'ine ya b'aci ganin ya zauna yana lallashinta tana b'ata masa lokaci
    "Wallahi Maisha ba Inda zaki kuma kika sake kika fito waje ranki sai ya baci shashasha,ki fadawa Abban kiga yadda zanyi gunduwa -gunduwa dake a gidannan".
Yana gama fad'ar haka ya fice daga dakin.

Haka Maisha tanaji tana gani aka Fita aka barta, ita kadai sai mai gadi da Yar aiki.

     Tash'i tayi ta nufi mudubi ta fara Dan shafa powder aranta tana cewa" Tayaya ma zaai yayi gunduwa-gunduwa dani sai kace kifi?......Kuma mafa zai iya gunduwar dani ko?........ai baida imani tas tunda gashi ya b'allan kafa".

    Gama kwalliyarta tayi ta sakko ta fice, mai gadine ya kalleta yace"D'iyar Abba ina zaki?".
        "Kajishi ko meye ruwanshi ma da Inda zani mtsww".
   Ta fad'a a ranta.

       A fili kuwa sai cewa tayi" biscuit zan sayo fa".
     "Aah Maisha bari in sayo miki".
     " Toh na baka kudinne?".
      "Aa basai kin banba bari naje na sayo miki kinji y'ata, zauna an an na jiraki".
    Allah sarki mai Gadi yayi hakane saboda dazu kafin su Yah muh su fita said a ya masa warning akan ya kula da ita kada ta fita.

     Mai Gadi na fita Maisha tad'an cangala k'afarta sakamakon har yanzu bata warke ba itama ta fita direct bakin titi ta nufa, yauma kuwa ta hango wannan saurayin zaune da Alqur'an a hannunshi, da faraarta Maisha tayi gunsa tana zuwa taja ta tsaya ta hard'e hannayenta tana kallonshi.

     Tunda ta taho ya rufe Qur'an din ya qura mata ido sakamakon ganin dauri a kafarta.

    Kallonta yayi da damuwa yace" Ah.....y'ar yarinya meya sami k'afarki?".
      Ai kamar Maisha jira take ta fara zuba masa surutunta.

      "Ba mugun Yayah na bane ya sani tsallen............................" Nan ta kwashe komai ta fad'a masa , sosai yaji ba dadi, amma sai yace da ita"Ke yayan naki kike cewa mugu ki dena ba kyau."
      "To ai naga kai babu ruwanka me mutunci da kai shi kuwa cin zali".

     " To kidena fitina kinji, sekiga kun sh'irya dashi, kuma ma meyasa kika fito da yamman nan?".

     "Bakomi fa, yauma tafiya sukayi suka barni, wallahi kuma ni bazan CE zan bisu ba amma sena fadawa Abba".
      Sosai ya fuskanci Abban nan Nata yanaji da ita.

      " waini Sabon Yayah ya sunanka, kaima sunanka irin nawa ne? Kaima naga kana da kyau kamafi Yah Muh kyau Ni kuma nasan nafika ma kyau, saboda sunana ma Pretty".
     Ta karashe maganar tana dariya da wani fari da ido.

    "Aa ni ba ni da kyau, kinataba ganin namiji da kyau in banda abink".

       Zaro ido tayi tace " Lah gashi kuwa kana dashi".

      "Toh naji, fad'amun sunanki,ko da Prettyn nima zan ringa kiranki?",.

       " Hahhhh sunana mai tsada ne seka siya,amma tunda kaine zan fada maka, MAISHA!!!".

       Seda yaji dummm, sakamakon jin sunan ta mai dadin gaske, kuma ya dace da ita.

       "Kaifa ya sunanka?".

" MO'TASEEM ALKHALI SHAREEF (MAS)".

      "Woww Yah Moh.......Sunanka dadi wallahi".

      " Hmmmm Maisha muje na rakaki gida, kinga yamma tayi sosai kuma banason ayi miki fad'a".

      "Toh Yah Moh".
          Ta fad'a tana rik'o hannunsa tana wasa dashi, a hanya ma sai zuba masa zance take, tana ta dariya abinta, shikam murmushi kawai yake mata saboda ya kula akwai tsantsar kuruciya da shagwaba agunta.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora