chapter 56

956 63 1
                                    

SARK'AK'IYAR SOYAYYAH

         Na

FOULANI CERDIYA
       &
KHAIRAT UP

        "58"

    "Ke me kike shirin yimun ne? Wulakanci? Dama Maisha duk SOYAYYAH din da kika nunan a baya ta karya CE? Mayaudariya CE ke dama Maisha, Amanata kikaci dama Maisha? Ameenuh fa Kanina ne why why?".

          "Ya isa haka Mana duk menayi maka da kake gaggayan wadannan maganganun? Akan me?".

         " Maisha Ameenuh fa k'anina ne ko kin manta, pls ki Samar mun wani kishiya amma banda Ameenuh bazan iya kishi da shi ba, I all fight for u Maisha da kowane ne, a baya na bari kin kufcemun a k'addara amma yanzu bazan iya ba, kina nema ki kara jefani cikin SARK'AK'IYAR SOYAYYAH!!!".

       Hawaye yake yi kamar wani karamun yaro,

      "Ki tausaya mana nida little kina jin abinda Mamy tace cewa tayi fa ta bawa Ameenuh ke matsawar kin amince pls Maisha kada ki mana haka kada ki yadda a rabamu a Karo na biyu".

                Kanta ta rik'e ta fasa ihu da kowa na gidan sai da yaji tace
      " Yah Muhd zan bar gidan nan, zan tafi wani gurin inda bazaku kara gani na ba ballantana Ku nemi ruguzamun kwakwalwa, wlh zan bar maku gidanku".

      Maisha ta mik'e ta zari Little ta sab'a a baya ta dauko wata akwati ta fara loda kaya a ciki kamar mahaukaciya, sai surutai takeyi.

Tana gama had'a kayanta ta sh'iga Jan akwati kiii zata fita, hannunta ya rik'e

      "Ba inda zaki tafi Maisha".

        Fisge hannunta tayi ta fara tafiya har tazo kan stair Yah Ameenuh ya rik'e mata hannu shima haka Yah Muhd kowa begging ta yake kada ta tafi.

     Tasleem CE ta hayo saman taji ana rarrashin Maisha kan kada ta gudu.

Ai da gudu tayi gun Mamy ta sanar mata sai gasu tare, ran Mamy ya b'aci over batasan sanda tasa hannu ta taska mata mari lafiyayye ba.

       " Zaki gudu ko? Ki gudu ga hanya nan ki ba'cemun da gani tunda baki da tunani bazaki iya zama kiyiwa kanki tunanin ta nutsu ba have a way and go duniya CE, Muhd Ameenuh Ku cikata ta tafi".

         Kuka ta fash'e dashi ta fincike hannunta da gudu tayi daki, wayarta ta dauka ta kira Yah Nasser baafi 10 mnt ba sai gashi a gidan hankalinsa tashe jin halin da ake ciki.

Da aka gaya masa shima jiyayi sunsakashi cikin SARK'AK'IYAR Dan ya rasa ma mai zaice.

     To waya fi dacewa Maisha ta aura ne tunda dukansu suna sonta kuma yan uwa jini daya kai wannan cakwakiya.


Daga k'arsh'e ya yanke shawarar zai tafi da Maisha gidansa kota samu relief.

     Haka ta tarkata ta tafi inda Mamy tace ta ajiye mata little kada ta tafi mata dashi, ganin dai ran Mamyn a bace yake da ita yasa ta ajiye shi yana ta kuka ta tafi.

      A can gidan kuwa Yah Nasser aikin rarrashinta yayi tayi.

Ya kuma bata shawara kan acikinsu ta zabi daya in yaso sai a aura mata shi amma ta nutsu tayi tunani.

       Har dare Maisha bata iya bacci ba, ga uban kiranan daga Yah Ameenuh da Yah muhd taka rasa wanne zata d'aga daga k'arsh'e tayiwa wayar switch off ta kwanta amma bacci yace nemeni inda kika ganni Maisha.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now